CHAPTER 15: SISTER IN-LAW

3.2K 231 10
                                    

Yau ya kama  saura kwana biyar biki nafisace kwance kan gadanta tana kallan sama da alama tinani take hadiza ta shigo dakin tace feena kitashi inji ammi.

Tace wanne makircin kikaje kika kulla. Dariya hadiza tayi tace huta madam ba abinda nayi cewa tayi kizo kishiga wanka sannan ga hajja nan mai tirare tazo.

Nafisan ta bata fuska keni nagaji dallah baa gama wankan nan na  wannan madarar shanun nan bane.

sannan tiraren bai isa haka ba nafi sati suna sani wanka da wannan perfumes din nasu har bana san shakan iska cause abun na hawa kaina

Hadiza tace ai kuma sai kiyi koni nan da bamuyi wata uku da aure ba saida nayi wankan madarar sannan idan mita zakiyi bani zaki yimawa ba ammi Zaki fadawa ehe.

Bansan ya akayi wannan tsohuwar ta maida wannan abun aladar gidannan ba ta karfi da yaji mtsww ayita takura mutum.

Hadiza tace to ni ba wannan ba kinsan akwai sauran kawayenmu dazamu kaiwa IV'S dinnan kuma dasafe bamu tafi ba so kiyi ki karasa wankan ayimiki tirare sai mu karasa rabon.

Nafisa tace ok gani zuwa ta shiga toilet ta dauro towel sannan ta fito sukanufi dakin ammi.

Ammi na zaune a daki tareda hajja suna dan taba fira su nafisa suka shigo ta gaida su.

Hajja tace mai sunan hajiya kinsan dai yadda aka saba yauma haka zakiyi saidai tiraren yau karfin yanada yawa ga madarar shanun chan bandaki ki shiga idan kikayi wankan madarar kika fito zan shiga in hada miki ruwan tiraren.

Bata musa ba ta shiga toilet din ammi tana bidar madarar sai taga wasu manyan abubuwa golden kamar kumbu amma ba kumbun bane ta buda taga madarar fara tas da wasu jajjayen abubuwa.

Batayi minti goma ba ta fito tacewa hajja ta gama hajja ta shiga toilet tafi minti talatin a ciki sannan ta fito tace ta shiga.

Nafisa tasake komawa toilet din kamin ta karasa wani kamshi ne nadaban mai dadi ya bigi hancin ta ta shiga toilet din ta kwanta cikin bathtub din tana wasa da ruwan tiraren.

Ta jima a ciki saida kamshin yafara hawa kanta sannan ta fito daga bayin tayi dakinta.

Da shigar ta  hadiza tagani tace shine kika gudo kika barni.

Hadiza bata amsa taba ta dauki wata baby pink din doguwar riga yasaka ta yafa gyalenta ta dauka Jakarta da takalma tace muje.

Hadiza tace yauwa ki dauko gabadaya gate passes din events din dake daban sabida yau masu anko anko din zaa kaiwa sannan mostly kawayenmu ne.

Bayan sun fito jabir ya buda mota suka shiga nafisa tace mubita gidan big daddy as usual zamu dau huhu.

Bayan sun dauka huhu( wato autar big daddy) suka Kama hanyar bafarawa estate.

Basu suka dawo ba sai kusan Sha daya na dare nafisa tace hadiza ai daga yau mu gama koh

Hadizan tace aa sai mun raba daga gobe shikenan sabida akwai sauran mutanen da zaa bawa.

Washegari ma suka fita rabon IV bayan sunyi sallar Magrib a gidan big daddy suka fito tace pls jabir zaka kaimu havila musha ice cream yace yes ma suka kama hanyar havila minti goma sha biyar suka Isa gurin.

Akwai mutane ba laifi saidai mafi yawancin su duk mazane.

Suna shiga sukayi gurin ice cream din matar ta tambaya scoops nawa nafis tace biyar biyar suka zaba wadanda zasu Sha suka karba suka nufi wani table dake empty suka zauna suna sha.

Ta juya taga jabir bayansu sannan wasu daga cikin sojojin sun shigo ciki ta cewa jabir suje su karbi ice cream yace no madam we are on duty tace I insist ta buda Jakarta ta fidda kudi ta bashi tace idan basu isa ba kadawo ka karba my treat yayi godiya.

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now