chapter 48

297 38 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
  
         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

48🍎

Tana shiga ciki sukaci Karo da matan yaya Muhammad zata fita Feenah ta tare ta tana kuka tace
"Aunty laweeza Yaya jikin baba suna inane yanzu? Ina jiddan take?"

" Ki kwantar da hankalin ki Feenah jikin baba da sauqi yanzu ma asibitin zanje, jidda Kuma tana ciki wurin mama"

Batabi ta Kan jidda ba suka shiga mota tare da aunty laweeza sukayi asibiti

Suna isa asibitin aunty Laweeza  Ta musu jagora xuwa dakin baba, dasuka qarasa kofan dakin suka samu sauran mutanen gida kowa yayi jungum jungum ana ta jiran aji Halin da yake ciki.

Doctor neh yafito daga dakin da Baban yake ciki yana fitowa kowa yayi  kanshi ana tambayansa ya jikin baba, Dan jimm yayi kafin ya fara basu haquri yana fadin
"I'm sorry gaskiya patient dinmu ya samu paralysis, munyi iya qoqarin mu wurin ceto rayuwarshi yanzu haka ya farka yace yana son ganin Nafeesah"

Da sauri ta shiga ta samu baba na kwance ya juyar da kanshi ta gefe.

tai mishi sallama ta qarasa gefensa tana kuka ta riqo hannunshi, ya juyo Amman baya iya motsawa koh kadan, murmushi  yasakar mata yace
"Nagode miki diyata haqiqa kin cancanta kowani uba yayi alfahari dake,  ke 'ya ceh tagari,  duk wani qoqarinki kinyi don ki sanya ni farin ciki, nagode miki Allah saka miki da alkhairi,
ku riqe yan uwanku ku qaunace su Dan naka naka ne komin munin shi amman Nikam yanxu nasan na haifi 'ya da tazamo min guba a rayuwata na haifi yarinyan da xata qarasa ni, Amman Allah ya gani nayi iya bakin qoqarina akan Hauwa'u  na fita hakkin ta. 

Kici gaba da yin biyayya wa mijinki Allah ya sauqeki lfy Allah ya baku zaman lfy, nagode Nafeesa Allah ya Miki albarka dake da mahaifiyarki Allah ya shirya min ku da sauran yaran"

kuka Feenah ta fashe dashi ta rungume babanta tace "insha Allahu babu abnda xai sameka baba insha Allah zaka tashi kuma sai Allah ya saka maka".

bayan ta fito aka bama sauran izinin shiga su ganshi daya bayan daya daga baya Kuma aka ce su tafi gida domin baba Yana buqatar hutu sosai.

Suna shiga gida suka dunguma bedroom din jidda, suka sameta a kwance gatanan ga yanda take,  tana isa wurinta ta tsuguna a gabanta cikin kuka tace
"Jiddah Whyyy? why Jiddah? Me muka yi miki da zaki saka mana da irin wannan abun? Miye kike nema kika rasa a duniyan nan? Menene bamu baki ba? duk wani abinda kikeso kin samu"

Jiddah tace "don Allah Nafeesah kuyi haquri ku yafe min haqiqa nasan na aikata babban kuskure son zuciya ya halakar dani,  naso abnda yafi qarfina ni bansan wata iriyar sakarya ba ceh da naso mijin yar uwata sonda nake yi wa Ahmad koda yake baxan ma ceh sonda nakeyi masa ba, son da nakeyi wa dukiyarsa ne yajawo min wannan Halin da nake ciki, son zuciya da son duniya shi yasa ni a halaka, na manta da lahira nah yanxu wa gari ya waya?

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now