CHAPTER 11: SECOND MOM

3.3K 222 3
                                    

3rd person POV

Ummace tareda anti Salma zaune a cikin private jet din daddy suna karasa  list  din kayan da zaa siya na lefe umma tace salma mea kike tinanin matar dannaki zata so kinsan kuruciya dan yarinyace naji daddyn nasu yace she is sixteen so ke saikin fini sanin mea yarinya warinta zata so.

Anti Salma tayi dariya tace anti komai da ake sakawa manyan Mata macce wacce ta amsa sunan ta macce sannan macce mai aji mai ji dakanta zaa sakawa matar boy dina haba anti abin farko a Abdullahi Abdulkarim family.

Kema kinsan dolene ayimata gata kowa yasan zaayi auran dan gata kawai dai ke da kika fini sanin kan atamfa da materials manya su nabar miki sauran kuwa ni zanyi.

Umma dai tun lokacin data fara magana kallanta take har ta dasa aya data kamalla tace to kina ganin kala nawa yakamata asaka dannan saiti nawa zaayi.

Anty tace toh yawuce ayi komai set din akwatinsa daban kingane ko ki barshi har muje siyayyar yanzu kawai mu karasa list din nan suka dinga tattaunawa har jirgin ya sauka a kasar Dubai suka nufi masauki

Da saukarsu gidan su dake nan Dubai din suka huta suka sake wanka da tufafi sannan anti Salma tace anti since kwanakin da suka rage mana basuyi 12 ba har kai lefen sannan kwana shidda zamuyi a nan to tinda yanzu 2 tayi mufara siyayyar kayan ko mai kika gani.

Toh Salma dagaskiyarki dauko mun mayafina Sai mu tafi. A cikin kwana shiddan suka karasa siyayyar kayan lefen da zasu siya a nan Dubai suka tura su zuwa Nigeria Amma ta jirgin sama.

Suka sake kwasa sukayi india nanma siyayya sukayi harta fitar hankali sannan suka biya Shanghai suka dawo Nigeria jirgin ya sauka a filin jirgin Abuja da karfe 5:30 na rana anti Salma tace anti tunda su anti hafsa da anti Amina da sauran na gidan muje a karasa hada kayan since gobene zaa kaisu komai kika gani.

Anya Salma baban iman bazaiga abin yayi yawa ba gwara ki tafi gida anti Salma tace haba anti wlh ke kike maida abin babban abu abban iman bazaice komai ba idan ma kwana nace zanyi zai gane dan yasan waye Mai sunan baba a guna

Anti kosan kike a nunamin ba dana bane Dan Allah bai bani da namiji ba wlh anti kinsan dai nina haifi iman da kaina amma bana mata san danake yiwa umar wlh nafi sansa akanta tana magana tana hawaye umma tace waye zai nuna miki bake kika haifi Mai sunan baba ba uhm Salma.

Kiyi hakuri kizo mutafi suka Kama hanyar fitowa arrival koda suka fito sojoji ne cike da wurin anti Salma tana tsinkayo Jay  tasake hannun umma data jata tayi gunsa shikuwa da gudunsa ya karaso ya rungumeta suna dariya sunma manta da umma daga baya ya sake ta ya durkusa ya gaidata.

Tace banace kadaina dukawa idan zaka gaidani ba kanasakani jina kamar tsohuwa yayi dariya sannan ya lura da umma. Umma kam ta zuba musu ido tana mamakin irin San da Salma keyiwa Jay.

FLASH BACK

Dan tun kafin a yayesa kullum tana gida da aka kaisa yaye gidan mamman su ranar ta tafi har gida ta saukewa umma nata kwandon masifa sannan ta tafi gidansu ta karbesa.

Bayan ta amshesa ne da zata fita saida ta saukewa yayarta wadda take biwa kwandon rashin mutunci sannan tayi gidan ta da lokacin dayake da shekara 5 yayi dambe dawani student din makaranta malamar ta likida masa dan banzan duka wai yaci zalin din dayan yaron.

Lokacin daukosa school yayi that time anti Salman na gidansu taje kai masa ziyara tace bari ta daukosa school din tana  parking a lot din makarantar gabanta yafara faduwa. Ta shiga makarantar zuwa class daga window din ta tsinkayo tambon bulala a jikinsa.

A guje ta karasa gaban sa tana tambayarsa mea yafaru ya nanata mata take ta yadda dan tasan baya karya ta juya ta karantawa wannan malamar shikashikan rashin mutunci sannan kuma tasaka bulala ta rama masa.

END OF FLASH BACK

umma ta nisa tana mamakin su suka shiga mota zuwa gida. Koda suka karasa gidan su anti hafsat Amina hajara da Madina suna gidan anti Salma kuwa kasa cin abincin da aka aza musu tayi saida taga an shirya komai tas cikin akwatunan sannan fa suka  zauna lafiya nan suka fara tsokanar ta.

Anti Madina tace su Salma zaa aurarda da masu Diya manya tace naji ku fada Allah ne ya nunamin ehe. Anti hajara tace yauwa dama inada tambaya zaa aza musu tukwici ko kuwa naga kamar kayan suyi basai ansaka kudin dinki ba.

Haba anti gudan Dan nawa guda zakice  bazaa aza dinki ba to gaskiya ki daina fada gaskiya bana so anti Amina tace wannan Dan naki sabida shi zaki iya batawa da kowa mai yayi zafi haka daga anyi maganar kudin dinki zaki tasowa mutane kamar wata uwarsu to idan ma zaa bayar ke zaki bada kudin ne.

Eh naji kuma wlh akansa zan iya batawa da kowa ita harma tacewa ne da ita kuma kudi dinki sai an bada babu fashi kuma ni nan zan bada wlh dana bazaiyi kunya ba kuma ina sake jadda muku kada wadda tayadda 10 batayi mata a airport ba Dan wlh tafiya zanyi in bar mutum koni kadai na isa in Kai Masa lefe ta figi Jakarta tayi waje umma na kiranta Amma tayi kamar bataji ba.

Anti Amina tace lallai abin Salma yayi nisa harni zata dage ta cuwa mutunci. Anti hafsa tace konifa idan bazaku mantaba sabida Mai sunan baba Babu irin cin mutuncin da batayi munba harda fa dukana ta tashiyi.

Umma dai  batace dasu komai ba saima kallan side din Jay datayi ta hangosa balcony dinsa na sama yana murmushi girgiza kanta kawai tayi tace Allah ya shirya.

Anti Salma kuwa tana fita taga driver dinta har yakaraso ta shiga suka wuce zuwa gida Koda 10 tayi umma tayi Mata missed call yafi a kirga Amma taki ta dauki wayar.





By Neera Naseer

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now