CHAPTER 43: COUPLES FIGHT

3.1K 230 19
                                    

Fita yayi daga gidan gaba daya ya shiga motarsa ya jata aguje ya bar gidan yana tafiya yana tinani chan kuma yayi parking ya hade kansa da sitiyarin motar ya lumshe idansa yana tinani.

Nafisa kuwa ganin ya fita a fusace yasata binsa dukda she was still shocked about his confession. Tana Kiran sa amma ko kurarsa bata gani ba asalima ko maikama dashi bata gani ba.

T koma cikin gidan tana tinani har ta dauka waya da niyyar kiran hadiza sai kuma ta fasa. Chan ta sake daukar wayar ta Kira anti Mimi suka gaisa, har tana tsokanarta wai autar ammi an girma ba'a kirana tafara defending kanta chan dai ta zayyane Mata abinda ke faruwa.

Anti mimin tace nafisa anya kinada hankali kuwa ya zaayi kibatawa mijinki rai ki gaza basa hakuri har ki barsa ya fita daga gidan ranshi a matukar bace.

Nafisa batasan lokacin data fara hawayeba anti Mimi tayita yimata fada tace kenan bakiji nasihar da akayi mikiba koh, kice nasihar su aunty Hafsat tashiga ta dama ta fita ta hagu.

Tun tana masifa hardai tadawo yi mata nasiha kamin tafara bata shawar wari tace idan kuma bazaki dauka shawarata ba ki zauna nan sake da baki har yatafi ya auro wacce zata kula dashi ta katse wayar.

Nafisa kuwa kara karfin kukanta tayi sai maganar anti Mimi ta dawo mata tace Ni kishiya Allah ya kiyaye wlh. Ta zabura tayi kitchen taga har four tayi ta cire dankwalin ta sannan ta fara shirya dinner.

Tuwon shinkafa tayi da white soup saida ta shirya komai kan dinning table lokacin har six tayi. Da sauri ta shiga dakinta tayi wanka ta shirya cikin wani hadden material almost golden mai designs fari a ciki dinkin doguwar riga ya fitoda coca cola shape dinta ya fito ko dankwali bata daura ba tayi packing gashinta

 Da sauri ta shiga dakinta tayi wanka ta shirya cikin wani hadden material almost golden mai designs fari a ciki dinkin doguwar riga ya fitoda coca cola shape dinta ya fito ko dankwali bata daura ba tayi packing gashinta

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

zari gyale fari ko takalma Bata tsaya dauka ba ta sauko falo taga haryanzu Bai dawo ba. Ta kirasa Bai daga ba har two missed calls.

Har akayi Isha tana tan jiransa duk ta damu sallarma a falo tayi ta sake trying numbersa tana ringing amma ba'a dagawa itace a parlor har Sha biyu tana trying numbersa tana hawaye amma still amsar dayace daga bayama sai ya kashe wayar.

Data kira taji switch off hankalinta duk inda yake ya tashi tana nan falo har bacci ya dauketa kan carpet din waiting parlor. Jay kuwa yana nan kansa a duke har bacci ya daukesa ya farka lokacin ana Kiran sallar Magrib ya Sami masallaci yayi sallar.

Saida akayi Isha sannan ya fita ya koma mota ya nufi guest house dinsa dake Apo dan a yadda yake jinsa idan ya koma gida haka komaima zai iya faruwa. Ya dauka daya daga cikin wayoyinsa ya shiga ciki da ita dan sauran na bayan motar ya kwanta saman kujerar three sitter yana kallan sama.

Yanata tinanin yaji wayarsa nata ringing batareda ya duba waye ke kiraba yasata a silent yacigaba da tinani har bacci ya kwashe shi. Bashi ya farka ba sai kusan daya na dare.

Ya dauka wayarsa da niyyar duba time yaga 1:05 ya zabura ya duba wayar yaga five missed calls din nafisa 2 missed calls from jalilah sannan 3 daga umma ya tashi ya dauka makullin motar ya kulle gidan.

Sannan ya shiga motar ya lalubo dayan wayarsa yaga Ashe ta mutu ya Sanya charge da car charger ya kunna ta kawo yaga ten missed calls dinta da wasu 2 missed calls din jalil.

Ya kama hanyar gidan ya sanya finger print dinsa ya bude kofar yaga gabadaya wutace gidan a kunne suke.

Yayi mamaki sosai Dan yasan idan zata kwanta komai saita kashe security lights kawai take bari, mamakinsa ya karu lokacin da idansa yakai kanta ta matse jikinta sosai alamar tana jinsanyi.

Dagani tana jiransane yadawo har bacci ya dauketa sai yaji wani haushin kansa da tausayinta yataso masa sai a lokacin ya tuna cewa nafisa fa yarinyace duk yadda akabi da ita hakan zata bi.

Ya karasa gurinta a hankali ya dauketa dankar ya tasheta daga baccin ya nufi stairs a dakinsa ya ajiyeta ya lulluba mata duvet din sai a lokacin ya kula da busassun hawayen dake kan fuskarta.

Saida ya koma ya kashe wutacen gidan sannan ya kunna na security alarms dinsu ya shiga wanka in thirty minutes ya fito dagashi sai boxers sai wani jikakken handkerchief ya kwanta dayan gefenta yana kallanta.

Saida yagama kare mata kallo sannan ya sa handki din ya goge mata fuskar being careful enough not to wake her up ya kashe side lamps din  sannan yajata jikinsa yayi musu adduar bacci ya rufe Ido shima.
Nace asuba tagari Jay.

Washegari Basu suka tashi ba sai karfe bakwai da ya mintota koshi abinda ya tayardashi sheshekar kukan nafisa ce ya buda idansa yana adduar tashi daga bacci yace lafiya babygirl kike kuka.

Ba abinda take fada inba am sorry ba bazan sake ba kayi hakuri harta bashi tausayi dagani da abun ta kwana a ranta. Ya daga fuskarta ya sakar mata murmushi yace don't worry komai ya wuce kinji yafada yana share mata hawayenta.

Yace to sakeni inyi sallah tunda kinsa na rasa jam'i sai a lokacin ta kula ta zagayesa da hannuwanta da sauri ta sakesa ta rufe fuskarta yayi yar bazawarar dariya a ransa yace yaro yaro ne Yana shiga toilet din ta fice zuwa dakinta.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
LIKE SHARE AND COMMENT ♥️ ♥️
.
.
.
.
.
.
.
DO VOTE PLEASE ⭐ ⭐ ⭐ WE

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now