chapter 44

287 34 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

44🍎

"Feenah!!! Feenah!!! Ki tashi a wurin dan Allah, ki bude idon ki mota a....." Maganar Sahar ne ya katse ta saki wani razanannen ihu ganin Ahmad ya shiga gaban motan da gudu ya tura ta gefe, shi Kuma motan ya bige shi ya Fadi a gefen hanya.

Da sauri ta bude idonta ta Jin faduwar wani Abu a gefen ta, a tare sukayi kanshi suna kuka ganin Yanda ya riqe qafarshi Yana jujjuya kanshi cikin zafin ciwo, Sahar ne tayi azancin Kiran ambulance Feenah kuwa Banda kuka babu abin da take yi.
"Na shiga uku na, wayyo Allah na wayyo Ammi na, Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" shine kawai abinda take faman maimaitawa.

Bude idon shi da duk sun kada sunyi jaa yayi ya sauqe su a kanta cikan dauriya yace
"Da'alla rufe min baki, da wanne Daya kike so naji? Duk laifin ki ne baqauyiyar yarinya, haka ake tsallaka titi a garin ku ba'a duba ko mota na zuwa sai kawai mutum ya shiga Kaman gidan su ko? Idan mun koma gida zakimin bayanin dalilin da yasa Kika jimin ciwo Kuma sai kin biya ni jini na"

Cikin tsiyayar hawaye tace
" Allah sarki ya Ahmad kayi haquri kodan ciwon da kaji ka daina masifan Nan Dan Allah, Kuma fa ciwon baiyi jini ba kake cewa zan biya ka, ka duba da kyau ka gani buguwa ne babu ko digon jini a wurin"

Wani sanyi yaji cikin ranshi rabon da Feenah tayi magana Mai tsayi dashi irin haka har ya manta, he missed her voice, murmushi ne ya subuce Masa ya duba qafan yaga da gaske ne Bai zubar da jini ba yace
"Laa Ashe babu jini Amman na targade Kuma shima bazan haqura ba sai na rama"

Tabe Baki tayi tace
" Ka Rama Mana ni me ruwa na, yanzu dai ga ambulance ya qaraso bari su saka ka cikin mota muje asibiti a duba maka buguwan"

Galla Mata hara yayi yace
" Waye zasu dauke ni su saka ni cikin motan? Ance Miki ni qaramin yaro ne da zakice a daukeni? Su tafi abun su zan iya tashi da kaina'"

Zuba mishi Ido tayi taga ikon Allah, sai fafutukar tashi yake Amman ya kasa, ta miqa mishi hannunta tace
"Riqe ni, na taimaka maka ka tashi"

Dariya yayi Yana kallon siraran hannun ta Mai Kama da tsintsiyan kwakwa, ya  saka hannun shi a cikin nata, ja Daya yayi Mata ta Fado jikin shi gaba daya, ta shagwabe fuska tace
"Haba ya Ahmad daga taimako sai Nima ka Yarda ni?"

" To ance Miki ni sa'an ki ne? Ko Kinga girman mu Daya da Zaki miqo min bulogarin hannun ki kice Wai na riqe?"

" Kayi maganin gobe, bazan sake taimakon ka ba tunda Kai duk abin da aka maka laifi ne"

" Ai da na Bari motan Nan yabi takan wannan bakin kin, muga da abin da Zaki dinga rashin kunya"

Ta bude Baki zatayi magana, Sahar tayi saurin tare ta
"Enough of this argument please!! Yaya Ahmad Bari wannan nurse din ya taimaka maka ka shiga mota mu tafi asibiti kada ciwon yayi tsami"

Saka shi a cikin ambulance din akayi Feenah da Sahar suka shiga motar da suka zo dashi Sahar na driving Feenah Kam ko tuqin Keke Bata iya ba, da suka je asibiti aka duba qafan bugewa ne kawai babu kariya ko targade aka shafa Masa magani aka daure qafan sannan aka rubuta mishi na Sha suka koma gida.

Zuwa washe gari qafan Ahmad yayi sauqi sosai yaci gaba da sabgogin gaban shi, Feenah na ganin haka suka koma gidan juya, fadan yau daban na gone daban Bata mishi magana idan ba ya zamo dole ba gashi sai wani Jan baya_baya take yi dashi, yanzu Kam Ahmad ya saduda neman sulhu yake ta ko wani irin hanya Amman Feenah taqi bashi fuska.

