CHAPTER 27: Visit

3.4K 252 14
                                    

Bayan sun Karasa lunch dinne har nafisa zata kirasa deexa tace nafisa kinkirasa ne tace aa yanzun zan kirasa tace to kawai kice ya turo miki address din office dinsa zaki kawo masa lunch daganan zaki biya shoprite nafisan tace anya nifa dizgi ne bana so deexa tace kedai kira.

Ta kira a ringing na ukku ya daga in his husky voice yayi sallama ta amsa hadeda murmushi for no reason taji muryar tayi mata dadi ta gaida shi ya amsa da lafiya kalau

Tace am dama lunch ne na karasa shine nace is it alright if zakayi mun sending address din office dinka I'll drop it there for you kokuwa turowa zakayi a amsa a tafi dashi.

Jay's POV

Jay kuwa tunda ya Isa office yafara aikin dayayi missing lokacin dayake holiday amma yakasa keeping mind dinsa off her ya kira Abdul yace ka shirya nan da minti goma ka sameni a first floor zamu tafi gurin da ake training yaran chan I want to make sure sunayin aikin su.

Koda yasauka kasa Abdul na kasa mota kawai ya shiga yabawa driver din order inda zai kaisu tafiyar minti arbain ta kaisu wani katoton guri gate din tankameme ne ga ginar kamar ta prison idanma bata fita tsawo ba a gefe anyi rubutu Marshal Soldier's Training School.

Sojojine kota Ina na adadi suna training suna ganin motocin sa duk sukabar abinda suke suka bi layi suka tsaya Kam tamkar an dasasu saida ya fito sannan suka sara masa yace yanzu ku wannan abin da kuke shine kuke cewa training haka ake training din a gidanku.

Wato idan aka sanarda ku zanzo sannan kuke training kenan and you call your selves soilders. You know yourselves idan cikinku akwai wanda yasan yatafi operation yayi accepting bribe ya fito

Kokuma kasan katafi wani gurin ka karbi kuddin mutane step out duk suka kame yace General call out their names Abdul yayi stepping gaba ya Kira sunayen mutane ashirin.

Batareda yace su fito ba suda kansu suka fita gefe yace take them away I will decide what to do to them later(kutafi dasu zan yanke hukuncin daza ayi musu anjima) wasu sojoji suka kamasu suka tafi dasu soilders

Ya kalla sauran yace how many of you are here in Marshal Soldier's Training School sukace 5,000 yace good you are five thousand in number General call the Marshal Soldier's out.

Tell me mea first rule na Marshal Soldier's Training School da aka gaya muku da kukazo. Sukace no corruption yace to tell me you are only trainees not yet recruited as Marshal Soldier's yana magana sojoji dayawa suka fara filing a compound din.

Bayan kowa ya iso suka sara masa yace trainees you all wish you were them ko karyace sukace no sir yace I am the first person to reach the position of Field Marshal in Nigeria.

Wannan ya bani right dazan buda training school har nakeda sojojin da I can call mine. Mea kuka rasa as trainees ana Baku allowance ana baku abinci an baku gurin zama.

What is the need for bribery do you know that you are hurting my pride by accepting bribe you want to spoil the name of this school before you are even accepted ya karasa fada jijiyoyin jikinsa duk suka fito jikinsa na rawa.

A tsawace yace answer me gabadaya saida cikinsu ya duri ruwa ya juyaga Marshal Soldier's yace how many of you are their as Marshal Soldier's sukace 7,000 yace good you are seven thousand in number from whom I trained 4,000 personally. 1,000 of you were trained by General Abdulshakur 1,000 by General Hakeem the other 1,000 were trained by General kabeer.

Am I right sukace yes sir yace tell me cikin ku from your training har recruitment har kuka kawo yanxu akwai wanda aka kama da sunan bribe suka amsa da no sir yace then hala mea suka fiku.

As the founder of this school I hereby place a new order if a trainee is even being suspected of bribery and corruption the punishment is death idan kunsan bazaku iya Abu tsakani da Allah ba get out. This place is not for people like you.

You want to be called Marshal Soldier's then you have to train hard to earn that right to earn that respect and in order for you to be respected you have to respect your self. Today I am disappointed in you. And for you to gain my trust again you have to prove your self to me all trainees get back to training.

Ya buda baki zaiyi magana wayarsa tafara ringing ya fiddata ganin sunan dake rubuce yasashi saurin dagawa tareda sallama ya amsa gaisuwar ta jin abinda tace yasa ya juyawa sojojin baya yayi murmushi yace yanzun zan turo miki.

