CHAPTER 34: LEAVING

3.1K 241 22
                                    

Tana shiga dakinta tayi sauri ta shiga wanka bata dauka lokaci mai tsawo ba ta fito tayi drying ta saka kayan bacci tasanya turarukan baccinta sannan ta kama hanyar dakinsa tayi knocking sannan tayi sallama ta shiga.

Saida ya amsa sallamarta sannan ta karasa shiga ciki tayi tsaye ta dukar da kanta yace come and sit down ta karasa ta zauna yace kin karasa packing dinki tace aa yace muje yaja hannunta suka koma dakinta suka shiga closet dinta ya fidda suitcase medium size ya buda shi ya fidda kaya kala bakwai sannan yasa Mata kayan dayake tinanin zata bukata sannan ya kulle yace kwana bakwai zakiyi sannan ana bakwan zaki dawo.

Gobe jirgin karfe takwas zaki shiga  so get ready early basai kinyi breakfast ba. Ya sake Jan hannunta suka sauka kasa ya zaunarda ita ya diba abinci yasa Mata a plate yace eat nasan kinajin yunwa. Taci abincin amma ba sosai ba tace ta koshi harzata dauka plate din ya rigata daukewa ya shiga kitchen ya wanke tace kai bazakaci ba yace aa I don't have apatite tace no bari indafama Koda indomie ce.

Kamin yabata amsa harta Jima a kitchen indomie tadafa wacce Tasha vegetables sannan tayi kyau harta gaji kokamin ta gama har kamshin indomie din ya game gidan. Tasa a plate ta dauko ta juyo ganinsa tayi tsaye bakin kofar kitchen din yana kallanta ta dukar dakanta shikuma ya karaso ya amsa indomie din.

Yace mata nagode ya ajiye kan dinning. Ta dauko ruwa da juice dinda ta kula yafi sha wato ice tea ya sa a tray ta ajiye kusada shi sannan ta zauna ta kula yafi minti ukku Bai taba abincin ba tace ko bakansan indomie din in dafa wani abu it's not good to go to bed with an empty stomach or is something wrong.

Yayi dariya ganin ta damu yafara cin indomie din yace tayi dadi it tastes delicious I love it Zaki koya mu yadda kikayi tayi dariya tace aa zandafama ne duk lokacin dakaso.

Goma na dare suka kwata bacci nace asuba tagari nafisa da jay. Washegari tinda ya tasheta sallar asuba ya tafi masallaci Bata sake ganinsaba har zata jirasa sai kuma tayi tinanin bazatayi breakfast ba kawai ta haye gadon nasa ta koma bacci.

Jay kuwa bayan ya dawo masallaci kitchen ya shiga ya fere dankali ya soyashi sannan ya soya mata eggs ya ajiye kan dinning table. Saida ya hada mata tea sannan ya koma sama yana shiga dakinsa ya Kai idansa Kan gado hangota yayi ta lullube da duvet din tanata baccinta ya kashe AC din sannan ya koma daidai kanta yadinga shafa gashin kanta Yana huramata iska a fuska.

In no time ta buda idanta tace mishi good morning yace morning love kishirya it's almost time ta tashi ta tafi dakinta ya hana ya nunamata toilet dinsa ta shiga tayi wanka ko kamin ta fito harya ajiyemata kaya kan gado.

Cikin minti goma sha biyar ta shirya tsap sannan ta dauka jakkarta da takalma ta duba a cikin jakkar taga komai nata na ciki daga kan wayarta har charger da earpieas. Ta kulle ta sauka kasa ganinsa tayi zaune saman dinning table kansa cikin hannuwansa biyu ta karasa ta janye hannuwan nasa ta kallesa.

Kamin tayi magana ya katseta yaja kujerarsa baya ya azata Kan cinyarsa ya fara bata abincin tanaci harta koshi ya bata ruwa tasha sannan yace let's go ta girgiza kanta ta kalla baincin alamun yaci Sarai yagane mea take nufi amma yace baki koshi bana dan yanasan yagani ko zatace yaci. Tace bazakaci ba yace kin kusa kiyi latti so muje idan nadawo zanci ta dauka juice din tabasa tace yasha ya amsa yasha yace happy ta daga kanta.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
.
LIKE SHARE AND COMMENT ♥️ ♥️
.
.
.
.
.
DO VOTE PLEASE ⭐⭐ ⭐

YAR GIDAN MODIBBOWhere stories live. Discover now