Suprise!!!

359 36 0
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.

Rayuwa itace wannan bugawar dake gefen zuciyarka, wannan motsin da a kullum yake sawa kaga safiyar gobe, wannan kiɗan ɗake sawa ka yaƙi tsoranka, sannan wannan dukan dake baka ƙwarin gwiwar da zaka fuskanci ƙalubalen rayuwarka.


"Kar ki damu da duk abunda zaki ji an faɗa a kanki in har kin san kina akan turbar Allah ne, in har kin san zuciyarki tsarkakakka ce baki nufin kowa da sharri sai alkhairi, duk wani al'amari da yazo maki a rayuwa kar kiyi gaba-gaɗi, ki bi shawarar manzon rahama da yace ku nemi zaɓin Allah akan al'amurorinku, kiyi istihara, har a zuciyarki ki sallama ma Allah, kisa yaƙinin shi ne zai maki zaɓi na gari domin shi yasan gobenki, kuma kome ya zaɓa maki to ki bishi sai kiga dai-dai a rayuwa.

Lokacin da kika zo min da maganar Al'ameen me na umarce ki da kiyi?" a hankali Bintu tace "istihara Inna".

"Masha Allah ko da na saki ba ke kaɗai na bari kiyi ba, nima nayi maki sosai kuma kamar yadda kika maido min amsar yanayin da kika ji, hakan ta kasance a guri na dan duk lokacin da nayi sai naji maganar ta ƙara kwanta mun a rai, naji ina son tarayyar ku da shi domin ina ji a jikina alkhairi ne, mun tattauna da Saleem ya faɗa mun komai, zai turo magabatanshi ai magana, daga lokacin da aka yi bincike akansa aka samo shedar shi mutumin arziƙi ne, to na baki goyan baya na ɗari bisa ɗari akan aurenki dashi, kawai dai yanzu sai dai mu cigaba da addu'a muga hukunci da Allah zai zartar!".

A hankali Bintu ta ɗora kanta bisa cinyar Inna tace "na gode Inna" ta faɗa a kunyance cike kuma da jin daɗin kalaman Inna, dan sai yanzu take gane ba ƙarami so ne take ma Al'ameen ba, har bata iya misalta wane yanayi zata shiga in Inna batai na'am da shi ba.

*** *** *** *** ***

A ranar da suka je islamiya, ita da Maryam suka gaya ma mallamansu cewa za suyi tafiya gobe, nan ta nuna masu wayarta suna ta murna ana ta latse-latse, gallery ɗinta duk hotunansu ne ita da shi wasu kuma ita kaɗai, hadda wanda ya ɗauketa bata ma sani ba, wasu ma bacci take.

Karime sam bata ji dadin tafiyar da za suyi su barta ba, ita ma sai cewa tai zata je ta tambayi babansu ya barta taje Kano can wajen dangin mahaifiyarta tayo masu zumunci tunda ta rabu da zuwa dama.

Washegari da safe Kawu Sulaiman yazo ya kwashe su sai birinin tarayya, da ƙyar aka ba Bahijjah haƙuri dan kuka tai tayi ita ma sai taje wajen Tatus, cewa akai ta bari sai sunyi hutu kana akaita.

Sun sha hanya, sun sha bacci har sun gaji, tunda suka zo Zuma rock kawu Sulaiman ya fara nuna masu gari har suka iso Jabi unguwarsu kenan, dai-dai gefen wani ƙaramin masallaci ya sha kwana, sai da yayi horn sannan gate man ɗinsu ya buɗe gate, ya danna hancin motar shi a cikin compound ɗin gidan, gida ne na haya mai hawa huɗu kowa da iya wajensa, a hawa na biyu suke.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now