chapter 41

306 39 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

41🍎

Ta koma ta kwanta tana ci gaba da kukan ta, tasan ko rarrashin Eesher tace zatayi ba zata yarda da ita ba zatayi ta ganin kamar itace batason zama a Nan din ta saka Ahmad ya koma Chicago tare da ita, zama kusa da ita Sahar tayi tace
"Daman bake Kika ce Masa kina so ya tafi da ke ba?"

Cikin kuka Feenah tace
" Sister Yaya za'ayi nace ya Ahmad ya tafi dani bayan wannan shine lokaci Mafi muhimmanci a wurin Eesher Wanda ya kamata ace Ina tare da ita, ban san me ya Ahmad yake nufi da Hana ni shiga cikin Yan uwana da yake yi ba, bansan Yaya yake so nayi da rayuwa ta ba, kullum ni kenan kulle cikin gida ni kadai kamar wata mayya!, Rabo na da qasa ta ta aihuwa wata uku Kenan ko Ammi na bani gani, yanzu nazo Kan Abu Mai matuqar muhimmanci Amman bazai barni na shaqi iskan duniya ba haba!"

Cikin bacin rai Sahar ta dauko wayarta dake Kan side drawer tayi dialling numbern Ahmad Yana dagawa ko sallama batayi ba tace
"Yaya Ahmad ko ka fasa tafiyan Nan sai bayan biki ko ka tafi Kai kadai kabar Feenah daga baya ta koma ko Kuma yanzun Nan na fada ma Dad abun da kake yi ma Yar mutane" da sauri Feenah ta taso ta fisge wayar Sahar tana share hawayen fuskar ta.

"Sister Baki da hankali ne? Yayan ki kike fada wa haka? Ai be Kamata ba tunda shine gaba dake, kiyi haquri yanzu zan shirya na bishi mu tafi, Mata ta gari Bata Saba umarnin mijin ta" miqewa Eesher tayi daga wurin da take zaune ta qaraso ta rungume Feenah tana tsiyayar hawaye, saida ta daidaita kanta kafin ta dago tana kallon cikin qwayar idon ta murya a dishe tace.

"Best naji Dadi da Kika canza alqiblar ki, Kika tuna da alqawarin da muka dauka ma kanmu tun muna yara cewa zamu zamto Yaya na gari waurin iyayen mu, sannan zamu zamo Mata na garin wurin mazajen mu, Kuma damu saka duk wani Wanda ke tare damu farin ciki Koda kuwa zamu sadaukar da namu farin cikin in the process, saboda mu samu rahamar Allah kuma duniya tayi alfahari damu, kibi mijin ki ku tafi wata Rana zamu sake haduwa idan kuka zo kokuma na saka hubby ya kawo ni har inda kike, I will miss you best friend".

Murmushi Feenah tayi ta share ma Eesher hawayen ta tace
"Thanks for understanding besty amaryar hobby, na gode ma Allah da ya bani ku a matsayin qawaye na" ta fada tana kallon Sahar " nasan cewa ko yaushe zakuyi min fighting wajen ganin Kun karbo min yanci na sannan Kuna iya qoqarin ku wajen ganin ban kauce daga Kan hanya ba, wannan alqawarin da na dauka Miki tun da dadewa bazan taba yada shi ba HAR ABADA Allah ya nufi haduwar mu wata Rana, I love you girls" ta ware hannuwan ta tayi hugging dinsu.

Sharp sharp ta yi wanka ta shirya cikin atamfa dinkin riga da skirt navy blue fiskar ta sai qyallin Mai take ta saka madaidaicin hijab akai, gaba Daya mutanen gidan suka Mata rakiya har mota driver yaja suka tafi airport.

**********
"Wallahi girman Kai shine abin da zai fara halaka ka, Kai waye da baza'a yi maka laifi ba iye? Kasan da mace kake tare Mai yasa baza ka dinga haquri bane Ahmad? Duk wasu hidimomin ka nine Kan gaba Amman saboda wani selfish interest irin naka jiya sai da na nemi abokin da zai tsaya min a venue din event fa! Yanzu idan Sahar ta fada ma dad abin da kayi ma yarinyan Nan na lahira sai ya fika Jin dadi".

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now