"Sister tun jiya nake binki ki fadamun next plan dinmu Amman kinyi briss dani, lokaci na qure Mana fa, sauran 5 days burin ya Ahmad ya cika, bansan me zaimin da zaisa nace Ina son shi ba, please ki taimaka min nayi saving dignity na"

Sauqe numfashi Sahar tayi tace
" Sister bawai banison taimakon ki bane, Ina tsoron kada wani Abu ya sake samun Yayana ne, shi kadai nake dashi Kuma Ina matuqar qaunar shi fiye da rayuwa ta, bazan jure ganin wani Abu Yana cutar da shi ba, inason ganin shi cikin farin ciki haka kema Ina son ganin ki cikin farin ciki Amman gaskiya yanzu tsoro ya darsu a zuciya ta Ina ganin kaman bazan iya ba"

Zama Feenah tayi kusa da ita take "sister kaman Yanda ya Ahmad yake da muhimmanci a wurin ki Nima haka yake da muhimmanci a wurina saboda shi miji na ne, nayi Miki alqawari babu abin da zai sake samun shi insha Allah sai muyi plan Mara hadari kinji?"

"Shikkenan yau qarfe nawa Zaki tafi school?"

" 2 o'clock"
" To idan Zaki tafi ki barmin wayanki a Nan akwai wata friend Dina a school din zan saka ta nema Mana wani saurayin da zamu biyashi yayi acting kaman saurayin ki, sai na saka ya turo love message ta wayan ki na nuna ma ya Ahmad ya gani Kinga a nan zamu Gane percentage na trust dake tsakanin ku, daga Nan Kuma dan tursasa shi ya bini school dinku da sunan zamu dauko ki, sai ya hadu da wannan guy din tare dake ki tabbatar kin sake mishi fuska ta Yanda shakku dai 'darsu a zuciyar Yaya Ahmad sai mu gane ko Yana kishin ki da yawa.

Gyada Kai Feenah tayi tace
"Very nice idea sister, Bari na tashi na shirya yanzu Dan sauran qiris lokaci yayi"

5:00pm

Sahar ta qaraso wurin da yake zaune Yana Shan iska ta zauna, ta miqa mishi wayan Feenah tace
" yaya kaga Feenah ta manta wayan ta a gida gashi tun dazu sai kiran ta akeyi, ka tashi mu Kai Mata kaji bansan ko urgent call bane"

" Lil sis kina da saka damuwa ma ranki, ki haqura ta dawo Mana sauran one hour kawai"

" Ayyah Yaya na fada maka kiranta fa akeyi maybe batama San inda wayan yake ba, Kuma Ina son Naga gari kaga rannan da muka fita bamuyi nisa ba muka hadu da tsautsayi please ka shirya mu tafi"

Tsaki yaja yace "bani wayar na gani waye me kirantan, da sauri Sahar ta miqa mishi, ya fara dubawa a take idon shi ya sauqa kan messages barkatai da aka turo ya shiga ya fara duba su daya bayan daya, ranshi ba qaramin baci yayi ba ganin kalaman soyayya da wani gardi ke tura ma matan shi, ya miqe hade da fadin "tashi mu tafi"

kallon shi tayi sama da qasa shirt be da three quarter a jikin shi tace " Yaya Ahmad baka shirya ba ai bare mu tafi"
" Yanzun tsirara Kika ganni?"

Ta girgiza Kai hade da fadin
" A'a Allah ya baka haquri"

Sunyi nisa da tafiya Sahar ta tura ma mutumin da sukayi hire message, suna zuwa wurin da aka yi musu kwatance suka samu Feenah da wani bature suna zaune, bayan shi kawai Ahmad yake iya gani sai fuskan Feenah dake kallon wannan mutumin tana sake Masa murmushi Mai tsada da alaman tana matuqar Jin dadin maganar da suke yi.

Already ran Ahmad a bace yake, ya cakumo wuyan rigan wannan saurayin ya juyo da fuskan shi Yana kallon shi sannan ya Kai Masa punch a take hancin shi ya fara fitar da jini,
"Who are you? And who gave you the right to sit and talk with my wife?" Duka yake Kai Masa ta ko Ina yaqi bari ko magana yayi, da qyar aka raba su, ranar su feenah sunga tijara don qasan ba kamar Nigeria bane, a lokacin suka Kama Ahmad suka gargame shi"

Feenah tayi kuka har ta gode ma Allah ranan Yanda suka ga dare Hala suka ga Rana, duk da saurayin yace ya yafe a bar Ahmad ya tafi haka police suka qeqashe qasa suka ce Basu yarda ba, sai ya kwana a cell saboda ya zubar da jini, Feenah tayi nadama da danasanin wannan plan din da suka shirya tun daga na farko, ko yaushe Ahmad ne ke cutuwa a cikin wannan test din, ita Kam yanzu ta haqura zata Bari Ahmad yayi winning bet din shi da imran..................🧚

#vote
#share
#comment.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now