chapter 38

302 37 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

38🍎

Kafin Ahmad ma nayi soyayya da maza musulmai guda biyu, na farkon class mate Dina ne mutumin kirki ne sosai balaraben qasar Oman, munyi alqawarin zamuyi aure daga zaran mun Gama makaranta Amman unfortunately tun da ya tafi gida har yau Bai dawo ba, zuciya na ya sosu sosai da na rasa shi saboda na so shi da yawa.

Bayan shi Kuma da na fara aiki aka tura mu wani company a Yemen, acan na hadu da na biyu, kyakkyawan balarabe mai aji, shi ya fara nuna cewa Yana so na daga farko naqi amincewa don bayi cikin tsarin mazan da nake so Amman daga baya sai nayi tunanin shima mutumin kirki ne tunda ance musulunci ya hana aikata alfasha, Amman yarda dashi shine babban kuskuren da nayi, yayi amfani da banbancin addinin mu ya nemi raba ni da mutunci na, duk lokacin da ya min abun da Bai Dace ba, idan nayi complaining sai yace ai addinin mu Bai hana ba, bani da wani zabin da ya wuce nayi haquri da irin abubuwan da yake min, sai dai ranar da har yau nake nadaman sanin shi da Kuma amincewa dashi shine wani Daren alhamis, Ina gida ya turo min saqo cewa akwai public dinner a mövenpick hotel a cewar shi za'ayi murnan nasaran da muka samu Kan wani aiki da muka Gama, amman da mamaki da naje Banga kowa ba Bayan shi, a lokacin ya saka min qwaya cikin Champaign da haka yaso ya raba ni da mutunci na sai dai Bai samu nasara ba da 'dan qarfin da ya rage min na buga Masa kwalban champagne din na gudu, tun daga wannan dare ban sake kwanan Yemen ba na tattara kayana washe gari na nemi transfer na koma Los Angeles gurin mahaifi na Kuma tun daga wannan Rana ban sake kula wani namiji ba na fitar da soyayya gaba Daya daga cikin raina.

Zaman los Angeles bayi mun dadi kwata_kwata don ko wace rana nakan kwana na tashi da takaicin mahaifina, tun daga ranar da mahaifiya ta ta mutu yaqi aure sai kwashe_kwashen Mata, duk ranar da na wayi gari cikin gidan mu macen da zan gani daban da na jiya, hakan ba qaramin Bata min rai yake ba, cikin sa'a ko wata biyu banyi da dawowa L.A ba aka zabi wasu daga cikin mu akai Mana interview, cikin mutane 50 mu 15 kawai aka dauka aka tura mu wani company dake Chicago, acan na hadu da Ahmad yaron CEO na legendary enterprises, tun da na daura idanu na a kanshi na fara son shi, Amman ban saka Rai dan same shi ba kodan dukiyar da yake dashi nasan yafi qarfin aji na, haka na riqe sirri na cikin zuciya ta har zuwa wani lokacin da yanayin aiki ya kawo ni kusa dashi muka fara magana har yakan zauna muyi shawara Akan aiki dashi, hakan ya saka min yaqini cikin zuciya ta cewa wata Rana Nima zan mallaki wannan musulmin African, nayi ta jiran ranar da zai Soni hakan Bai faru ba shine na yanke shawaran samun mahaifin shi da zancen, don dagaske nake son shi Kuma nake son auren shi, mahaifin shi Bai nuna damuwa ba ya fada min zai tuntubi Ahmad din idan har Yana so na to babu makawa zan aure shi.

Saidai ana sanar da sir L wannan lamarin ko tunani baiyi akai ba yace shi bayi so na, duk da haka ban cire tsammani ba Kuma na daura aniyar Koda musulunta yake so nayi saboda ya aure ni zan musulunta, kwatsam Rana Daya ya sanar Dani aure zaiyi, ban gaskata zancen ba sai Bayan auren ku a office aka turo pictures dinku tare na dinner party, ranar da zai dawo aiki Kuma ya zo tare dake" kukan da ya kufce Mata ne ya Hana ta qarasa magana, ta rufe fuskar ta da tafin hannun ta tana rerasu a hankali Feenah na patting dinta a baya tana lallashin ta.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now