CHAPTER 64: OUT SHOPPING

2.2K 171 10
                                    

Da kanta ta kaishi airport saida private jet dinsa ya tashi sannan ta juya kan motar ta koma gida. Zaunawa tayi tana kallan wani film a dakin ta saida twelve tayi sannan ta daura dankwalin atamphar ta

 Zaunawa tayi tana kallan wani film a dakin ta saida twelve tayi sannan ta daura dankwalin atamphar ta

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Farin medium gyalenta ta dauka hadeda farar handbag dinta da takalmanta na company din Bonia.

Saukowa kasa tayi taga ammi zaune tareda Yaya Hydar da yaya Sadiq suna firar yadda bikin ya khaleel da ya Imran.

Gaidasu tayi sannan tace am ammi zan fita zan tafi inda anti zamu shiga kasuwa kayan da ake bukata zamu karasa siyowa.

To Allah ya tsare ammafa karkiyi dare amsawa tayi da to hadeda yi musu sallama. Saida ta shiga mota sannan ta sake kiran jay tafada mishi zata fita.

Go ahead ya bata sannan ta kashe wayar taja motar zuwa gidan anti Mimin. Shiga tayi ko kallan anti mimi dake tsaye rikeda gyalenta batayi ba.

Kitchen ta shiga tafara binciken fridge din saida hannunta yakai kan strawberry flavored hollandia ta buda tasha sannan hankalinta ya kwanta.

Juyowa tayi suka hada ido da anti mimi dake tsaye baki sake galala tana kallanta. Murmushi tayi sannan tace anti anti Ina wuni.

Tabe baki tayi kamin ta amsa da lafiya idan kin gama binciken naki mutafi ko. Fita tayi antyn ta kulle kofar sannan suka shiga mota wannan karon driver ke tukasu.

Kayanmu dana ammi suna gurin hudayya yau zamuje mu karba bayan magrib. Anti hadda nawa kun bada?

Eh hadda naki na bada saidai bana tinanin zasuyi fitting dinki because kin kara jiki. Allah anti ko numfashi ne bana iyayi idan nasanyasu saina sa.

Dariya anti mimi tayi tace to hajiya am sure idan mukaje fitting around two idan batayi Miki ba zata gyara.

Anti me zai kaimu kasuwa ne? Takalmi zan siya a shagon naziru yakawo wasu takalma da sukayi mun sannan Ina tinanin siyan sabuwar sarka gurin ummaru Mai zinari.

Minti goma suka kaisu q kasuwar gurin Mai takalmin suka fara zuwa inda anti Mimi ta dauka wasu heels blue colour da wasu flats biyu daya milk daya red.

15k ya amsa a kan ko wanne a cewarsa yayi musu sauki wai dan suna customers dinsa.

Fita shagon sukayi suka nufi gurin ummaru Mai zinari. Koda suka Isa akwai mutane gurin.

Amma kasancewar su regular yasa aka kawo musu kujeru yabawa wasu Mata daya gwadawa sarkoki hakuri ya sanya kanensa dake gurin attending to them sannan ya nufi gurin su nafisa.

Gaisawa sukayi sannan anti mimi ta nuna mishi wadanda taga sun bata sha'awa. Tunda Suka shigo idan nafisa suka sauka kan wata sarka set hadda mundaye da agogonta.

Nuna mishi ita tayi tace dan Allah muga waccan sarkar. Kallan inda ta nuna yayi, jiki na rawa ya dauko box dinda sarkar take ciki.

A gabanta ya ajiye dubawa tafarayi kamin tace anti duba wannan English gold din set ne. Dubawa anti mimi tayi kamin tace kin rigani dama inada niyyar cewa ya kawo in gani.

Gaskiya tanada kyau siya zakiyi? Daga kanta tayi tace eh ya min kyau. Wayarta captain Jabir ya bata dubawa tayi taga Jay ne ke Kira.

Saurin dagawa tayi tayi sallama kamin ta gaidashi. Kallan Mai zinarin tayi tace ka auna inga. Ya auna me? Jay ya tambaya lokacinda yake fitowa daga cikin gida.

