chapter 26

255 34 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
            (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

      RUBUTAWA

      UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

26🍎

Da azama ya miqe yayi kanta, ta iba a saba'in tayi waje ya dawo seat din shi ya zauna Yana fadin
"Da kin tsaya na gwada Miki qarshen marasa kunya, mtsww! shegiya kina Nan kaman an daura ma muciya zani".

Biki saura one week ana ta shirye shirye ba Kama qafar yaro Sahar ta zage tana ta hidindimu gaba daya ta zamo busy Bata da lokacin Kan ta.

Da dad ya tilasta wa Ahmad ya tafi Bauchi duk da Bata so Haka ya tattare ta suka tafi saboda babu abin da zai iya wurin su Feenah idan Bata tare da shi.

Imran kam ya Dade da tsufa cikin garin Bauchi satin shi biyu da zuwa ya tare a L mansion Yana zuba soyayya shi da Eesher.

***********

Da gudu ta shiga dakin ta rungume Feenah Wanda fitowar ta daga wanka kenan, ta kamo hannun ta tana kallon jikin ta da yasha gyara.

"Kai sister Kinga Yanda kike qyalli kuwa har wani kashe Ido kike, nide kiyi haquri kada ki zautar mun da Yaya" ta qarasa fada hade da dariya.

Tabe baki Feenah tayi tace
" ke Kika ji wurin Kuma Yar wulaqanci kawai, tun yaushe nake jiran ki kin shanya ni sai yau Kika ga Daman zuwa"

" Ayyah sister na fada Miki fa sai Yaya na ya dawo damu zo tare"

" Yau ne ya dawo?"

" Aa tun last week ya dawo ya danyi covering aikin office ne kafin mu taho"

Kawar da kanta Feenah tayi Chan qasan maqoshi tace
"dama Bai dawo ba, yayi ta zaman shi a can wallahi"

Da sauri Sahar tace "Mai Kika ce?"

" No babu komai"

Sahar tayi qwafa tace
" Zaki maimaita"

Feenah na cikin saka Kaya sai ga Eesher ta bankado qofar dakin ta shigo Dan ta samu labarin zuwan su Sahar a wurin Imran, ta fada jikin ta tana "oyoyo sister"

Dan ture ta kadan Sahar tayi tace
" Sister baki yi Mana sallama ba kawai Kika shigo wa mutane daki, wallahi da ke ce matar Yaya na da ya koya Miki hankali"

Feenah tace
" Ohh kice yayan naki ba sauqi kenan"

"No aikuwa bayi da tsanani shidai dan qa'ida ne idan Zaki bi dokokin shi daku zauna lafiya"

Feenah ta tabe baki ta cigaba da saka kayan ta.

Eesher ta juya tana kallon Sahar tace
" Sister Yaya hanya Ina Kika bar Mana angon mu baizo yaga amaryar sa ba"

" Ango na wurin yaya Imran, yaje yaji dalilin da yasa yabar aikin sa ya dawo Bauchi ya zauna"

Murmushi Eesher tayi tace
" Ayyah kuyi Masa haquri yazo ganin saheebar sa ne"

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now