CHAPTER 28: MISTAKES

3.4K 239 10
                                    

Bayan sunyi dinner gabadaya huka hau sama kowa yayi side dinsa da shigarta dakinta saida tayi wanka sannan tayi alwala tayi sallar Isha. Bayan takarasa azkar dinta ta shiga closet nata ta fidda kayan baccinta da robe daya.

Harta kwanta taji wayarta na ringing ta daga muryar Jay taji yace ki hada mun tea ki kawo mun daki yana gama fada ya kashe wayar ta saki baki tana kallon wayar wato ko please bazai ce ba tayi tsaki ta dauka robe dinta ta daura

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Harta kwanta taji wayarta na ringing ta daga muryar Jay taji yace ki hada mun tea ki kawo mun daki yana gama fada ya kashe wayar ta saki baki tana kallon wayar wato ko please bazai ce ba tayi tsaki ta dauka robe dinta ta daura.

Bayan ta hada ta tafi dakinsa da sallama ta shiga ta duba dakin taga baya nan ta duba toilet nanma baya nan har zata koma dakinta taga tea din zai huce idan bai sha yanxu ba ta dauka tray din ta fito.

Ta fito tayi hanyar dakinta da niyar nemansa kila yana dakin ta kula da corridor dinda ke karshen falon kuma taga haske Yana fitowa daga cikin corridor din wata zuciya tace to ki duba kila Yana chan.

Tabi wannan hanyar ta taga wata brown din kofa ta buda ta shiga katon office ne daga gefe ga shelves har sun kai gurin pop din dake office din cike da littafai sai katon table din glass ne
sai white leather chair sai wani makeken hotonta lokacin ranar kamun hadiza ne a cikin gida from head to toe ta tuna lokacin amma batasan an dauka hoton ba.

Tabi wannan hanyar ta taga wata brown din kofa ta buda ta shiga katon office ne daga gefe ga shelves har sun kai gurin pop din dake office din cike da littafai sai katon table din glass ne sai white leather chair sai wani makeken hotonta lokacin r...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Har zata koma sai sukayi ido biyu da kofar dake dab da kofar shigowa office din ta buda kawai tasa kai a ciki ba komai cikin dakin Banda  wata kujera sai TV's manya manya guda takwas a ciki duk a kunne sai mutane dake ciki da alama meeting yake  kamin ta karasa shiga ciki yayi sauri ya danna wani remote dake hannunsa

Ya juyo a tsawace yace what the hell are you doing here mea yakawoki nan get out of here and never ever make the mistake of stepping foot in here. Yana cewa get out ta yadda tray dinda ke hannun ta.

Mug dindake kan tray din da sauran abubuwa dake sama duk duka tarwatse a kasa jikinta na rawa ba abinda bata so a rayuwarta irin ai mata tsawa ko fada tanajin lokacin dayace kada ta sake shigowa ta juya aguje gurin tabar office din ta taka daya daga cikin mug dinda ya fashe.

Wani ciwo taji har cikin zuciyarta tasaki wata gigitacciyar kara am sure da dakin ba sound proof bane da nawaje sunji da karfin hali irin nata ta sake taka kafar ta wuce da gudu tana tafiya jini na zuba jin Jay na kiranta yasa tayi saurin shigewa dakinta ta kulle kofar a fuskarsa.

Tana sakin karar ya tashi daga seat dinsa yanufeta ganin ta juya da gudu kuma ga Jini gurin daya zuba yasashi jin ba dadi bai sake jin takaicin kansa ba saida yabita yaga jinin data zubar akan hanya ya kara hanzari ganin zata shige daki ya Kira sunanta amma tayi shutting door din to his face

Ya fara knocking kofar ganin yafi ten minutes yana knocking taki budewa yasa shi balla kofar ya shiga ganinta yayi kwance kan gado rike da kafarta tana kirin amminta yayi sauri harya dauketa sai kuma ya ajiyeta ya shiga closet dinta ya fito rike da jallabiya da gyale.

