chapter 60

309 32 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

60🍎

"Yaya akayi kika bari hakan ta faru? Kinsan matsalolin da muke ciki Basu qare ba Yaya akayi Kika Bari ciki ya shiga jikin ki Feenah?"

" Na Isa naja da ikon Allah ne ya Ahmad? Duk wani qoqari inayi wajen ganin nayi supporting dinka Amman ka sani banida ikon yin halitta ko Kuma hana wanzuwar abinda Allah ya halitta, kasan abinda zakayi bazan yarda na haife 'dana anan qasar ba saboda bansan wani kallo iyayen ka zasuyi min ba"

Neman wuri yayi ya zauna hade da dafa kanshi da yake Masa wani mahaukacin ciwo hawaye nabin idanuwan shi
"Feenah why did you do this to me? Dan Allah da wanne zanji? Yaya kukeso nayi da raina? Acan ga mom ga Amrah anan Kuma ga 'dana kwance babu lafiya ga cikin jikin ki, a Ina zansa kaina a duniyar Nan naji sanyi?"

Tasan a irin wannan lokacin musu bazai amfane su ba, ta zauna hade da daura kanta akan kafadar shi tana zubar hawaye tace
"Allah na sane damu hayaty zai kawo Mana mafita, dukkan tsanani Yana tare da sauqi I'm very sorry"

Baice da ita komai ba itama Bata qara magana ba sukaci gaba da zama a haka na dan wani lokaci, can ya miqe gaba daya fuskar yayi jaa, ya daidaita nutsuwar shi sannan ya shiga dakin Abdallah tana biye dashi suka samu har ya koma bacci.

Ya zauna a kujeran gaban gadonshi ya zura hannun shi cikin gashin kansa da ya kwanta luff Yana sheqi, a hankali yake shafa kanshi Yana Kiran sunan shi.

Bude idon shi yayi ya sake wa mahaifin shi murmushi yace
"Abbah Ina kazo Kenan ba Zaka tafi ba? Zamu ci gaba da zama tare dakai da Ummi".

" No my boy Dole zan koma Nigeria Amman idan kana so zan tafi dakai"

" Abbah teacher Meg tace na girma a daina cemun boy I'm now a man"

Dariya Ahmad yayi yace " ok man idan ka warke sai mu tafi tare ko?

"Da Ummi zamu tafi?"

"No ita zataci gaba da zama anan daga baya sai mu dawo mu dauke ta"

" Ni bazan je ko Ina ba tare da Ummi na ba" da sauri Feenah tace

" Haba hayaty idan ka rabani da Abdallah bakayi min adalci ba, bayan duk mutanen da na rabu dasu a dalilin ka yanzu Kuma Kai da kanka kake so ka rabani da gudar jini na gaskiya bazan yarda ba, saidai idan ka yarda mu tafi tare gaba daya Amman bazan taba barin ka kadauke Abdallah daga gareni ba"

baice da ita komai ba ya fita daga dakin dan bayiso tun yanzu su fara sa'insa a gaban yaran su, Bai dawo ba sai dare.

Yaje an gyara masa gashin kansa da fiskan sa, yayi wanka ya shirya cikin kayan sanyi na Christian louboutin ga qamshin oud sharqiyya da yake fitar wa, hasken fatar shi da haibar shi ya qara fitowa cikin wuni daya har ya Sami nutsuwar kula da kanshi Amman kwanciyar hankali Kam har yanzu Bai ganshi ba.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now