part 40

24 3 0
                                    

nan jamila tashigo dakin tace ai likita baya kirana ina matar datace likita nakirana

saince yanzu haka batamasan inda aka aikotaba shine tashigo nan dakin

jamila tace hakane kikwanta kihuta

wajan karfe shadaya nace malam yazo idan yaji shiru bandawoba shine yazo yatambaya aka hanashi shiga nayiwa wata nose magana munada bako a waje idan yashigo a barshi yashigo taje tasamu kuwa yazo an hanashi shigowa ciki tayi magana aka barshi ya shigo takawoshi har dakin

nan muka shiga bandakin na nuna masa saratu nace muyi saurin dauketa kar jamila ta farka yacemini mubari sai gobe nace a a domin daga gobe na tabbata wlh bazamu kara samun damarnanba sabida daga gobe asibitin zaikoma kamar kasuwa dakuma gidansu sabida murna da farin ciki dakuma yan uwa da abokan arzuki musamman dan kasuwane mujinta kaga bamu da mafuta idan muka huce yau kenan

natashi nakamat tamike tsaye yariketa nariketa muka fita a hankali kamar barayi mukayi sa'a bamuga kowaba nayi sauri yasata akan mashin nashi nahau nariketa muka tafi muna zuwa muka shigar da ita dakinmu mukayyo waje muka hau mashin yamaidani asibiti yajuya yakoma ina shigowa natarar da jamila ta tashi da hisham a hannunta yana kuka yatashi yananeman nono nashigo dakin a durkushe kamar marar lfy

tayi mamakin ganina domin ta daukama nashiga bandaki

tace saratu lfy daga ina kike jinake kina bandaki ai ina kikaje

nazauna abakin gado nace cikina kemini ciwo sosai nara yanda zanyi shine naje nadan zaga asibitin dakyar kafinnan nadanji dama dama

aidakin tasheni kingayamini gashi yaro nata kuka kukansa yatasheni daga barci  wlh

ayya kiyi hakuri jamila narikice sabida azaba wlh

to kihuta gashi kibashi yasha mebi yakama yanzu tunda dazu yaki shama

nace to nakarbeshi wlh inabashi ya amsa kuma nonon yakawo ruwa nayi mamaki sosai

washe gari aka sallamemu da yamma muka koma gida naga gatan dangi yanda suke mutukar kaunar saratu da danta alhajin yadawo naga soyayya a gurinsa ya kware takomai irin namijin danake fatan nasamu a rayuwa amma bansamuba

kuma wlh alhaji bay ganeniba kokadan sabida bazaman garin yakeba bare zaman gidan

naga gata annuna mini gata nasamu komai da komai danake bukata amma haryanzu babu kaunar yaronnan a zuciyata sai gabar dake tsakanina da uwarsa saratu ita tashafeshi

ita kuwa saratu tunda muka kaita washe gari tafarka naje gidan amma banbari ta ganniba nabawa malam iro kudi masu yawa yasai mata abinda yadace har tasamu lfy sannan mufara bata wuya

bayan wata guda muka fara azabtar da ita abinci sai munga dama muke bata gata a daure wanka kuwa da sallah muna barta tanayi tuntanayi har tadawo tadena sabida wuya da azabar da take ciki kullum tambayarta ga malam iro shine

menai maka dan allah asanina banida makiyi ko makiyiya a rayuwata amma karabani da dangina mijina dakuma dana ina dana yake dana dana inayake wayyo kubani dana dan Allah

hakaday kullum take gaya har tafita daga hayyacinta sabida tambayar mijinta dakuma danta tadawo mai tabin hankali idan haukan yatashi gaskiya da kyar malam iro yake iyawa da ita

shekarar hisham goma muka hadu dake bilki a wani shago nagani kefa yar hannuce shine kekuma kinganni hajiya muka hadu shikenan muka zama aminan iskancin juna

yana shekara goma sha biyu alhaji yace mukoma a merika da zama muka tafi kuwa muka zauna acan

amma dukda haka ina zuwa Nigeria bada sanin alhajiba dannaga komai yayake tafiya a wajan malam iro

GIDANMU KOH GIDAN MIJINAWhere stories live. Discover now