Babban gida.

624 71 9
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎


STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).


Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa.



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.







Alhaji Muhammad Mani cikakken bahaushen mutum ne wanda yake da dattako da halin girma, zaku iya sashi a rukunin tsaka-tsaki a fannin kyau sai dai baza ku sashi a cikin sahun fararen mutane ba domin baƙine amman kuma ba wulik ba, mahaifiyarshi Hajiya Amina wanda ake kira da Ya Gwal-Gwal sunyi auren saurayi da budurwa da mahaifinshi Alhaji Sammani ɗan mutan ƙaramar hukumar Mani dake garin Katsina ta Dikko, ɗakin kara.

Tun farkon aurensu har zuwa lokacin da Alhaji. Sammani ya amsa kiran ubangiji suna zaune ne a garin Mani, matar shi Ya Gwal-Gwal macece me ji da sarautar masifa don ƴar bala'i ce ta bugawa a jaridu, ko a waccen zamanin da take budurwa haka ake gwagwarmaya da ita, ta-Allah dai yasa matar Sammani ce domin hannun riga sukai a wajen halayya, a haka dai ya gurgura da ita har Allah ya albarkace su da yara ɗai-ɗai har bakwai.

Muhammadu shine babban ɗansu sai Atika wacce a halin yanzu take zaune da mijinta da ƴaƴanta biyar a ƙauyen Caranci.

Dije ita ke bi mata inda ita ma take Lamba gidan mijinta tare da ƴaƴanta shidda.

Sai Uwani da tai aure Bindawa sai dai a halin yanzu auren nata ya mutu da ƴaƴa uku wanda uban ya riƙe kayansa ita kuma tana can hannun dagin mahaifinta tana zaman jawarci.

Daga ita kuma sai Tanimu wanda ya gaji da zaman gida ya fantsama garin Lagos neman abunyi sai dai tun bayan tafiyarshi kimanin shekaru tara kenan be kewayo gida ba kuma ba wanda keda labarinsa.

Bala ke bi mashi, shi kuma tunda ya haɗa certificate ɗin secoundary ya yaye boko, Muhammadu wanda ƙannen nashi ke kira da "Yaya Babba" shi ya siya mashi mota yana kabo-kabo zuwa garuruwa, shi ke sauke yara a makaranta da safe ya wuce aiki sai kuma dare, har yau Allah bai sa layin markaɗen shi na aure ya iso ba duk da yana taɓa harkar mata.

Balaraba itace autar su kuma zakkar gidansu domin a halayyar mahaifinsu ba abunda ta rago, tas ta dama shi ta shanye.

Ita kuma ƙaddara sai ya haɗa ta da mugun miji wanda tasha baƙar wahala a hannunshi da ƙyar aka ƙwaceta a hannunshi sai da ma aka haɗa da kotu sannan ya yadda ya saketa.

Sai Allah yasa ba ɗa tsakaninsu, dan da ta samu cikin wuya ko mai cikin da kanshi ya ke zubar da abunsa, inya sha ya cake a lokacin da yake jin kansa a wata duniyar nan ne yake lakaɗa mata dukan mutuwa yayi kaca-kaca da ita, yanzu shekarar su ɗaya da rabuwa tana zaune wajen ya Gwal-Gwal.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now