CHAPTER SIX: MARRIAGE PROPOSAL

4K 240 0
                                    


Daddy ne zaune kan carpet din dakinsa yana danna laptop dinsa umma ta shigo.

File dinda Jay ya mika mata ta bawa daddy tace "gashi inji Mai sunan manya yace a baka kan maganar da kayi mishi kwanaki" hannunsa na dama ya Mika ya karba yace ok.

Laptop din yayi shutting down sannan ya buda file din wani picture ya fado dauka yayi ya duba ya mikawa umma kamin ya fara duba file din saida ya gama sannan ya saki murmushi.

"Lafiya Alhaji naga kana murmushi me yasa wannan yarinyar take cikin file din?" mika mata file din yayi yace "ki duba zaki gane karba tayi ta duba kamin tace Masha Allah Allah ya sanya alkhairi" ameen daddy yace.

✳️✳️ONE WEEK LATER✳️✳️

Daddy ne zaune cikin mota jalila dasu ajmal tsaye suna sallama airport ya wuce da isarsa cikin minti goma sha biyar jirginsu ya daga zuwa sokoto.

A airport din daddy ya hadeda wasu dattijai su biyar suka shiga motar da Kabir yazo da ita while some went with samir's car.

Abba ne sanyeda farar shadda yana kokarin sanya babbar rigarsa ammi na tayasa bayan rigar ta shiga ya sanya hularsa yace "nina tafi am sure na kusan latti"

Sallama sukayi ya fito bayan motar ya shiga driver yaja Abba "yace akwai bakinda zamu jira wajen junction din estate kamin mu karasa inda Yaya."

A gaban junction din suka hadu dasu daddy inda suka wuce Abuja road since gidan big daddy zaa tafi da isarsu driver ya Danna hon sojojin dake a bakin gate suka wangale katon gate din cikin katafaren gidan suka shiga sukayi parking.

Abba ya fara fitowa sukayi musabaha dasu daddy kasancewar dazun wucewa kawai sukayi basu gaisa ba sannan suka shiga ciki.

Cikin karamci da fara'a aka tarbesu kamin Abba yace "Umar Ina shi babban yaya?" uncle din nafisa ya mike yace "bari in duba sama baisan da isowarku bane"

Sama ya haye bai jima ba ya sauko yace "yayan yace Dan Allah kiyi hakuri yanzun zai sauko" baiyi minti ukku da gama maganar ba sukaji karar saukowa daga stairs.

Maida kansu chan sukayi daddy ne yace "aa wanake gani kamar Dan hajiya da sauri big daddy yace aa boy kaine yau a sokoto?"

Karasawa yayi cikin waiting parlor din suka gaisa kami a fara firar yaushe gamo. Sai chan daddy yace "gaskiya naji dadin lamarin nan. Ashe ma yar gidace za'ayi"

Murmushi big daddy yayi yace "Ibrahim dama so suke sukazo neman auren hajiya babba."

"Eh sune big daddy yace to wanne daga ciki diyan nawa akazo nemawa?"

Daddy yace "waye kuwa banda Umar" dariya big daddy yayi kamin ya bata rai yace "da yanzu ba yata kukaxo nema ba Alhaji Abdulkarim da yanzu bazan san da wannan bidar ba Ina abotar take ka sanya almakashi ya datse ka yar ko."

"Toh let all bygones be bygones after" the formal business aka tambaya big daddy "Munzo nemawa danmu Umar auran yarka Nafisa akan sadaki naira miliyan biyu ka bayar?"

"Na bashi."

With that the engagement was sealed and laughter was heard through out the house suna dinning table suna cin abinci daddy yace to "Kai my friend ka zartar da hukunci batareda kaji ta bakin yarinyar ba."

Murmushi big daddy yayi yace "I have confidence in nafisa yadda nasan bazan ja layi nace daya daga cikin diyana karsu tsallaka basu tsallaka ba nasan nafisa bazata tsallaka and nayi hakan because nasan duk Wanda zata kawo gidannan bazai kai Umar ba nasanshi tin yarintar shi.

Besides daga kan iyayensu harsu kansu yaran ba'a haifi wanda zance yayi abu yace bazaiyi ba and you know it better than anyone tarbiyar YAN GIDAN MODIBBO."

Har waje sukaiwa su daddy sallama sannan suka koma ciki big daddy yace "Ibrahim" Abba yace "naam"

Big daddy yace "are you angry nabada auran nafisa without your consent" "aa ko kadan kayi hakanne dan ka Isa."

Big daddy yace "you very well know I have the best interest of you and your children in mind Ibrahim will you believe me if I told you i was planning to match that boy with one of my kids kallansa abba yayi?"

Big daddy yace " idan harta auresa tayi dacen miji Idan harya aura nafisa to he's the luckiest man on Earth nasan salan ince bazan bada auren nafisa garesa ba in bashi yata but hajiya babba is my daughter as well she holds the same position as them in my heart I just hope that bazata watsa mun kasa a ido ba" ya mike yay tafiyarsa.

Abba ya kalla wani dattijo dake zaune kusadashi yace "do you still think bayasan nafisa shiyasa ya bada auranta batareda yayi bincike ba?

"What do you mean yaya?" Uncle Umar ya fada hadeda karasowa gurinsu.

Kallansa Abba yayi yace "Umar dazun faisal ke cemin yaya ya raina min da wayo wai ya bada yata batareda shawarata ba also baiyi bincike ba.

Kallan Faisal uncle Umar yayi yace "kagafa banasan iskanci da rainin hankali inbanda kaddara kaiba jinin Modibbo bane fa kai din agolan gidannan ne so watch out kar in karajin magana makamanciyar wannan ko wallahi na lahira saiya fika jin dadi"

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now