Duniya juyi-juyi.

506 55 7
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎


STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).




Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.




🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.











Ku zode wa ma'abota mutunci ƙananan laifuffukansu, domin ba wanda zai yi kuskure daga cikinsu sai hannunsa ya kasance a hannun Allah yana daukaka shi.





Hello readers its been a while huh? i know!, i wasn't stable dats why, just going here and there! but now i am! So here is a long update i hope u'll lyk it, but i can't promise you a tear-free ride couz dis chapter contains a horrible moment😪😭.

Anyways Happy reading🙌.





Page 1⃣1⃣: DUNIYA JUYI-JUYI.






"Yauwa Bintu tunda yau an tashi makaranta da wuri, muyi maza mu biya ta gidan su Sajida mu gaido ta da jiki".

"Aiko dai Karime kar ma tace bamu da kirki, ko da yake ma bamu dashi ɗin, sati ɗaya fa kenan tana kwance babu lafiya amman bamu dubo ta ba".

"Hmm ke dai bari, ni in ta dawo makaranta ma banje dubota ba bansan da wane ido zan kalleta ba Allah".

"Ba ke kaɗai ba wallahi, ga shi Sajida akwai mutunci tana san mu Allah".

"Eh mana tana son taga mun zama ƙawaye da ita".

"To amman nifa bansan sabon gidan da suka koma ba! duk da tace can ƙasan layin mu ne".

"Ke dama Bintu Allah sai a ɓatar da ke a ɗan ƙaramin ƙauyen nan namu, ina mamakin yadda baki san gurare ba sosai a wannan ɗan ƙaramin garin, kuma wai anan aka haife ki aka raine ki, kika kuma taso a cikin garin nan, kiɓ!".

"To kin ganni nan wallahi ba inda nake zuwa in ba wajaje huɗu ba zuwa biyar, daga gida, gidan su Naty, gidan Yakumbo, makaranta, asbiti in ta kama sai ko gidan ku, ko ita Sajidar sau ɗaya na taɓa zuwa tsohon gidansu".

"Caɓ mu kam mun sha yawon yarinta, ban tunanin akwai inda ban taɓa zuwa ba a garin nan Allah".

"Sai kace wanda kare yaci ƙafarta" Bintu ta faɗa tana dariya Karime na taya ta tana bata labari ɓacewar da suka taɓa yi suna yara garin ɗan banzan yawonsu, Bintu na kwasar dariya har da riƙe ciki.

Karime ta kaisu har ƙofar gidan su Sajida, sannan suka shiga, sun taras ma ta warware sosai tunda wanke-wanke ma suka iske tana yi, sun gaishe da Innarta da yayyanta kana suka mata ya jiki, sun ɗan taɓa hirar makaranta kana suka fito, ta rako su har bakin ƙofa tana mai jaddada masu gobe da izinin Allah tana nan fasowa makaranta.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now