chapter 16

258 32 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

🌹HAR ABADA🌹
(bazamu rabeba)

LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

RUBUTAWA

UMMU NAJMA

DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

Special gratitude to
Maman mamy shalele
Ammyn khairat golden girl
Ruqayya ikra ummu sultan
Ina matuqar godiya da gudumawar da kuke bani na gode da kulawa❤️

16🍎

"Imran please let me be, I need to rest."

"I know you are the boss and you have the right to rule, Amma baka Isa ka mulke ni ba Dan ubanka, Kuma Bari kaji ni ba mazinaci bane idan ma tsoron abin da ya saka kake shiga tsakani na da qanwar ka kenan to ka daina daga yanzu nabar shiga sabgar ku gabadaya kowa yayi damuwan sa. Ya juya yayi tafiyar shi.

Bin shi a baya Ahmad yayi Yana fadin "wait Imran ba abin da nake nufi ba kenan listen to me"

Amman inaa Imran ya hau dokin zuciya Bai tsaya yaji abin da yake fada ba ya fita tare da rufo qofan da qarfi har sai da office din ya amsa.

Juyawa yayi ya buga center table da qarfi hade da fadin "darn it"
Yayi wurgi da glass pigeons statue dake Kan table din a take suka yi rugu_rugu.

Ya zauna Yana fitar da huci Mai zafi a ransa Yana Allah wadai da tunanin da ya saka yake zargin Imran, shifa aboki na ne tun muna yara , nasan shigan sa nasan fitan sa nasan irin abin da zai iya aikatawa Mai yasa nayi wa kaina haka? ohh God!.
Ganin tunani bazai ficce shi ba yasa ya dauki wayoyin sa ya yi gaba.

**********

Zaune take tana wanke shinkafa amman hankalin ta bayi jikin ta, ta dulmuya cikin tunani, yau kwana biyu kenan da zuwan su jamb office ta rasa yanda zatayi ma baba bayani yanda zai fahimta ya barta ta tafi Abuja.

Sallamar da tajiyo ne ya jawo hankalin ta ta zuba ma qofar shigowa idanu,
Tsallen murna ta fara ganin aunty fatima babbar Yar mama zainab Wanda take zaune a Abuja.

Da gudu Feenah ta ajiye qoqon dake hannunta ta rungume ta tana dariyar farin ciki.
"Aunty fati sannu da zuwa, sauqar yaushe? gaskiya Kin shammace mu."

Dariya aunty Fati ta yi tace
"Feenan Ammi sarkin surutu, ko ruwa ba Zaki barni Nasha ba?"

" Sorry auntynah shiga Kisha ruwa, Amman Ina Jakar ki."

Bata juyo ba ta shige dakin mama tare da fadin "Yana hannun su Hassan da Hussain."

Godiya ma Allah Feenah take ba qaqqautawa Allah ya kawo Mata dalilin tafiya cikin sauqi, Amman tasan sai Tasha artabo da Ammi kafin ta barta ta tafi Abuja.

Bayan aunty Fati ta huta Feenah ta shigo Mata da qaton traveling bag da ta karbo a hannun su Hassan ta nemi wuri ta zauna tana jiran tsara ba.

Mama sai zabga Mata harara take yi ita Kan ko a jikin ta, aunty faty ta miqa mata wasu silver earrings,
"Gashi Feenan Ammi, kiyi haquri babu yawa Ina Kan hanya ne ba zama nazo yi ba shiyasa banyi tsaraba da yawa ba."

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now