Am kamanta Ina kasuwa zamuyi siyayya. I wanted to tell you am going to be a little bit busy this days so idan kin Kira ban dagaba feel free to leave me a text or voicemail. And please karki daga hankalinki.

Amsa mishi tayi da ok Allah ya taimaka but yaushe zakazo if you will be busy? Amsawa yayi da I will be done by Thursday.

So Ina sa ran zanshigo sokoto Thursday afternoon I Sha Allah. Ok Allah ya tsare tace ya amsa da amin sannan suka kashe wayar.

Kallan Mai zinarin tayi yana aunawa bayan an auna taga grams din sukayi converting to carat sannan ya fada kudin.

Anya ba cutarmu zakayi ba kuwa? Nafisa ta fada lokacinda yace gabadaya set 11.2M. Allah ba haka bane  kinsan gram ya hau yanzu gram daya a kan 50k yake.

Sannan wannan design din unique ne jiya kayan suka iso. Account details dinsa ta amsa kamin ta Kira wata number da aka sawa immediate cousin.

Dagawa akayi tace hello cousin, Bayan sun gaisa tace na turoma wasu account details kudi nakeso kasa a ciki 11.2 yanzu please.

Allah nafisa am busy yafada yana Jan numfashi. Rolling eyes dinta tayi tace please kasan da zan iya transfer danayi.

Amsawa yayi da toh tace also anti Mimi ma zakayi Mata transfer to the same account. Sallama sukayi sannan ta kashe wayar.

Bayan an auna na anti mimi sarka da Yan kunne masu zobe guda biyu ta dauka. Itama depositing din 9M din  cousin dinsu dake manager na na UBA yayi.

Packaging akayi musu suka kama hanyar fita a shagon hudayya suka yada zango. Kayan sukayi trying. Na nafisa ne duka sai an buda Mata while anti Mimi dayace ba'a karasa ba.

Daga shagon hudayya suka tafi wata plaza ta anti sumayya(matar baba Jamilu) SUMMY'S FASHION EMPIRE

Gefen gyaluluwa suka nufa inda suka dauka kala tara each har ammi ko wanne new design. Ciki babu na kasaga 36k daga nan suka shiga gidan wata cousin dinsu surayya CEO of SURRY'S BEAUTY WORLD.

Maganar gyaran jiki sukayi da makeup hadeda lalle. Gaskiya anti ba karya bazaku samu gyaran jikin ba sabida amarenma ni zanyi musu gyaran jiki.

Maganar kwalliyar da lalle kawai sukayi sannan suka nufi gidan wata kawar anti mimi wacce ta shahara gurin daurin dankwali.

Anti Bari kawai in daura mana dankwalin nafisa tace lokacinda suka Isa gidan. Am not doubting you nafisa but it will be less stressful on us.

Idan a gidanku ake biki komawa zakiyi kamar mahaukaciya. Shiga sukayi sukayi maganar daurin dankwalin sannan suka Bata deposit suka fito.

Kiran chiroma Mai atampha ya shigo a wayar anti mimi. Dagawa tayi tana sallama amsawa chiroma yayi yace hajiya atampopinki sun iso yanzu.

Okay ganinan zuwa anti Mimi tafada tana ending call din. Driver din tacewa mutafi tsohuwar kasuwa daga baya ma tafi AGG din.

Kiran ammi tayi tace a tura Hilux daya kasuwa da shigarsu shagon ton ton din atampopi Suka gani baje kuma wadanda anti Mimi tabashi sample dinsu ne.

Sojojin suka fara jidarsu suna kaiwa cikin Hilux din gida da aka turo kamin su iso. Saida suka daukesu duka sannan su nafisa sukayi mishi godiya hadeda bashi 50k na wahalar dayayi.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
LIKE SHARE AND COMMENT ♥️♥️
.
.
.
.
.
.
MANAGE THIS FOR TODAY PLEASE
.
.
.
.
.
DO VOTE PLEASE ⭐ ⭐⭐

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now