CHAPTER 3: FAMILY TRIP

5.2K 257 2
                                    

Tun tafiyar su shida Abdulshakur basu dawo gida ba saida suka share shekara daya sannan suka dowo a lokacin har Jay ya Sami mukamin captain sabida kokarin shi.

Yanzu haka Jay din babban soja ne Mai mukamin field marshal (5 star general) shi kuma abokin nasa yanada position din General mai star hudu.

🌀🌀🌀🌀🌀cigaba🌀🌀🌀🌀🌀

Yaje ya zauna kusada ita yana gaida ita

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Yaje ya zauna kusada ita yana gaida ita. Tace "babana yau kuma mea mukayi maka kayi muna yaji tun safe sai yanzu."

Ya daga Kai ya kalleta ya buda baki zai yi magana sai kuma yayi shiru tace "Ina jinka mana"

yasake buda bakin zaiyi maga wayar dake can center table din falan tayi kara ya daga wayar ya mikawa umma ta amsa hadeda yin sallama.

Shi kuwa ya kwanta jikinta kansa a kan cinyarta ya mika kafafuwan sa kan kujerar ya lumshe idan sa.

Ita kuwa taci gaba da wayarta tadan jima tana wayar kafin ta ajiye tadan shafa sumarsa hadeda cewa "babana ko kayi bacci ne" bude idan nasa yayi yana kallanta.

Tace "ai na dauka bacci kayi mun a jiki." Yayi murmushi dai baice kala ba ya maida idan ya rufe dan bai cika san yawan magana ba

Tace "babana dazun muna magana maman ka ta kira." Ya sake buda idan yaja numfashi yace "umma maganar zuwa sokoto ce goben naje airport to sai suke cemun jet din wai pilot Kabeer baya gari."

Yana gama fadin hakan yasake lumshe idansa umma najira ya karasa taji shiru adan hasale tace "wai ba magana kake ba naji kayi shiru ko kuwa tun dazun fitarka cema kawai sukayi baya nan ka juyo ka dawo gida?"

Dasauri ya buda idansa Jin muryar umma ta chanja yace "umma bayanan kuma sauran a busy da wani zai kai mu.Shine nayi mana booking flight din gobe.

And goben da safe zamu airport in Allah ya yadda sabida Arik ne kuma first flight ne." Tace ok Allah ya kai mu.

Nan suka danyi fira amma rabin firar duk umma ce keyi. Daga baya ya mike yace "umma nizan tafi side dina tace to amma kada kayi bacci kasan laasar ta wuce yace to umma na yayi part dinsa."

A Sokoto kuwa nafisa na fara tafiya hadiza tace kada ki jima ta gyada mata kai hadeda yin part din hannun dama da sallama aka amsa.

Karasa shiga palon tayi sukayi clashing da wata matashiya sa'ar ta nafisa ta daga kai tace "waike Maryam bakya ganine ko jine bakyayi kina abu saikace wata sobuwa hala bakiji sallamana bane."

Yarinya tace "ni zaki cewa sobuwa."

Nafisa tace "eh an fada din kin mafi sokuwar sakaraci" tayi tsaki tajuya zata fita wata mata ta tsaidata.

"Nafeesa dan kinyi fada da maryam bazaki tsaya mu gaisa ba?"

tace "anti zan dawo ne" ta fice tana mitar an bata Mata mood tayi part din hage tundaga kofar shiga wani kamshi ya daki hancin ta tafara kwala Kiran anti Aysha kina ina?

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now