The forbidden loss!.

492 47 8
                                    


🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.








Hmmm! me zaka faɗa a lokacin da dukkan wani tunani ya gushe a cikin zuciyarka? me zaka yi a lokacin da dukkan wani ƙarfi ya ƙare a jikinka? Ya zaka ɗauki al'amarin da baka da wani zaɓi a cikinsa?...........
BINTU.






--------------------------------------------

A hankali kalmomin likitan suka fara zarya a iska kamin su samu damar shiga jijiyoyin kunnuwanta zuwa wani lungu na fahimtar bayanai da yake cikin ƙwaƙwalwar kanta, gama fahimtarsu tsab!, yasa zuciyarta tayo wani irin tsallen hargowa ta cigaba da bori a ƙarƙashin ƙasusuwan ƙirjinta, shin waye a kusa? da zai zo ya faɗa mata a sauƙaƙe likitannan ya zauce! waye ne zai faɗa mata likitan nan baya da kalma ta 'hankali' kwata-kwata a jikinsa? ya ko san me yake gaya mata kuwa?.

Ya ɗauki kalmomin da yake gaya mata a matsayin wasa a wajensa, bayan ita a ɓangarenta sune kalmomi da zasu lanƙwasa duk wata ƙaddara ta rayuwarta!, sune za suyi sanadin duk wani sauran farin ciki da yai saura a rayuwarta!, shin yau wace irin baƙar rana ce take gani ita Bintu? dama ƙaddara ta aje mata haka a rayuwa bata sani ba?.

Kaaai! inaaa! ƙarya ma likitan nan yake mata! Sai dai ko in bai san aikinshi ba, duka-duka mintuna nawa ne tazararta da saduwa da farin cikin da a yanzu ake mata iƙirarin yai mata nisa, nisa wanda ba zata taɓa cin masa ba a doron ƙasa!.

Abunda ko a mafarki bata taɓa yin makusancin sa ba, ko a tunane-tunanenta ƙwaƙwalwarta bata taɓa hasko mata abu iri wannan ba, zato bai taɓa kawo mata shi ba, balle tasan wane irin tashin hankali ne zata riska in hakan ya faru a zahiri!, sai kawai yau da farar safiyar Allah a nemi kawo mata labarin ƙanzon kurege? wanda kunnuwanta sam baza su juri ɗauka ba? kai da sake ko kuma kuskure a wani wajen!.

Miƙewa tai cikin rashin kuzari ta doshi ɗakin duk da cewa da ƙyar take iya haɗa hanya sanadin juya mata da taga gaba ɗaya asibitin nayi, tana tafe tana rangaji idanunta na lumshewa tana ƙoƙarin buɗasu kamar wacce tai tatil, ko da yake tayi tatil ɗin, amman da tsan-tsan tashin hankali, ruɗani da baƙin ciki haɗe da rashin sanin makoma!.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now