CHAPTER 26: ARCHES

3.3K 203 15
                                    

Yau takama Monday kuma yau Jay zai koma aiki, plus yau suka cika sati biyu da yan kwanaki da aure. Tunda safe ta tashi ta sauko kasa direct kitchen ta shiga ta duba store tayi deciding tayi doya da egg sauce for breakfast.

saida ta fidda duka kayan datake bukata sannan ta koma kitchen din taga Fatima da Zainab a tsaye suka gaisheta ta amsa.

Tace harkun gama naku breakfast ne Zainab tace eh anti sai nafisa tace ok har Fatima takai inda kayan cleaning suke zata fara aikinta saita tuna nasihar da anti Mimi tayi mata tace Fatima ki bar wannan shara da mopping din harsai idan Maigidan ya fita kinji sukace ok tace kukoma side din ku.

Ta cigaba da aikinta sai takwas da minti goma ta karasa jera kayan saman dinning tayi sauri ta koma sama ta shiga dakinta tayi wanka. Da fitowarta ta nufi closet batajima ba ta fito sanye da riga da skirt na atampha fitted ta daura dankwalin ta sannan tayi make up simple ta sanya sarka da Yan kunne

 Da fitowarta ta nufi closet batajima ba ta fito sanye da riga da skirt na atampha fitted ta daura dankwalin ta sannan tayi make up simple ta sanya sarka da Yan kunne

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

ta fito ta nufi downstairs tsinkayo Jay tayi Yana tafiya gurin dinning table din sanye da uniform dinsa complete na sojoji Banda hularsa daya rike a hannu.

Kayan sunyi masa balain kyau suka sake fidda farinsa da kyansa ya zauna itakuma ta karasa dinning din har zata zauna wata zuciya tace ki gaidashi koba komai Yana gabadake kuma ai mijinki ne ta Dan rinsina tace Ina kwana ya amsa Mata da lafiya.

Ai kuwa ji tayi kamar ta hadiye zuciya ta mutu duniya ba abinda ta tsana irin ta gaida mutum ya amsa mata da lafiya daka amsata da lafiya gwara ma kayi shiru ka kyaleta. Taja karamin tsaki sai a kunnensa ya dago kansa da sauri ni zakiyiwa tsaki tayi shiru a tsawace yace ba magana nake miki ba take tafara shaking jikinta na rawa murya na rawa tace Dan Allah kayi hakuri.

Yace hakuri nace kibani ko tambayarki nayi ya buda baki yayi magana yaga hawaye na zuba a idanta. Ya rufe idansa yace ya salam yasake buda idan yana tinanin its not proper yadinga loosing temper dinsa around her sabida koba komai nafisa yarinya ce she is only sixteen.

Wata zuciyar tace masa sai mea zaka zauna ta rainaka ne ya tamke fuska yace kina jina ta daga kanta yace ni sa'ankine dazaki daga mun kai bazaki buda baki kiyi magana ba. Tace inaji yace akwai abubuwa biyar danakeso ki kiyaye su these are the rules to my house.
1. Bana cin abincin masu aiki dan ban yadda da tsaftar su ba
2. Bana san kazanta ki kiyaye
3. Ban amince wata wai ita mai aiki ta shigar mun daki da sunan gyara ba ko a side Dina bana sansubi idan kinga zaki iya bari su gyara naki dakin to shikenan your choice.
4. Ban yadda ki tafi Koda makwabta ne batareda izinina ba
Lastly kada ki kuskura ki bari koda gaisuwa ce ta hadaki da sojojin gidannan do you understand tace Masa eh.

Tayi serving nasa tayi serving kanta sukaci abinci lokacin daya karasa yace Mata the food was delicious thank you nina tafi. Daukar backpack dinsa dake nan dinning yayi ya fice tace Allah yatsare.

Bayan ya fita tasa su Fatima kwashe kayan dake dinning table din sannan ta hau sama ta share dakinsa ta mope ta wanke toilet dinsa ta nufi dayan dakin shima kurace kawai yayi ta gyarashi sannan ta gyara parlor dinsa shima ta share ta mope.

Sannan ta nufi side dinta shima ta gyara shi ta koma dakinsa ta chanja bedsheet din ta chanja masa wani ta shiga toilet dinsa. Dan lokacin datake wanki ta lura laundry basket dinsa yacika ta duba mafi yawanci boxers dinsa ne da singlets sai jallabiyoyinsa da kayan baccinsa ta sakasu cikin bucket ta wankesu tas sannan ta daurayesu ta fito dasu ta shiga dakinta Koda ta duba time 11 tayi kawai tayi wanka ta Sanya doguwar riga gown ta English gown dark green ta yafa gyale fari a kanta ta dauko kayan data wanke ta sauka kasa.

Bayan gidan taga wurin shanya ta shanyasu sannan ta koma ta kofar baya ta shiga ta dauka robar ruwa taji Fatima na magana tace anti kinyi bakuwa tace ok ganinan zuwa tasha ruwanta sannan ta fito main parlor taga hadiza zaune harzata Mata magana saita tuna yaune rana ta farko tun bayan kawota da hadiza taxo gidanta saita karasa ta zauna tace sannu da zuwa malama saidai ban gane ki ba.

Hadiza tace lallai nafisa kin cika yar iska ni zaki kalla kicewa baki ganeni ba nafisa tace idan nasanki zance bansanki bane hadixa ta girgiza kai tace kin rama shike nan tace eh yanzu ki kyauta kenan kusan satina ukku bakizo ganina ba. Deeza tace wlh nafisa rashin lafiya nayi kaman in mutu nafisa tace ai nadauka dagangan kikaki zuwa hala mea yake damun ki kedai maleria nayi.

Suka Dan taba fira deeza tace am nafisa bazaki koma school bane tace to ni baimun maganar school ba kuma bansan yazan masa maganar ba deeza tace to idan ya dawo yau saikiyi masa maganar tunda 3 weeks kawai kikayi missing kila ke yabari ki karasa to zanyi masa magana imsha Allah.

Sai da 12 tayi sannan suka shiga kitchen deexa tace nizan tafi gida zanyiwa my dear lunch zaa kaimasa nafisa tace yanzufa kikazo har zaki tafi Bari kawai ai sai insa abincin harshi tinda shima zaa kaimasa lunch office.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
LIKE SHARE AND COMMENT ♥️ ♥️

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now