chapter 8

382 42 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

    🌹 HAR ABADA 🌹
           (Forever)

     LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

08🍎

7:33am
Hayaniyan su ne ya daga ta daga baccin da take a hankali ta fito parlorn khaleel ne zaune nesa da Intee suna ta dariya.
Kallon su ta tsaya yi,
sunyi Mata kyau a yanayin da suke sun Dace kamar Mata da miji,
Haka kawai taji kishin Intee a ranta.

Nan da Nan ta kawar da tunanin   ta qarasa wurin su tana murmushi, ta zauna kusa da khaleel tace
"Hiran me akeyine aketa dariya?"

Mamaki ne ya kama Intee da furucin Fannah domin da abaya ne cewa zatayi sun cika Mata kunne da ihu kaman marasa hankali, kokuma wani Abu makamancin haka.

Murmushi Intee tayi tace
"Ina kwana anty Fannah"

Wani wawan harara ta wulla Mata
"Ke mage banison iyayi da shegen kadifiri, sai yau kika san wani aunty? Shegen kwainanen banza kawai."

Tabe baki Intee tayi tace
"Ashe har yanzu hali Yana nan, to kiji da mijin ki nikam Kinga tafiya ta aiki nakeyi" Tawuce kitchen ta barta.

Bayan intee tagama hada breakfast nurse tayima Fannah allura yaukam saida sukayi drama da khaleel kafin aka samu ta tsaya,
Taja hannusu su ka tafi garden.

Suna tura ta a swing taji jiri na diban ta sauqa tasa Intisar tahau ita Kuma ta koma gefe cikin inuwa ta zauna tana kallon su.

Yanda khaleel yake tura swing din da qarfi sai Intee tana cilluwa sama sosai, ta qanqame igiyan swing din tana kyalkyala dariya.

Fannah dake zaune tana Shan banana smoothie ta tsaya tana kallon su,
Sun Bata sha'awa sosai Amman tanajin zafin kasan cewan wata tare da khaleel dinta.

Runtse idanuwan ta tayi ta bude su hawaye na tsiyaya a idanun ta,
Wasu abubuwa barkatai take saqawa a ranta, duk da suyan da zuciyan ta ke Mata Amman tasan hakan shine kadai mafita tunda ita tun ba yauba take ji a ranta baza tayi surviving ciwon da ke jikin ta ba.

Tashi tayi ta shiga ciki ba tare da sun lura ba, ta shige daki ta rufe tana kuka Mai cin zuciya,
Ita kanta tana tausaya wa rayuwan ta Kuma tana dada gode wa  Allah da ni'imomin da yayi Mata.

2:45pm

Fannah ne zaune a parlor Intee tana kwance a gefen ta,
Kallo sukeyi suna hira jifa_jifa.

Intee tayi dariya tace
"Amman kinyi fama da rashin ji, kin manta lokacin da muke Zariya Deejah tsagera seniors suke kiran ki fah!"

Dariya itama tayi tace
"Ba dole ba kin manta lokacin da nazuba ma Abigail qarara a ruwan wanka duk ji da kanta da take yi haka ta fito tana Mana rawan banjo a tsakiyan hostel aka yi ta Mata asosa."

"Hmm ai bani manta wa a dalili na Abigel taji jiki lokacin bulala goma tamin Wai ban fita assembly da wuri ba shine kika Mata wannan danyen aikin,
Inaga tun ranan ko harara ta Bata sake ba."

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now