chapter 28

236 34 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

       🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
  
Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

28🍎

Mama yanzu shikenan bazan taba samun abin da nake so ba, Feenah ta riga ta ruguza min buri na, please ki barni na mutu na huta da baqin cikin su.

Buge Mata Baki mama tayi tace
"Kull na sake Jin wannan maganar daga bakin ki jidda, ke wa yace ana haqura da burin rayuwa tun da wuri? Idan kina son Abu to ya zama wajibi kiyi yaqi Akan shi, ke dai kiyi ki samu lafiya mu koma gida musan abin yi".

Share hawayen fuskar ta tayi ta dauko wayar ta dake ta faman ringing, tsaki Taja ganin sunan Feenah bayyane Kan screen din wayar ta maida wayan ta ajiye
"Wannan yarinyan anyi baqar mayya wallahi, haba! So take yi ta kashe ni ne?"

Dauko wayan mama tayi ta miqa Mata tace
"Ungo dauki wayar"

Shagwabe fuska tayi tace
"Amman mama meyasa?"

"Saboda ba'a kashe zafi da zafi, matsala ta dake Baki da wayo ko kadan, tunda ta gwada tana tausayin ki to da wannan tausayin dakiyi amfani ki raba ta da abin da take dashi, karba ki Kira ta"

Wani murmushi hawas tayi ta karbi wayan, tana Shirin Kiran Feenah sai Kiran ta ya shigo.

Sai da Kiran ya kusan tsinkewa kafin tayi picking ta qara a kunne.

"Hello jidda"

Lanqwasar da murya tayi kafin tace
" Kin Kira ne kiji ko na mutu ko?"

"Aa aunty jidda wallahi bani da niyyar cutar dake ko kadan"

" Qarya kike yi Feenah Daman burin ki kenan kiga na wulaqanta, idan Kuma ba Haka bane Mai yasa Kika auri Ahmad bayan kin San Ina son shi? Ashe ba Zaki iya sadaukar da soyayyar ki saboda na rayu ba?"

" Nifa bani son shi, ban taba son shi ba, tilasta min yayi na aure shi please jidda ki yarda da ni"

Dira tayi daga gadon ta daka tsalle tana fadin "yess" kafin ta maida wayar kunne tana tarin qarya, sannan tace
" Idan har kina so na yarda da ke sai kin rabu da Ahmad na aure shi hakan ne kawai zai tabbatar min da gaskiyar maganar ki"

" Yanda kike so Haka za'ayi, nayi Miki alqawarin nan da Dan wani lokaci zan saka Ahmad ya sake ni"

Cikin farin ciki suka yi sallama, ta kashe wayar tana ajiyan zuciya tana juyawa suka yi Ido hudu da Eesher.

Kafin tayi wani magana ta dauke ta da Mari, dafe cheek din ta tayi ta dago Ido tana kallon Eesher da take ta huci da alaman ta Gama Jin conversation dinsu da hawas.

"Ahir dinki Feenah, ahir dinki da abin kunyan da kike son ki jawo mana, wallahi duk ranar da Kika yi kuskuren barin gidan mijin ki Kika saka zuciyan baba bugawa Allah ya Isa ba zamu taba yafe Miki ba.

Kuma na fada Miki aure ba abun wasa bane, gidan da Zaki tafi gidan zama ne na HAR ABADA ba na wani qanqanin lokaci ba, Feenah babban kuskuren da Zaki tafka Wanda zai ruguza Miki Jin dadin duniyar ki da lahirar ki shine kashe auren ki Akan mutanen da Basu San darajan ki ba ko kadan, kin fi kowa sanin ba qaunarki suke ba.

And daga ranar da Kika bar gidan Ahmad da sunan rabuwa ba mutuwa ba kada ki mayi tunanin kin taba sanin wata Mai suna Aisha, and from that day I will only be hating you, bazan sake Baki wuri a cikin zuciya ta ba, idan Kinga dama ki fito mu Kai ki idan Kuma kinso tun daga Nan ki kashe auren, banza! wawiya! shashasha!" Ta juya tayi tafiyar ta.

