CHAPTER 2: MAID OF HONOUR

7.2K 311 6
                                    

Shekararta goma Sha shidda tana  SS 2 a MODIBBO INTERNATIONAL SCHOOL.

Abunda keda ban sha'awa a rayuwar family's din modibbo sunada son junan su kuma ga uwa uba hadin kai koh business Dan gidan Modibbo yakeda shi zakaga ansa Modibbo a karshe Koh a farko.

     🌀🌀🌀cigaban labari🌀🌀🌀

Yau takama ranar laraba da misalin karfe 10 na safe nafisa ta fito sanye da wata arebian gown purple tayi acuci da gashin ta tai rolling gyalen gown din.

Hannunta rike da hand bag dinta fara kafarta sanye da high heels farare ta sauka kasa tayi coming across ammi a falon kasa ta gaida ta.

Tace "ammi zantafi kinsan yau zaa fara kunshin hadiza kuma nizan biya in dauketa."

Tace "toh kishiga nan dakina akwai keys a cupboard ki dauki daya, sannan durowar Dake kusa da gadon kija ta farko kidauki 20k na kunshin da abubuwan da zakuyi a yau."

Tace "toh ammi nagode sosai Allah ya Kara budi."

Bayan ta dauko tadawo tayimata sallama tace "Allah ya tsare banda tukin ganganci kinji ba? Nidama Sadiq Koh Aliyu na nan da sunkaiki"

tafita Bata karasa jin maita fada ba. Ta Danna remote din motar wata bakar Benz S550 tayi Kara ta bude ta shiga tayi setting aux tasa wakar HABA.

Ta kunna A/C ga motar da tinted windows bakikirin ta fita maigadi ya bude Mata gate din. Takama hanyar Mana babba.

Batayi minti 20 ba ta karasa gaban wani duplex Mai kyau tayi horn Mai gadi ya bude gate ta shige parking tayi bayan ta fito ta gaida shi ta shiga cukin gidan tana Mai sallama.

Daga ciki gidan akwai mutane da Dan yawa ta gaida su ta hau sama sai dakin danake sa ran na hadiza ne ta shiga tana fadin "ke yar rainin sense kitaso mutafi ana jiran mu"

yarinya sa'ar ta ta tashi zaune daga kan bed ashe Hadiza ce. Tana fadin feena sunana hadiza ba Yar rainin sense ba ehe taja mini hijab dake kan gadon tace mutafi sukayi musu sallama suka fita.

Suna cikin motar wayar hadiza tayi Kara ta daga tana murmushi chan kuma ta chanza fuska tace "toh kasani idan har bakazo kamun nan ba toh ba auren da zaa daura ranar jumuaa sai ka aureshi tunda yafi maka Ni"

Tsaki tayi kamin ta kashe wayar. Nafisa tace "ke kuwa lafiya" deeza tace "ke wai Abdulshakur ne wai bazai samu zuwa kamun ba saboda best friend dinshi yaune zai iso bazai Sami damar zuwa kamun ba shine Shima bazashiba."

Feena tace toh shine na fada. Toh Allah ya shirya. tayi parking a gaban wani babban shago a gaba a rubuta MODIBBO BEAUTY SALOON AND SPA suka shiga gurin like yake da ma'aikata kala kala.

Suka tararda Yan matan amarya su neehal ne su nawal ne sa safina ne Kai har su Amina intakaice muku masu karatu yanmata sunyi 30 nan aka fara yiwa amarya gyaran Kai bayan ta gama akayi Mata manicure and pedicure.

Sauran yanmatan ma dayawa sunyi kafin afara zana musu lalle. Basu suka bar gurin ba sai around 3 suka fito kowa ya nufi gida Dan su shiryawa bridal shower karfe 4.

Feena ta Kama hanyar gida tareda deeza da Amina da Khadija tayi parking a inda ake parking kowaccen su tayi part dinsu.

Deeza ce  kawai tabi nafisah suna shiga sukayi wanka feena taja MK kit dinta tafara yiwa deeza kwalliyar bridal shower.

Bayan ta gama ta fidda wada doguwar riga a sif Mai shining tace saka tasa it's kuma tafara casual makeup ta dauki wata royal blue gown.

Mai kwalliyar silver a ciki da hannu tayi turban da wani silver silk dankwali tasa 6 inches high heels silver tayi mugun kyau.

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now