chapter 30

301 35 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
  
Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

30🍎

"Tsoro nake ji ya Ahmad, bazan iya kwana ni kadai ba"

" Yau Kuma? To jiya waye ya Taya ki kwana?"

" Ai jiya na riga nayi barci ne, Amman yanzu bazan iyaba, ko a gida ma ba ni kadai nake kwana ba"

" How can I be sure that you are saying the truth?"

" Allah gaskiya nake fada maka idan ma baka yarda ba ka tambaya"

" Wa zan tambaya?"

Turo Baki tayi tace
"Ammi ko Eesher"

" Ok bani numbern Ammin sai in Kira ta na tambaye ta"

" Seriously?? Yanzu Kiran ta zakayi ka tambaye ta ko Ina da tsoro ko bani dashi? Me yasa baka yarda da ni bane?"

" Feenah akan me dan yarda dake? Haka siddin ki fado min cikin bedroom da tsakar Daren nan nasan me Kika zo yimin? Wa ya sani ma ko kinzo lalata ni ne?"

Wani dogon tsaki Feenah taja, ta fita a fusace hade da rufo qofan da qarfin tsiya, maganar shi ba qaramin Bata Mata Rai yayi ba.

Tafiya take yi zuciyan ta fall da tsoro, tana addu'oi a zuciyar ta tana bin garu tana tafiya a haka har ta Isa bedroom dinta, ta kunna watan dakin ta tura ta rufe qofa.

Kallon girman wurin take tana jin kaman wani Abu zai fito ya kama ta, ga mirrors ta ko ina, wani mugun miyau ta hadiye ta nufi wardrobe ta dibo Mayafai jikin ta na kyarma.

A darare taje ta saka mayafin ta rufe duk mirrors din da ke dakin ta dawo ta zauna har yanzu Bata daina Jin tsoron ba, duk motsin da taji sai ta waiga gashi tana ganin kamar inuwar mutum na leqo ta ta window.

Kuka ta fara Saida ta Sha abin ta ta qoshi da taga babu sarki sai Allah ta tashi tana salati ta qarasa ta garqame windows din, Juyowan da zatayi taga wani Abu baqiqqirin ya nufo ta da gudu, ta sake wani razanannen ihu tana Kiran sunan Ammi, babu Wanda yaji ta saboda duka qofofin dakunan sound proof ne.

Ta sulale ta zauna a qasan wurin ta dunqule tare da cusa kanta cikin cinyoyin ta tana rera kuka Mai tsuma zuciya, can anjima taji kaman da mutum a gefen ta, Bata juya wurin ba ta rarrafa ta qarasa jikin gadon ta.

Kwanciya tayi ta janyo blanket ta rufe tundaga qafan ta har fuskan ta jikinta na bari, barci gaba Daya ya qaurace a idanun ta ga wasu strange muryoyi da take ji, lumui tayi cikin blanket kaman Bata da Rai, can taji duk wasu qaran da take ji ya tsaya cakk, ta sauqe ajiyan zuciya tana share hawayen idon ta.

Bata gama samun nutsuwa ba taji ana buga qofar dakin ta da qarfi kaman za'a balla shi, kurma ihu tayi ta sake duqunqunuwa cikin bargo, gaba Daya ta jiqa da zufa jikin ta na mazari, ta rasa wani kalan addu'a ya kamata tayi.

Tunawa tayi da lokacin da irin hakan ya faru da ita a gida, bayan anyi renovating gidan su ta gwada kwana ita kadai a dakin ta, ba tare da ta nemi Yar Taya kwana ba kaman Yanda take yi ko yaushe, same abubuwan da ta ji yau su taji ranan, Amman ihun da tayi na farko ya jawo hankalin Ammi ta shigo ta same ta cikin wannan yanayin ta rungume yarta tsamm a jikin ta tana Mata addu'a har ta samu bacci ya dauke ta tun daga ranar Bata sake kwana ita kadai ba, gashi yanzu Allah ya kawo ta wurin wancan Mara imanin shi Bai damu ba ko mutuwa zatayi bayi da asara, kuka taci gaba dayi tana Kiran sunan Allah tana jin tausayin  kanta da irin rayuwar da zatayi cikin wannan gida.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now