CHAPTER 16: BRIDAL SHOWER

3.2K 235 8
                                    


Dakin cike yake da yanmata zaune suke suna surutu ana labari.

Nawal data shigo yanzun tace Dan Allah wadanda zasuyi wanka suyi wadanda zasu shirya su shirya har biyu da rabi tayi Dan Allah kada ayi African time

Neehal twin sister din nawal dake bayanta tace lallaikam dan amaryar ma tafara shiri please kuyi hanzari.

A dakin ammi kuwa nafisace ta fito daga toilet daure da bathrobe tacewa hadiza ki fada musu nakarasa ta zauna gefen gadon hadiza ta fita.

Batayi minti ukku da fita ba ta sake dawowa tareda Arya mai make up tana tareda yaranta su ukku rike da kaya suka gaisa tace amarya wannan kamshin tin Ina falo nake jinshi.

Nafisa tace haba anti banda zolaya Arya tace dagaske nake Dan Allah waya yimiki wannan hadin tiraren sabida insa a min idan lokacin nawa auran ya karaso.

Hadiza tace ai hadin family din mune Amma zanyiwa hajja magana tinda kinaso. Arya tace dakin taimaka tace gaskiya nafisa kinkara kyau fiyeda lokacin danaga hotonki mea sirrin.

Nafisa tayi murmushi tace ba wani sirri idankine dai. Arya tayi dariya tace toh amarya wadanmi kalar kaya zaki saka yau hadiza tace wlh in-law dinta zata kawo kuma haryanzu bata iso ba.

Arya tace jalilah kike nufi tace eh. Arya tace to mea ya tsaidata dan nasan bata latti kan abubuwa balema matar babban yayanta ai kobatayi sauri Dan Allah ba tayishi dan Dole amma bari a fara kamin akai inda zaa saka colour

Tafara yi mata make up din har sunfi rabi akayi Knocking jalilah ce ta shigo sai haki take kamar wadda tayi gasan tsere.

Jalilah tace anty na Ina wuni nafisa ta amsa mata da lafiya kalau jalilah tace Patricia kuzo ki ajiye kayan wasu mata biyu sukazo suka ajiye wasu manya manyan ledoji da tambarin A&A a jiki.

Jalilah tace Allah anti gobe saidai zaliha ta kawo miki kayanki hadiza tace mea yasa. Jalilah tace jar uban chan wlh mutuwace kawai bayiba ayau dinnan kedai bari.

Bayan jalilah ta fita zuwa gida aka karasa make-up din Arya tace ummi zoki gyara mata gashin. Daya daga cikin matan tazo ta kwance towel dinda ke kan nafisa tayi styling dinsa yayi kyau.

Bayan ta karasa Arya tace to yanzu kayan zaki saka suka tayata saka kayan OMG guys wata arniyar ball gown ce mai ja baya royal blue da patterns din silver masu design din roses rigar daidai ita.

Rigar mai dogon hannuce na material din hannun yayi fitting dinta kamar a jikinta aka dinka riga tayi sosai sukayi mata daurin turban da wani dankwali silver daga cikin kayan ta zauna kan gado Arya tace Masha Allah bantaba ganin wacce nayiwa make ...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Rigar mai dogon hannuce na material din hannun yayi fitting dinta kamar a jikinta aka dinka riga tayi sosai sukayi mata daurin turban da wani dankwali silver daga cikin kayan ta zauna kan gado Arya tace Masha Allah bantaba ganin wacce nayiwa make up tayi kyau kamar haka ba.

Make up din ba heavy make up bane Bai cika ba Amma yayi dadai suka saka mata 5 inches high hills silver mai shining sannan suka bata clutch fara mai glitters din silver.

Make up din ba heavy make up bane Bai cika ba Amma yayi dadai suka saka mata 5 inches high hills silver mai shining sannan suka bata clutch fara mai glitters din silver

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now