chapter 42

274 41 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

42🍎

"Ban Gane ba"

"Kamarya Baki Gane ba Eesher? Ya Ahmad da ya Imran caca suka saka Akan zuciya ta, idan har nace Ina son ya Ahmad Nan da sati biyu ya Imran zai bashi 60 million naira, me yasa shi Bai San halacci bane? After all that I have done to him he is putting all my love and sacrifices on a bet?" tana kaiwa Nan ta fashe da kuka.

Duka Eesher ta Kai Mata a baya tace
"Tashi wawiyar banza, ke duk abin da paka Miki sai ki bude Baki kina kuka, shi yasa ya samu Daman Raina ki Yana Miki abun da yaga dama"

Juyo da ita Sahar tayi tana fiskantan ta tace
"Zage dantse dakiyi mu hadu mu kowa ma Dan iska hankali, babu tausayi babu rangwami ki share hawayen ki muna tare dake"

10:30pm

Bude ma Eesher marfin mota yayi ya zaga zai shiga driver seat ahmad yace
"Friend ku kwana a Nan Mana tunda akwai enough rooms"

"babu abin da zai saka na kwana a cikin gidan Nan haka kawai neman a Hana ni sakewa ni da madam dina? Yanzun ma sa'a kaci na yarda nazo Nan muna qarasa wannan aikin Nan da sati biyu zamu koma 9ja ni bani son zaman qasar nan" Yana Gama fadan haka ya shiga ya tada motan suka bar gidan.

Juyawan da Ahmad zaiyi yaga babu Feenah babu sahar, sai hango su yayi suna Shirin shiga ciki, ya wuce bedroom dinshi yayi Shirin bacci Yana jiran zuwan ta har 12:00am shiru, ya tashi ya tafi dakin ta ya same su suna barci, a hankali yake tapping din qafarta har ta bude Ido tana murtsuke su, ganin shine yasa ta hade Rai tace meye?.

"Ki tashi mu tafi daki mu kwanta Kinga dare yayi nisa sosai"
" Ni Babu inda zanje ka tafi kawai a Nan zan kwana"

Jinjina Kai yayi a tunanin shi Dan taga Sahar ne yasa taqi kwanan dakin shi yace
"Ok naji Amman idan lil sis ta tafi kada ki kuskura ki sake dawo min daki"
" Zuwa lokacin Allah zai kawo Yanda zanyi, Kuma zan duqufa ma addu'a Allah ya yaye mun wannan jarabawan tsoron da nake fama dashi" ta koma tayi kwanciyar ta.

Shiruu yayi Yana kallon ta yanzu Kam ya tabbatar Feenah tana da aljanu don Yanda take Masa magana a tsatsatsaye tana kallon cikin idanuwan sa ba ita Daya bane akwai matsatsaku a kan ta, ya ja qafan shi yayi gaba.

Har 1:30 barci yaqi zuwa masa, yana jin kanshi wani daban rashin Feenah a kusa dashi ya Hana shi Jin dadi kallon gadon yayi yaga ya Masa fadii sosai Yana missing Yanda Feenah ke zuwa ta takura idan tana juyi a cikin barci, sai wuraren asuba ya samu barci ya dauke shi.

9:01am

Ya sauqo cikin farin suit da ya amshi jikin shi sosai qamshin oud al Amer Yana tashi a jikin sa, tadi suke yi suna qyalqyala dariya ita da Sahar kallo daya tayi Masa ta dauke Kai ta hade rai, a take annurin dake fuskan ta ya bace batt.

Ya qaraso Sahar tayi hugging dinshi ta gaida shi Yana zuwa jikin Feenah ta ja baya da sauri tana jifan shi da wani mugun kallo, ya jawo ta kusa dashi Yana kallon idon ta da ruwan masifa ke kwance a ciki yace
"Wifey yau babu gaisuwa ne? Ko har yanzu aljanun kin Basu tafi bane?"

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now