CHAPTER 1

14.5K 537 17
                                    

A/N
Hello guys this is a new book that I am posting I will be posting this everyday by the grace of God Insha Allah also please most of the media that will be in this book do not belong to me they belong to their owners so credit goes to them. Please if you are not following me click that follow button share some love like share and comment. I post it before editing so it's not edited there will be errors.

Happy reading

Bismillahirrahmanirrahim
Da sunan Allah Mai rahma Mai jinkai Ina farawa da sunan Allah Allah ya nuna Mana mungama lafiya. Ameen

SOKOTO (Birnin shehu)

Tafe suke su biyu suna tafiya sanye da uniform din islamiyya milk and brown dayar na rike da Al Qurani mai girma da wasu littattafai a hannun ta.

Yayin da dayar take rike da wata jar jaka a hannunta. Mai jakar naji tana fadin "Dan Allah ki taka mutafi kinga dare ya farayi mana"

Wacce ta Kira da nafisa na kalla naganta farace saidai irin mutanen nan ne da akecewa (tanned skin) gashin girar ta ba wani Mai yawa bane.

Tanada manyan ido golden eyes ne da ita tanada dogon hanci har baka sai peach lips da Allah ya bata.

Ta buda baki tace "wlh Deeza iyakar saurin da zan iya kenan. Sannan hanuwana sun fara ciwo saboda jakar da ta tsinke."

Suna tafiya suna labari har suka kawo gaban wani babban mansion gabanshi an rubuta MODIBBO FAMILY HOUSE deexa "tace mu shiga ciki inda hajiya kamin ki shiga gida" ta fada tana nuna wani part.

Yi tayi kamar Bata jita ba suka shiga gidan part part ne suka nufi sashin hannun dama na farko

wani upstairs suka shiga a sitting room dinda aka kawata da komai jah da baki suka iske dattijuwar da akallah zatayi shekara 47 a duniya zaune a kan 2 sitter

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

wani upstairs suka shiga a sitting room dinda aka kawata da komai jah da baki suka iske dattijuwar da akallah zatayi shekara 47 a duniya zaune a kan 2 sitter.

Dukawa sukayi har kasa sukace ammi Ina wuni tana Mai fadada murmushin ta tace "lafiya kalau ya karatu?"

Suka amsa da lafiya kalau. Deeza tace ammi zan isa gida tace toh "Hadiza kigaisar min da maman ki"

Amsawa Deeza tayi da toh tana fita nafisa tayi sama zuwa dakinta Mai queen size bed purple komai purple and white

Amsawa Deeza tayi da toh tana fita nafisa tayi sama zuwa dakinta Mai queen size bed purple komai purple and white

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Shiga tayi bathroom dinta tayi wanka ta chanza kaya zuwa wata maroon din doguwar riga ta sauko kasa.

Saukowar ta yayi daidai da isowar wasu maza hudu ta gaida su tace ya jalal Ina wuni ya khaleel Ina wuni ya ya Hydar ya Sadiq Ina wuni?

Mazan suka amsa da "lafiya kalau sister" Sadiq yace "yi hakuri sis yau koda 8 lokacin tashinku islamiyya yayi ina nesa Ina gidan daddy, sannan kinga tin lokacinda baba driver yabar aiki ba'a samu wani ba shiyasa kuka dawo kasa "

Tace "lah ya ba matsala ai munyi excercise"

Tare suka nufi dinning area suna zama kofar shigowa cikin gidan na budewa chan wani dattijo zaiyi shekara 54 ya shigo dinning area din duka yaran su duka suka gaida shi.

Amsa musu yayi cikin sakin fuska yace "ku zauna muci dinner din koh?" jalal da khaleel sukace sunci a gida yace toh kutashi kutafi kunbar iyalan ku a gida sukayi musu sallama suka fita

WACECE NAFISAH??

Nafisa Umar Modibbo shine cikakken sunan ta nafisa ya'ce a gun Alhj Umar Modibbo da Hajiya Khadija.

Nafisa taci sunan kakarta ta wajen uba wato iya mata a gun mallam Aliyu Modibbo.

Mallam Aliyu Modibbo shine mahaifin baban nafisa yanada mata 4 cif da daya ta rasu ya sake auren daya.

Yana da Ya'ya 46 a cikin su 30 maza ne 16 mata. Matar sa ta farko ana kiranta da Rabi ko ince Inna tanada Yara 16 a tareda shi.

A ciki kuwa 11 ne maza biyar mata itace mahaifiyar Alhaji Nasir Wanda family din modibbo akafi sani da babban Yaya a cikin iyaye. Yara kuwa anfi sanin sa da Daddy shine da nafarko Mallam modibbo ya haifa.

Tareda matarsa ta biyu yanada yara 9 biyar maza hudu mata suna kiranta da Hajiya itace mahaifiyar Alhaji Umar Modibbo shine Dan fari a gunta

Sai matarsa ta uku tanada Yaya 11
Suna kiranta da Hajiya karama
Sai ta hudu tanada Yaya 10 suna kiranta da iya karama.

Kowaccen su raba musu gariyayi saboda tsabar kishin matar shi ta farko. Inna ita ya bari a garin Sokoto sai Hajiya babba ya kaita a garin Kaduna.

Hajiya karama aka bari a Kano sai iya karama da yake yar garin yolace sai ya barta a chan. Sai bayan Allah yayiwa Hajiya karama rasuwa ya sake auro Hajja Hadiza wadda ya aje a katsina.

A takaice dai Alhj Umar Modibbo shine da na 14 ga mallam Aliyu Modibbo
Koh bayan rasuwar mallam Aliyu Modibbo zumuntar su Bata watse ba Daddy shine ya zamto kamar uba a gare su.

Alhj Umar Modibbo yanada Yaya shidda hudu maza biyu Mata
Jalal Umar Modibbo shine na farko yanada shekara 29 da Mata daya da Ya'ya 2

Sai Maryam Umar Modibbo shekara 27(anti Mimi) itace ta biyu tayi aure Amma Bata haihu ba

Sai khaleel Umar Modibbo shekara 25 yayi aure bada dadewa ba

Sai tawaye Hydar da Sadiq Umar Modibbo sunada shekaru 20 sannan autah nafisa Umar Modibbo tanada shekara 16 tana a SS2 a MODIBBO INTERNATIONAL SCHOOL

Zamu tsaya a nan sai gobe in Allah ya kaimuna rai dafatar zakuji dadin shi

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now