R.I.P😭.

324 35 9
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎








STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).






Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.




SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.






Duniya kamar hadarin mushaki ne (hadarin da baya ruwa) ana ganin hadari ya hadu kamar da gaske ruwa za a yi sai kaga ya watse wayam!
BINTU.....






Page3⃣8⃣: R.I.P😭.




Cikin wani irin tashin hankalin da bazata iya misalta ya take ji a zuciyarta ba take ta shirya kayansu cikin akwati, ko da yake ba zata ce shiryawa ba domin dai a hargitse take watsa kayan nasu a cikin jakka, burinta kawai a yanzu tasan meye dalilin faɗuwar gaban da take tayi tun wayewar garin yau.

In kuma wani sashe na zuciyarta ya tuna cewa nan da wasu ƴan-awanni da baza su fice ɗirgar yatsun ɗan-adam ba zata san wace iriyar ƙaddara ce ta afko ko take shirin afkowa cikin rayuwarta, ba zato ba tsammani, sai taji gaba ɗaya duniyar tai mata baƙiƙƙirin, sai taji duk ilahirin jikinta yayi sanyi laƙwas!.

Har yanzu bata daina hango yanayin jiki da ma fuskar Kawu Sulaiman a lokacin da yazo gaya masu ko ma meye, wanda take tsammanin yana ƙunshe da dalili da kuma sanadin faɗuwar gabanta, ba tantama abunda zasu je su riska shine zai bata amsa bayyananniya.

Yau safiyar Jumma'a ana saura kwana biyu su tafi ranar lahadi kenan, tunda sun gama hutu ran litinin zasu koma makaranta, tunda sassafe Kawu Sulaiman ya fita wajen aikin kamar yadda ya saba sammakon zuwa aikin, sai dai ƙarfe tara bata ida datsawa ba ya dawo gidan a hargitse, abu ɗaya ya iya cewa dasu, "Kowa ya fito za muje Mani kamin sallar azahar!".

Daga haka bai ƙara cewa dasu komai ba, amman yanayin shi da yadda yai maganar kawai ya isa ya gaya ma mutum cewa "tabbas ba lafiya ba!" musanman matar shi da duk duniya ba wanda ya kaita sanin halinshi, ita har ta riga ta gama yanke me ya faru a cikin zuciyarta.

Cikakkun minti sha biyar basu rufa ba da dawowarshi duk suka ɗunguma cikin mota cike da rashin sanin makomarsu, shi kuma ya cigaba da jan mota a gaggauce ya zuƙi hanyar MANI, Maryam da Bintu kam ko wanka basu yi ba dan suna kitchen ne ma suna aiki sai dai suka kashe komai na wuta suka haɗa kaya suka zura hijabai duk da wannan ba shine abun damuwarsu ba a yanzu, babbar DAMUWAR ita ce, shin me zai riske su ko me zasu riska!?.

Cikin wannan taraddadi suka ɗago suna haɗa ido, da hannu Maryam tai mata alama da "wai meke faruwa ne?", alamun "nima ban sani ba!" ta maida mata, gashi duk sun kasa tambayar Kawun nasu abunda ke faruwa, daga haka kowa ya cigaba da kiran sunan Allah da addu'oi a cikin zuciyarshi cikin fatan suyi katari da alkhairi.

Bintu ce ta kasa haƙuri ta jawo wayarta ta kira Inna, ko wanne bugawa na ringing ɗin da wayar keyi yana tafiya ne dai-dai da bugawar zuciyarta, can ƙasan zuciyata kuma na roƙo da ɓoyayyiyar murya "Inna dan Allah ki ɗaga ki faɗa mun komai lafiya, ba wani a cikin masoyanmu da yai rauni DAN ALLAH INNAH!".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now