The Engagement.

316 35 20
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎



STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).



Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.




SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.







My love come back to me when you wake up, our dream has come true..........
Al'ameen













---------------------------------------

"Ƙarfe uku da rabi!" ta ƙara maimaitawa a cikin zuciyarta a yayin da take kallon agogon dake manne a cikin ɗakin Naty, "To wai shin me ma Bintu zata tsaya yi har tsayin wannan lokacin bata dawo gida ba? bayan sunyi da ita yau zata dawo da wuri, to me ya tsaidata?" gabanta ne ya faɗi rassss! sanadin tunanin da ya gifto mata a zuciya na ko dai ba lafiya ba, dama tun ɗazu gabanta ke faɗuwa, hakan yasa ta gaza sukuni ko kaɗan sai ambaton Allah kawai da takeyi.

Yakumbo ce ta fito daga madafar Naty inda hayaƙin wuta ya cure tafff! ta isa drum ɗin ruwa ta ɗebo tana wanke hannu ganin ta kammala girkin da tun ɗazu suke fama da wuta, ta tashi, ta mutu, gasu da baƙi kuma a cikin gida, duk da dai ba'ace baƙi ba dan duk ƴan-uwane kuma makusanta ne ga Naty da margayi Baba ɗan tsoho, ita ma hankalinta a tashe yake rashin ganin bintu da ba'ai ba, Naty kam ma ba'a maganarta.

Dai-dai lokacin ta turo ƙyauren kewaye tana faɗin "wai har yanzu ba labarin takwarata? Kai jama'a! Allah gamu gareka!" ta faɗa tana gangarawa magudada don ɗora alwallar la'asar tana ta mita ita kaɗai, sauran mutane kuma ana ta jajanta abin tare da faɗin "za'a ganta ne ma insha Allahu, kuma ba abinda ya sameta sai alheri".

Jin muryar Maryam na doko sallama yasa Inna saurin fitowa daga ɗakin da taketa zirga-zirga a cikinsa domin jin ba'asin aiken da aka ma Maryam ɗin, sai ganinsu tai tare ma da Lamunden.

Naty ce da ta gama wanke ƙafafu dai-dai lokacin da suka shigo tai zunbur ta miƙe tana faɗin "To kun same ta dai ko? halan rashin babur ne ma ya tsaidata ko?" ta faɗa tana ƙara leƙen ta inda Bintu zata fito, sai da taga wayam ta maida masu kallon tambaya.

"Wallahi ko Naty bamu ganta ba, ga Lamunden nan ma ashe ita bata je makaranta yau ba, ni kuma yadda mukai da ita zamu haɗu a nan gidan kuma zamu baro makaranta da wuri yau" Maryam ta faɗa idonta narai-narai.

"Yau ga shegantaka ba sai kuje makarantar ku dubo ta ba?" cewar Naty tana faɗi kamar zata make su.

Lamunde ce tace "Eh Naty mun je gidansu Sajida ta shaida mana tabbas Bintun ta bar makaranta misalin ƙarfe ɗaya da ƴan mintoci, sai dai mu kuma bin hanyar makarantar".

Da sauri Inna tace "ina zuwa bari na kira Saleem naji ko yana kusa" ta faɗa tare da komawa cikin ɗakin ta ɗauko wayarta, ta shiga ƙoƙarin kiransa dan tunda ya gama internship ɗinsa a Katsina ya samu aiki a can general ɗin, dan haka duk weekends yake dawowa gida weekdays kuma yana KT, akasin sati biyun da suka wuce da ya ɗauki hutun wata ɗaya don ya shirya ma bikinsa da ya ƙarato, wanda aka sa a ƙurarren lokaci a cewarsa kenan fa, wai dan ansa wata huɗu kawai, hakan yasa yanzu ko yaushe yana gida, sai babansa da yake ɗan kama ma aikin kasuwa, gefe ɗaya kuma yana tashi hidimar bikin.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now