Girls outing 2.

316 37 5
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.

Wani lokacin biye ma zuciya ba ya zama mafita.





Da suka gama duk gaban gidansu Teemah aka sauke su, ko baka shiga ba kasan gidan ya haɗu ba laifi, dama tun kan su iso Meerat ta kira dirabansu, tace yazo gidansu Teemah ya ɗauke ta, ana sauke su kuwa ba daɗewa sai ga shi ya iso, tace ma su Bintu suje ta sauke su gida, sukai sallama da ƴan matan bayan sunyi exchanging numbers suka tafi, har gaban gida su Meerat suka sauke su da kayansu sukai sallama ta tafi, Viturous mai gadin gidan yazo ya taya su ɗaukar kaya har gaban door step ɗinsu, Maryam ta zaro 2k daga cikin kuɗin da Alhaji minister ya zuba mata a jaka ta bashi, ya amsa yana ta washe baki yana masu godiya ya wuce.

Su kuma suka ja kaya cikin gida ƙiiiii! cike da rashin gaskiya, Aunty Nassey tana can side ɗinsu tana wanka, Tatus da Amir ne kawai a falo tana mashi wasa, suka kwashi kaya suka kai ɗaki suka aje, sai da suka gabatar da sallar la'asar kana suka rage kayan jikinsu suka faɗa kitchen tuwan semo da miyar kuɓewa ɗanya ce rubuce a jikin menu ɗin daren yau, dan haka shi suka shiga girkawa.

Suna cikin aikin Aunty Naseey ta leƙo tana faɗin "ƴan-mata har kun dawo?...." sai kuma taja ta tsaya tana kallonsu yadda kasan an canjo su haka ta gani tace "daga outing kuma sai ku canjo fata?" ta faɗa da zolaya ganin yadda sukai wani irin kyau suna sheƙi, duka suka sa dariya suka ce "Hmm Aunty Naseey bari dai a natsa za kiji story".

"A lallai kam to bari naje na shirya" nan ita ma Tatus ta shigo dama tun ɗazu takr binsu da tambayar inda suka je aka masu lalle mai kyau haka nan ta cigaba.

Suna gama wa suka koma ɗaki suka yo wanka, yau wankan ma na musanman sukai, sai da suka daɗe suna cuɗa jikinsu kowa ta fito sai tai shar, dukansu suna ɗaure da towel suna shafa mai, Bintu na gaban madubi saman stool ita kuma Maryam na zaune gefen gado kusa da madubin, gaskiya ba ƙarya sunyi asalin kyau, ke kanki in kika gansu a yanzu zaki sha ƴaƴan wasu mashahurin mai ji da nairori ne.

In suka haɗa ido sai kowa ya nuna alamun rashin gaskiya, Maryam ta saki ajiyar zuciya tace "ke dai sis faɗi abunda ke ranki".

Bintu ta jijjiga kai tace "ke ma faɗi abunda ke naki ran".

Sai kuma suka sa dariya gaba ɗaya, Bintu tace "wallahi bamu da gaskiya!" suka ƙara kwashewa da dariya ta cigaba "ke nifa a tsorace nake wallahi na ma rasa gane abunda muka aikata dai-dai ne ko ba dai-dai bane?".

"Hmm naki wasa ne sis, ni da Alhaji Minister ya maƙale mun wallahi ji nai kamar zanyi fitsarin wando tsabar tsoro, musanmman da naga yadda su Teemah da alhajinta ke shige ma juna suna taɓa jikin juna hankali a kwance, gashi abokinshi ne, wlhi Allah yaso shi da baiyi gigin taɓa ni ba Allah da sai na tara mana ƴan-kallo a wajen nan".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now