Yayi texting nata address din sannan ya kira wata number yace my wife, your Madam is coming out in a few minutes make sure she is protected. I want you to take some soilder's and go with her. She should not under any circumstances go out alone i don't want any mistakes ya katse wayar.

Ya juya yaga kallan da Abdul ke masa ya cewa sojojin dake tsaye you are my personal soilders train well I don't want any flaws and about your salary raise I'll see to it yashiga mota suka koma office.

Nafisa kuwa tana ajiye wayar taji karar text ta duba taga address dinne ta koma daki tace deexa jira zan chanja Kaya saimu tafi koma bani minti goma zan watsa ruwa kema ki watsa ruwa duk karnin kifi kike tunda am sure zaku shiga.

Bayan minti talatin deeza ta fito main parlor sanye da wando pencil trousers blue sai riga half gown blue da kimono blue a jikinta tana kokarin daura zare saita ajiye dayar kimonon dake hannunta fara mai designs in army green jin saukowar mutum yasani kallan sama

Masha Allah nafisa ce sanye da wando ripped jeans fari rigar sojoji wadda tayi stocking dinta long sleeve ce kanta tayi packing dinsa da ribbon fari tayi make up tasaka jambaki red kafafuwan ta sanye cikin wasu Tom's Suma army green tace inazuwa tashiga kitchen bayan rigar ansaka Field Marshal Umar Abdullahi Abdulkarim Abdallah in white writing.

Ta dawo da gorar ruwan Nestle guda biyu ta karbi kimono dinta ta saka sannan ta yafa army green din gyalen rigar su Fatima suka fitar musu da baskets din abincin. Tayi pressing wani remote wata farar Maserati tayi Kara suka nufeta akasa abincin a baya ta shiga drivers seat deexa ta shiga passengers seat. Start button ta danna motar ta kawo ta kunna AC din motar sannan tayi connecting da wayarta ta saka musu wakar wiggle.

Ta iso gate ta mirror taga motocin sojoji har ukku a bayanta tace wai wannan abun har yanxu tayi tsaki ta taka motar suna tafiya taga daya daga cikin motocin ta shiga gabanta suka kunna wutar jiniyar su.

In no time suka karasa office din buildings ne daban daban kowanne akalla zaiyi hawa biyar ga sojoji suna yawo suka karsa shiga duk inda suka wuce sarawa motar ake hadiza tace sun daukafa Jay ne nafisa tace wannan respect dinfa har ina.

Daidai building dinsu Jay tayi parking kamin ta buda kofar har wani soja ya buda ta fito suka fidda baskets din guda shidda sojijin suka dauka wasu sojojin sukayi tsaye suna gulmar wacece a cikin motar Ogah wadanda suka Santa sukace matarsace. Tasaka wani shades data dauko suka nufi ciki fifth floor sukayi pressing suka shiga elevator din ta kaisu deeza tace nanne stop dina office din Jay is on the sixth floor.

Deeza tayi office din Abdul nafisa kuwa aka kaita na jay saida suka wuce secretary dinsa ta tsaidasu tace Ina kuma zaku wacece ita hamisu. Dan naga batayi kamada kanwar Oga ba har mutumin zai bata amsa nafisa ta daga masa hannu tace wacece ke matar tace sunana sakina secretary din Mr Umar ce.

Nafisa tayi tsaki tace muje am tired of seeing this sunansa manne a kofar tayi knocking yace come in ta mirda handle din ta shiga yadaga kansa daga kallan laptop dinsa ya kalleta sama har kasa sannan ya tsaya Kan fuskarta yayi murmushi yace you look beautiful my love ta dukar da kanta kasa.

Ya Jima Yana kallanta kamin tayi serving dinsa abincin yaci sosai kamin ita kuwa tanasan Masa magana Amma tsoro takeji yace say it ta kallesa kamin yace dama maganan school ne inasan in karasa sannan kuma inaso zan tafi shoprite to buy something.

Yace maganan school bazaki karasa ba idan lokacin waec yayi you will write it about shopping kuma muje zan rakaki tadan zare Ido yace what bakyasan mutafi tare tace aa da tareda hadiza zamu yace then saimu tafi taredasu.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
LIKE SHARE AND COMMENT ♥️ ♥️
.
.
.
.
.
.
.
DO VOTE⭐

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now