CHAPTER 36: Twinning

2.9K 211 8
                                    

Tana fita tanufi orange venza dinda ke gidan ta danna remote motar tayi unlocking harta buda zata shiga taga peter sai lokacin ta tina Ashe tare takeda sojoji.

Peter yace madam we shall come with you tace ok suka shiga motocinsu itama ta shiga tata sai a lokacin ta tina cewa bata kira jay ba ta dauka wayarta tabar motar tana slow saida tayi masa 3 missed calls sannan tasa gear tafita daga gidan suka Kama hanyar lapai road cikin minti goma suka karasa gidan.

      Horn sukayi maigadi ya buda gate suka shige sukayi parking tana tafiya suna binta har suka karasa inda mutane suke saida suka Isa sannan ta kula duka yan matane tace aa kuce nazo Kan saa lalle ake miki kenan??

Mubeena tace eh matar soja ta waiga tacewa Peter su koma mota idan zata fita zatayi notifying dinsu ta zauna sunata tsokanar junansu ta kalla meema mai lallen tace daga kin gamawa amarya saini.

Sannan wanda yafi nata kyau zakiyimin tace angama ranki ya dade. Sai around six thirty suka wanke lallen dan ita nafisan ma saida tayi kitso bayan anyi lallen suna gama wankewa ta kiro Peter tace yaje gida ya anso mata kaya gurin ammi.

Ta shiga nanne ta haduda anti Mimi ta tuma ta rungumeta saura kiris su sha kaye a kasa.

Tace antina naje gidanki bakyanan mimin tace karya kike baki tafiba Dan ban shigo nan gidan ba sai biyar da rabi kuma naganki tayi murmushi tace ayya antina wlh gobe nakeda niyyar inje miki yini hadda kwana.

Ammafa idan Yaya zai bari Mimi tace wanne yaya. Yayan da bayanan saidai idan ammin taki zata yadda. Ai ammi batada problem inji nafisa. Sukayi alwala sukayi sallah suna azkar akayi knocking kofar.

Ta tafi ganin waye sai ganin Peter tayi tsaye da jakka a hannu ta karba hadeda yi masa godiya sannan ta koma ciki.

Daga ita sai anti Mimi ne a dakin bayan anti Mimi ta gama shiri ne ta karba ashoken anti Mimi tace anti juyo in miki dauri ta kashe mata dauri  Mai step step. Saida ta gama sannan tace Bari inga kayan da ammi ta aikomin.

Tana ganin kayan tace haaa anti irin naki ke kikayi mana tayi dariya ganin fuskar nafisan tace ninayi mana wani shago na shiga naga ashoken yayi mun kyau shine na siya na hado da wannan material din.

Ta saka nata itama mimin ta daura Mata ashoken sannan suka fesa tirare suka fito tare idan kagansu zaka zata twins ne sabida sunyi balain kama da juna mutanen gidan sukayita praising dinsu Kan cewa sunyi kyau.

Suka Kama hanyar zuwa wankin amarya suna shiga jay ya kirata. Saida gabanta ya fadi ta daga tayi sallama hadeda gaidashi ya amsa yace kina inane naji hayaniya tafara yan kamekame.

Yace ko bakiji me nace ba tace am naji ai na kiraka dazun baka daga ba dama tambayar ka nasoyi zan fitane Amma baka dagaba shine kawai muka wuce gurin wankin amaryar yay shiru yace daban dagaba bazaki iyayi mun text message bane jin ransa ya baci tace kayi hakuri hakan bazata sake faruwaba kaji yayi ajiyar zuciya yace only this time kada ki sake sukayi sallama yace kada tayi dare ya ajiye wayar.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
LIKE SHARE AND COMMENT ♥️ ♥️
.
.
.
.
.
.
.
DO VOTE PLEASE ⭐ ⭐⭐

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now