Girls outing.💅

302 38 5
                                    


🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.

Duniya! Abin ayi hattara da ita ce domin idan kayi sakaci wata rana zata saka kuka.


Abubuwa da yawa sun faru cikin sati biyun da suka wuce, su Bintu yanzu an zama ƴan gari, makarantar su kuma suna maida hankali haiƙan musamman da abunda suke koyan ya kasance ɗaya daga cikin jerin burukansu na rayuwa, hakan yasa suka dage sosai, so suke su zama wasu abun tunƙaho a fannin.

Wata sa'in in sun gama class ɗinsu suka fuskanci basu gane wani abun da aka koya masu ba sai sui joining next badge tunda duk abu ɗaya ake koya masu a rana.

Kuma basu da wata matsala a gida dan kamin su fita sai sun tabbatar sun gyara ko wane lungu da saƙo na gidan sunyi girkin safe, da rana kuma sai Aunty Naseey taji da girkin da sun dawo kuma su ɗora na dare, dan haka ita kanta Aunty Naseey ƙarfafa masu gwiwa take sosai ganin yadda suka dage, Kawu Sulaiman ganin Maryam ce ke riƙe ƙaramar waya sai ya siya mata babba ita ma, ranar sun sha murna.

Cikin pocket money ɗin da yake basu suke yin sub ɗin data sai su shiga youtube da daddare sui ta kallan vidios akan kwalliya da girke-girke, da yake dama in sun dawo gida suna exchanging knowledge, ita Maryam ta koya ma Bintu abunda aka koya masu a make-up class ɗinsu na ranar.

Ita kuma Bintu ta koya mata nasu sirrin girke-girken da kuma dabarbarin da ake yi in an samu kitchen accident tun daga kan su knife cut har zuwa in mutum ya cika gishiri a miya ya zaiyi ya daidaitu ko in ya ƙona abinci ya zai ɗebe ƙaurin daga abinci da dai sauran dabarbarun kitchen, tunda har yanzu basu fara practical ba sai next week, dama sai sunyi a rubuce sai suzo su fara practical, hakan ne da suke yi yake ƙara sa suma abun yana ƙara zama a kansu sosai.

Fanin ɗayan karatun nasu kuma na wayewa shima sun fara ɗaukar course ba laifi dan ma ƙarancin kayan gayun na kawo masu cikas, Bintu kam kullum tana gefen Meerat tana sa mata ido a wayance tana kwasar karatun taku, jan aji da gayu.

Tun Meerat bata sake mata har ta fara, sanadin wata rana da sukai quiz a ajin Bintu ta cinye, bayan an tashi ne Meerat ɗin ke tambayarta ya akai duk ta riƙe abubuwan da akai masu tun farko, nan Bintu ke sheda mata ɗan jotting ɗin da ta keyi ko wane class shine ya taimake ta ta rirriƙe in ta duba shikenan.

Da haka har Meerar ɗin tayi snapping note ɗin nata, aiko washe gari da ta zo ita ta fara mata magana akasin kullum da ita Bintu ce ke fara mata sallama, daga nan kuma har suka ɗan fara hira jefi-jefi yanzu haka sunyi exchanging numbers suna chatting sosai.

Binafa da Deey kam soyayya sai wacce bata halalta ba, yanzu wata shaƙuwa ce sosai ta ƙara ƙulluwa a tsakaninsu, Maryam da Adeel ma suna narka tasu a waya san rai barin ma yanzu da yake shirye-shiryen dawowa gari sati biyu masu zuwa.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now