Har suka Isa gidan, Eesher ko kallon wurin da Feenah take zaune Bata sake yi ba,
Da aunty Sumayya qanwar dad, da maman Adnan ne suka shiga motar da amarya take, aka sake diban zuga yuuu sai gidan amarya.

Gidan Duplex ne Mai tsananin kyau pha'ixer da miss danzango suka fara zagaye gida suna kashe qwarqwatan idanu.

Duk yanda suka so su zaga gidan gaba daya sun kasa Dan tsananin girman da yake dashi, ga qofifi sunqi buduwa, bayan qofar bedroom din amarya dake bude su Basu ga wurin da zasu saka key su bude qofan ba ma.

Bayan mutane sun watse umma sulaiman ta sake zama tayi ma Feenah nasiha Wai Ita bataso a wahalar da Ahmad tana tafiya hadiza aminu Ali ta zauna ta hure Mata kunne a take ta watsar da duk nasihar da umma ta mata.

**********
"Kaga boss sabon ango duk wannan zumudin na zuwa wurin  amarya ne?"

"Dan ci ubanka Imran idan baka rabu Dani ba, Kai ance maka kowa Dan iska ne irin ka? Akan me Dan zauna Bata lokaci na Kan wannan tatstsiyar yarinyan? Idan zaka tashi mu tafi to, idan Kuma ba zaka tashi ba kaga tafiya ta gobe Monday akwai aiki"

"Wani aikin? You are not serious, da'alla malam ka daina waskewa kana Raina wa mutane hankali,
Ya juya ya kalli sauran abokan su dake dakin yace
"guys ku tashi mu tafi mu kaishi na lura idan Bamu yi sauri ba zai iya tafiya Kai kadai".

9:02 abokai da ango suka qaraso  akayi duk abun da ya Dace suka yi ma amarya da ango kalan nasu wa'azin na qala qato suka tattara suka tafi Ahmad ya raka su aka bar Feenah ita kadai.

Har yanzu Eesher fushi take yi da ita kowa yayi Mata sallama kafin suka fita Amman duk da fiskan ta na rufe da mayafi tasan Eesher Bata Mata magana ba Dan tana shaida muryar ta ko cikin barchi ta Mata magana zata gane ta.

Kuka take wiwi yau gata cikin wani sabon duniya ta kwanta a Kan carpet din dakin a Haka har bacci ya dauke ta.

Ahmad da ya dawo daga rakiyan su imran Bai ko kalli side din dakin Feenah ba ya dauki laudan kaza da drinks wanda Imran ya tilasta shi ya siya ya wuce dashi kitchen ya juye Kazan a plastic bowl ya saka a fridge, sannan ya Danna wani Abu wutan gidan gabaki daya ya mutu ya shiga nashi dakin.

Washe gari da safe

Kiran assalatu na farko a kunnen Feenah, ta tashi ta cire kayan da aka kawo ta dashi tun jiya halin da take ciki ya Hana ta canzawa.

Ta shiga toilet tayi wanka hade da alwala, ta fito ta shafe jikin ta da lotion, sannan tabi duk wani lungu da saqon jikin ta da turaruka masu sanyin qamshi, ta nufi wardrobe ta bude, Kaya ne birjik a ciki kaman super market ta tsaya tana dube_dube hannun ta ya sauqa Kan wani riga da wando ta dauka ta saka.

Wandon nada Fadi kadan sannan rigan takai Mata har quiwa ta saka hijab dinta ta tada sallah, sai da Rana ta fito kafin ta tashi ta nade darduman sallan ta shiga ta wanko toilet dinta ta danyi light makeup a fuskar ta sannan ta shiga store neman tsntsiyan shara.

Banda wasu kalan injina Ita babu abin da ta gani cikin wannan store, Chan idon ta ya sauqa Kan wani vacuum cleaner da ta taba ganin irin shi a TV, sa'ar ta Daya komai na gidan sabo ne Dan Haka a jikin shi akwai manual.

Ta dauka ta tafi dakin ta dashi ta karanta manual din Tass sannan ta kunna ta share dakin tayi dusting ta ja cleanern zuwa dakin Mr arrogant dinta.................🧚

_More comments_ _more typing_ 😎

#vote
#share
#comment.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now