The news of joy.

360 40 2
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.


Kada ka damu da cewa ƙarya ta miƙe ƙafa, tabbas ƙarya zata gushe. Kada ka damu da tambayar yaushe ne gaskiya za ta bayyana? Lallai za ta bayyana komai daɗewa. Abin da ya kamata ya da meka shi ne, menene matsayinka; a kan gaskiya kake ko a'a?.


Allah sarki! Allah gatan bayinsa, yau safiyar yau cike da murna su Bintu suka tashi, sanadin alkhairin da kwatsam ya riske su a daren jiya, Inna na zaune tana ida kammala saƙar ƴan-makaranta da aka kawo mata sanadin ba wuta take amfani da aci-bal-bal, kawai sai ga kiran Ya Sulaiman ɗinsu, kamar a mafarki taji yana sheda mata ya biya mata Makkah, kuma bama ita kaɗai ba hadda Murja da matarsa Nasiba, dama shekaru biyu da suka wuce ya biya ma su Baba da Naty da shi kanshi suka je suka sauke farali, wannan shekarar kuma sai ya biya ma matar shi da ƙannanshi, tunda yanzu ba laifi kasuwancinshi yana ta haɓaka yana samun bunƙasa da albarka, ga kuma ɓangaren aikin shi yana ta samun promotion.

Inna kam bata iya misalta iya adadin farin cikin da ta shiga daga lokacin da wannan labari mai daɗi ya riski kunnuwanta kawowa yanzu, wanda kuma take jin zai dauwama har abada, lallai Allah ne kaɗai me share kukan bayinsa, wannan azumin da ya wuce a goman ƙarshe ba abunda tafi roƙa kallar Allah ya kaita ɗakinsa ko sau ɗaya ne kamin ta cika, sai ko addu'oin da tai ta ma ƴa-ƴanta, ashe Allah ya karɓa mata, ita kam tayi mashi godiya ba iyaka domin har sadaka da azumin nuna godiya ga ubangiji sai da tayi.

Mutanen arziƙi suna ta taya su murna, Baba kam da labari yaje kunnensa tsohon tsumi ne ya taso, duk sai yaji bai ji daɗin da ba shi bane ya kai Inna makka da kansa ba kamar yadda yayi ma sauran matansa, amman still yai mata murna matuƙa saboda shi a yanzu baida kuɗin kujerar makkah, su Iyatu dasu Gwoggo kam duk sai suka mayarshe da abun na baƙin ciki, ko dan ya haɗu da wadda suke ma hassada ne?.

Sobada haka ne ma su Bintu bacci jiya sama-sama suka yi shi, Inna kam data farka sai ta sami kanta da ɗoro alwalla tana jera nafilfili duk godiya ga Allah, safiyar yau suna ta shirin zuwa Abuja, inda Sulaiman ɗin ya kira su domin a ida kammala shirye-shirye, ana haka Yakumbo ta iso, nan wata murnar ta ƙara kaurewa, suko matan gida sai suka koma ƴan kallo dan basu da tacewa domin dai ɗan uwan Inna ne da kansa ya biya mata makkan nan, ba mijinsu bane balle a yada habaici, Yakumbo duk da yaran ta taho, haka suka ɗunguma sai gidan Naty nan ma baje kolin murna akayi, suna zaune diraban Sulaiman da zai kaisu can Abujai ya iso, daga Inna sai Yakumbo suka tafi yaran kuma aka bar ma Naty.

***

Lokacin da mahajjata suka tashi tafiya kuwa da ƙyar aka ɓanɓanre Bintu daga jikin Innarta wannan ne karo na farko tunda ta tashi tai wayau, zasu rabu da Inna na tsawon lokaci, Inna kam lallashinta tai tayi tana ce mata "Bintu kar ki manta akwai mutuwa fa, in na mutu fa kece magajiyar ƴan-biyu, ki riƙa tuna kece babba mana! kuma shi babba juji ne, dole kece ya kamata ace kin fisu ƙarfin zuciya".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now