CHAPTER 29: NEIGHBOR

3.2K 222 18
                                    

Bayan tagama dressing kafar ne tace Jay zan rubuta mata magunguna nasha dana shafawa insha Allah nan da sati daya zata samu lafiya ammafa zaka rika chanja bandage dinta Allah ya bata lafiya.

Bayan tafiyar Doctor shareefa ya duba time yaga har karfe biyu ta kusa ya dauki nafisar ya fito daga dakin ya nufi hanyar fita. Sanyata yayi cikin mota seat din baya ya shiga tareda ita yasa daya daga cikin sojojin driving nasu.

Bayan sun Karasa gida ya dauketa ya sanya fingerprint dinsa kan scanner din, sannan yayi scanning idansa sannan kofar ta bude ya shiga. Ya maida kofar ya kulle part dinsa ya nufa da ita a dakinsa ya ajiyeta saman gadonsa bayan ya chire mata hijab da jallabiyar daya saka mata yaja mata duvet cover ya rufa mata.

Bathroom dinsa ya shiga ya watsa ruwa ya sanya wani farin boxers da wata singlet fara ya fito ya kashe wutar toilet din kamin ya dauka wata iPod dake kan bed side table ya daddan na wasu abubuwa take naji karar rufewar kofofi da windows har kofar toilet dake bude taja dakanta ta kulle.

Wutar dakin ma da kanta ta dauke sai wata wuta blue data fito dan space dinda ke tsakanin windows da kofofin  ya ajiye iPad din ya cire talakmansa ya kwanta ya juya yana facing dinta yana kallan fuskarta.

Ya shafa fuskarta yace if only you know how much I love you. I fell in love with you at first sight I didn't believe in love then but I came to know what it means. Babygirl since the first day I saw you I knew you were mine.

Now all that's left is for me to teach you how to love me I hope you will love me yayi pecking dinta a forehead ya rungumeta a faffadan kirjinsa within his broad-shoulders yana shakar kamshinta har bacci yayi awon gaba dashi.

Da misalin karfe shidda da rabi nasafe ya kira umma tadaga suka gaisa umma tace lafiya wannan kira tunda sassafe babana yace umma nafisa ce ba lafiya jiya ma saida cikin dare muka dawo daga asibiti shine nace zamu sami breakfast daga nan gida.

Umma tace subhanallah ya akayi haka kada ka damu yanxun nan zansa Jamil yakawo muku kamin muzo dubata Allah ya bata lafiya yace ameen kamin su ajiye waya.

Ya tashi ya nade sallayar ya ajiye ya dauka laptop dinsa yafara wa aiki jin karar wayarsa yasakashi ajiye laptop dinsa ya daga wayar baiyi second goma yana wayar ba ya kashe ya dauka wannan iPod din tajiya ya sake danna wasu abubuwa kofar waje ta bude.

Yakoma parlor ya zauna bai jima da zamaba Jamil yayi knocking ya bashi izinin ya shigo. Shiga yayi ya gaidashi ya bashi basket na breakfast sannan yayi mishi sallama ya ya koma cikin dakin still tana baccinta.

Aikinsa ya cigaba dayi chan yaji motsin mutum nafisa ce ta tashi daga baccin datake ya taso ya karasa bakin gadon tana ganinsa ta fashe da kuka ta fara yarfa hannuwanta tana kiran Abba ya tamke fuska yace ke natsu mana mea namiki kina cikin hankalinki kuwa.

Ta sake fashewa da kuka da kyar da boni ya samu taci abincin ya fidda magungunanta ya balla na sha ya mika mata nan aka fara sabon jidali saida ya zare mata ido sannan tasha maganin.

Ya kaita dakinta ya bata minti talatin tayi wanka ta shirya sannan tayi sallah sallar ma daga zaune tayita sannan ya shigo dakin da first aid kit ya zauna kan gadon ya Kama kafar ya cire bandage din jiya.

Ya jika cotton wool cikin spirit ya kalla kafar da inda akayi mata stitches ya goga tasaki kara da hawaye da murje murje da fada da komai aka gama dressing din dan saida ya danneta sannan ya gama.

Yau Jay ya tafi gurin aiki bayan an kirashi gameda wani important meeting. Saida yajawa su Fatima kunnen kan cewa su kula da nafisa kamin ya dawo fitarshi da minti ashirin ta dingisa ta sauka kasa dan rabonta da downstairs tun kwana hudu da suka wuce.

Ta zauna main parlor ta kunna tv tana kallan zee world taji knocking kamin ta tashi zainab ta tafi ta bude wata mata ce ta shigo chocolate colour kyakyawa zatayi akalla shekara 20 sanye da riga da skirt na less brown tareda wani yaro fari tas iyakarshi shekara ukku.

Suka gaisa tace zauna mana ta zauna tace nasan baki sanni ba amma sunana Aisha mune immidiate neighbors dinku koda kuka dawo nan gidan munyi tafiya zuwa oman ne sai shekaran jiya da muka dawo dayan neighbor dita maman zainab tace an kawo amarya shine nace Bari in zo mu gaisa koba komai musan juna.

Ayya nakuwa gode ya sunan mutumin nawa tace Hafiz ne sunan shi nafisa ta tara hannunta yaki zuwa tace badai kiyyuya kake ba Aisha tace wlh haka yake ba Wanda yake yadda da idan bani ko abban sa ba

Nafisa tace kin kyauta Aisha gwara ke duk layin nan ba wacce ta shigo da sunan wai tasan sunyi sabbin makwabta Aisha tace aa ba haka bane nafisa duk da dai Shirin bayada karfi tsakanin mu sosai sabida zaa ce Abuja barikice.

Balema nan shiyar dayake ta masu kudin garinnan ce itada maitama ba ruwan kowa da kowa gaskiya maman samir tazo maman zainab mata shiga hakama maman grace ta shigo amma sojojin gidannan ke hanasu shigowa.

Dan koni sabida sunsan sojan dake mana gadi ne shiyasa. Nafisa tace aini sunma isheni idan masu gadi yakeso yabar daya kobiyu mana amma yatashi ya cika gida da sojoji saikace bariki Aisha tace dolene a baki tsaro sabida ke matar field marshal ce koni da abban Hafiz captain ne ya bar soja hudu a gida bale ke matar Oga.

Nan sukaita fira sai data jima a gidan kamin tayiwa nafisa sallama nafisa tace to Aisha tunda kin dage kan bazakici abinci ba ai kya tsaya ki tafida dessert dinnan ko tace aa wanda naci ya isa tasake yi mata sallama sannan ta tafi.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
LIKE SHARE AND COMMENT ♥️ ♥️
.
.
.
.
.
.
.
.
DO VOTE ⭐ ⭐⭐ ⭐

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now