chapter 19

253 36 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

      RUBUTAWA

      UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

19🍎

Kuka taci gaba dayi
"Ammi wallahi bansan Yaya akayi hakan ta faru ba Koda zasu fita Saida na hada su da driver ya kaisu Kuma na fada musu idan zasu dawo su kira ni a waya na tura shi ya dauko su, bansan wani dalili ne yasa suka dawo da kansu ba".

Cike da takaicin daura laifi da suka yi ma 'yarta mama tace
"Ai kema maganin ki sai da na gargade ki kafin ki tattaro su kuzo amman Kika yi kunnen uwar shegu Kika qi saurara na, yanzu  ga abin da taurin Kai ya janyo Miki".

Sabon kuka aunty fati ta fara tana jin wani bakin ciki a ranta.

Baba yace "haba zainab ke miyasa kullum Baki fadan alkhairi ne, menene laifin Fatima a wannan lamarin ai Dan Adam bayi wuce qaddarar sa".

Tabe baki mama tayi "to  ita wannan yarinyan da taqi magana ta saka mutane a gaba tana kallon su tana kuka ai tafi kowa sanin inda Nafeesah take ta bude Baki ta fadi wurin da suka tafi". Ta fada tana nuna Eesher.

Eesher Kam jinta kawai take yi Bata da tabbacin abin da take fada don halin da take Bata banbance tsakanin fari da baqi.

Ammi ma zama tayi ta rafka uban tagumi kuka ma yaqi zuwa Mata zuciyar ta ruruwa yake da wutan azabar rashin sanin halin da Yar ta mace toll guda daya take, roqon Allah take yi ya Bata ikon zubar da hawaye ko zataji dama_dama cikin ranta.

**********

Kamar kullum ya baza takardu a gaban shi Yana dubawa Daya daga cikin wayoyin shi ya fara ringing,
Bai duba ba yayi picking saboda yasan mutanen da suke neman shi ta wannan wayar yasa akunnen sa.

"Hello sir there is a problem".

Baiyi magana ba na cikin wayar yaci gaba da cewa
"She is not eating anything".

Tabe baki yayi yace
" Ku barta ai yunwan cikin ta ne".

Cike da ladabi yace
" Ba matsalar ba kenan sir abincin da muka Kai Mata jiya ma Bata ci ba, yauma bata ci breakfast ba yanzu ma mun kai Mata lunch taqi ci sai aman wani farin ruwa take yi".

Tsaki yayi ya kashe wayan, sai bayan 30 minutes ya miqe ya dauki hular jamfan shi ya saka ya fice.

Yana shiga dakin ya same ta kwance shame_shame a qasa neman wuri yayi ya zauna Yana kallon ta kafin cikin kaushin murya yace
"Ke! Kee, Wai ba dake nake magana bane?".

Juyowa tayi tana kallon shi idanuwan ta sunyi jaa still tana kwance a qasa.

"Mai yake damun ki?"

Cike da haushin shi tace "babu "

" Bari kiji idan ma Baki ci abin ci ba makan ki Kika yi ni babu ruwa na".

Juya kanta tayi ba tare da ta tanka shi ba tana jin wutan tsanan shi na qara ruruwa a zuciyar ta, tsaki yaja ya daga waya ya Kira doctor.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now