CHAPTER 13: LEFE

3.2K 228 5
                                    

Washegari da misalin karfe Tara da rabi na safe anti Salma takama hanyar gidan su Jay.

Umma na zaune kan dinning table tana breakfast tajiyo sallamar ta daga main parlor ta amsa hadeda cewa kizo gani a dinning.

Ta karaso dinning din suka gaisa kamar ba abinda ya faru bayan sun koma parlor ne anti Salma tace yauwa anti kafin namanta wai mu nawa zamu Kai lefennan ne.

Umma tace gabadaya total ku talatin ne anti Salma tace dawa dawa kenan umma tace daga chan gefen daddyn nasu zaa tafi da mutum 15 kuma namu gefen 15 ne.

Anti Salma tace to dama inada magana dama my son jiya ta kirani yace bashida bukatar anti hafsat taje kai lefen ina fata dai baki fada mata tazo ba.

Umma tace how bangane ba kina nufin ya hafsat din ce keda Mai sannan baba bakwa san taje anti Salma tace eh ita.

Haba Salma yazakiyi haka miye anfanin haka zumunta fa kuke san yankewa keda umar din ina tinanin ki ina hankalinki yatafi lokacin da kika yadda  da abinda Umar yafada.

Yaron Zaki biyewa haba Salma mea haka. Kada kimanta duk abinda tayi miki yayarki cefa. Kai ya isa anti yazaki dinga hadani da wata chan kisani ni Salma na yanke zumuntar dake tsakanina da hafsat.

Daga yau banida wata alaka da hafsat wlh anti ki rubuta ki ajiye komai kama da Hafsat nagani a Sokoto bama gidan su nafisa ba saidai uwarta ta haifi wata badai itaba.

Ta yafa gyalenta tace ki gayawa sauran da zamu tafi tare zasu iya samuna a airport nizan wuce da kayan also am not doing this for you I am doing it for my son ohh!! Namata an nunamin cewa ba dana bane.

Duk yadda kaso dan daba kaika haifesa ba sai anma iyaka da shi so I am going there for my nephew tayi hanyar fita sukayi clashing da Jay dake tsaye yanajin duk abinda suke ya buda baki yayi magana tadaga masa hannu.

Tafice zuwa airport bayan tasaka anyi loading kayan lefen. Jay ya kalla umma ya maida kansa gefe yayi side dinsa.

Sokoto

Anti Mimi ce tsaye tsakiyar filin family house din tana kallan decorations dinda akayi kalar blue da pink  Masha Allah komai yayi daidai.

Kiran da ammi ta kwala matane ya janye hankalinta daga decoration din ta nufi part dinsu ammi tace Mimi naga tin safe kike tsaye baki huta ba kuma gashi sun kusa isowa.

Kitafi kiyi wanka ki shirya. Anti Mimi tace toh ammi Amma Bari in duba kitchen ko sun Karasa abincin da zaaci. Aa Mimi angama basai kintafi ba to ammi kayan dazasu tafidashi. Mimi nace kitafi zuwa wanka.

Tashiga zuwa cikin gida tayi wanka ta shirya cikin wani farin Swiss Les mai kyau da tsada tasaka silver din sarka da Yan kunne tana karasa daurin dankwali taji horn din motoci tayi saurin saka takalmanta ta fice itama.

Anti Salma kuwa batayi miniti arbain a airport ba taga isowar sauran da zasu tafi tare sun shigo inda zasu jira jirgin anti hajara ta zauna kusada ita tace Salma tace naam anti hajara tace kiyi hakuri duk abinda akayi kiyi hakuri.

Kinsan Khadija nasanki kamar fiyeda zaton ki kinsan bazata zabi hafsat akanki ba Amma ki bata lokaci nasan itama abinda yafaru tin baya yana damun ta kinji. Anti Salma tace ba matsala anti amma nidai daga lefennan bazan sake saka kaina a lalurar nan ba.

Suna cikin jirgi kamin su tashi wayarta tayi Kara MY SON rubuce a jikin wayar ta daga ya gaida ta ta amsa yace sunda jima suna magana bansan mai yake fada mata ba amma naga tana dariya.

Da saukarsu a Sokoto suka fito zuwa harabar airport din anti salmace tsaya kayan suka fito ta lodawa masu turawa suka fito tare ta Kira wata number bayan minti biyar da wayar saiga motoci Prado Prado ne farare har guda goma sai motocin sojoji guda takwas. A gabansu motocin suka tsaya suka shiga sannan aka saka kayan suka kama hanyar gidan su nafisa.

Mintin talatin cif suka kawosu gidan aka bude musu gate sukayi parking. Kamin su karasa fitowa su Anti amarya, matar big daddy da sauran manyan suka fito zuwa tarbon.

Bayan anyi settling ne anti Mimi tace to su fara cin abinci ko daga baya a buda kayan anti Salma tace sam ba abincin da zataci sai angama komai . Suka kwasa suka nufi meeting parlor din gidan inda aka jera kayan .

Akwatina ne saiti saiti har saiti goma kala daban daban kowane saiti yanada akwati kwara shidda gabada idan an hada akwati sittin. Matar big daddy tace Mimi keda kannen ki kufara budawa kinsan aladar nan gidan basai na maimaita miki ba.

Suka nufi set din farko Mai kalar peach Yana da duwatsu a jiki suna shining babro baro ajiki an rubuta JAYFEEN da pure silver. Set na farko atamfa atamfa ne duk ciki ba wacce tayi kasa da dubu dari dan duk aura ne sai wasu na dubu hamsin guda tara wadanda da suka.

sai wata unique one mai matsakaitan patterns anyi rubutu da manya manyan baki JAYFEEN a jiki anti Salma tace please Mimi fiddata daga cikin kwalin ki juya ta koda aka juyata aka budata hotansa ne gudan Kato da signature smirk dinsa haka sukayi ta budar Kaya saida suka budasu kap sannan aka maida.

Mommy (matar big daddy) tace to muje kuci abincin ko anti Salma tace tukunna ga wannan wata jaka faratas tabawa mommy tace wadannan sarkokine na zinari sannan ga wannan ta fidda box kanana guda biyu.

Aka buda daya makulai ne guda biyu dayan kuma wani diamond ring ne anti Salma tace wadannan makullan motoci ne wadanda aka saka a ciki daya tana nan a Sokoto dayar kuma tana a Abuja wannan zobe cewa yayi a Bata idan yazo zaiyi mata bayani.

Sannan tabata wata farar  takarda tace ga kudin dinki yanxu zamu iya cin abincin yanxu. Suka tafi sukaci abinci sunaci sukaga ana fitowa da kaya nan tsakar gida ana ajewa. Da suka tashi tafiya akayi musu sha tara na arziki sannan suka hada musu da tukuici.

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now