Ya saka mata su saman nightwear dinta sannan ya dauketa ya sauka kasa direct waje yafita sojojin dake gida suka nufesa bai tankasu ba ya buda wata jar mota ya dannan start botton yaja a guje yayi hanyar asibitin da suke zuwa.

Sojojinsa ganin yana gudu a tsiyace harya tashi bige wani mutum sukasan ba lafiya ba suka kunna giniya akaita basu hanya sabida giniyarsa ta musamman ce dawuya yasa a kunnan jiniya amma idan an kunna to tamkar jiniyar ambulance aka kunna dan mutane jayewa zasu yitayi har sai ya wuce.

Tafiyar minti talatin takaisa TRIPLE A AND SON'S bai ma tsaya parking din arziki ba ya fito ya dauketa daga gidan baya ya shiga nurses suka taso suka karbeta suka shiga da ita ciki by yayi kusan minti talatin yana to and fro a gurin chan ya koma reception yace how is she

nurse dinda ke gurin tace eh to doctor on night duty zai shigo nanda minti goma yace you mean tun dazu ajiyeta kawai kukayi Kuna kallanta bakuyi treating dintaba cikin halin ko in kula tace to abin ne yafi karfin mu glass din ya shiga chan ciki kuma ta zubda Jini sosai am surprised ma takai yan.....

Bata karasa maganar ba ya watsa mata wani mari wanda saida takai kasa ya tarwatse duk kayan dake gurin sannan ya fidda wayarsa ya kira wata number danaga ansawa Doctor shareefa ta daga yace doctor kina asibitine tace aa wlh yanzun nan na fita daga asibitin ko minti biyar banyiba yace please ki jiyo ki dawo emergency ne tace ok ya kashe wayar.

Ya kalla nurse din yace you are fired and kisani cewa rayuwarki duk asibitin da kika tafi bazasu daukeki aiki ba ya fizge ID card dinta dake kan wuyanta yayiwa wani soja alama da hannu kan yazo ya karaso ya bashi ID card din yace make sure bazata sake samun aikiba Koda kuwa a matsayin cleaner ne.

Jin an kira sunansa yasa ya juya sukayi ido hudu da Dr shareefa wata mata zatayi shekara 30 farace Amma guntuwa tasaki murmushi tace Marshal Umar yau Kaine a asibitin mu kodai jikin daddy ne yatashi yace aa muje madam ce ba lafiya  Koda ya ankara nurses duk sun taru ana kallo yace get back to work a dan tsawace.

Suka shiga dakin datake tayi examining kafar kamin tace nafisa ki daure kinji zan cire ceramic din tana taba glass din tadan ja kadan.  Tasaki kara sosai ta janye kafar ta girgiza kai tana hawaye Dr shareefa tace haba nafisa kidan daure ba ciwo a haka zakiyi nakuda ki haifo mana babies masu kyau ta lallasheta amma tana sake taba kafar ta saki kara Dr shareefa tacewa daya daga cikin nurses dinda ke dakin ta Kira jay.

Jay da tundazu yaji kararta ganin nurse tazo kiransa ya shige gaba ya shiga dakin Dr tace wlh Marshal akwai matsala da alama matarka bazata bari a cire wannan glass dinba cikin kwanciyar hankali kuma the longer yana cikin kafar the more risk dinda zatayi facing na infection sannan kuma jinin zaiyita zubane harsai an fidda yace what do you want me to do tai mishi alama daya rike nafisar.

Nafisa data rintse ido jinta kawai tayi an rungumeta ga kuma kamshin tiraren Jay daya cika mata hanci bazato ba tsammani taji wani balain ciwo tarasa daga inane tasaki wata Kara again chan kuma idanta suka fara kullewa.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
LIKE SHARE AND COMMENT ♥️ ♥️
.
.
.
.
.
.
.
Happy Iftar guys Allah ya karbi ibadunmu.
.
.
.
.
.
Do vote please ⭐⭐⭐

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now