Burin Rai...

350 33 0
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.






Ruhina da Burina wasu abubuwa ne dake tafiya a tare, ɗaya baya iya aiki saida ɗaya, idan har na rasa burina to tabbas na rasa ruhina.




Yau satinsu ɗaya kenan a Abuja suna hutawarsu, shekaran jiya ne suna zaune da daddare Kawo Sulaiman ya kira su yake shaida masu ya sayo masu form ɗin wata makaranta ta koyan sana'oi, maganin zaman banza, abubuwa ne da yawa akebkoyarwa a makarantar, yace kowa ta zaɓi ɗaya sai ya biya masu, domin ko wane abu ɗaya zakai kimanin wata uku kana koyansa, gashi hutun nasu da yawa yafi da sui ta zaman banza.

Kar ku tona irin daɗin da suka ji, sai murna suke tuni sun kira gida sun shaida masu ana ta san barka, ita dai Maryam tunda ta karanta jerin abubuwan da ake koyawa a makarantar tace kwalliya zata cike, ita kuma Bintu ba abinda ya ɗau hankalinta sai fanin cateering da ta gani inda za'a koya masu abincin kala-kala, na gargajiya, turawa har dana yarukan Nigeria daban-daban, ga kuma foreingn dishes suma, sai fannin baking snacks da drinks, gaskiya shi yafi birgeta tana da burin taga ta iya girki kala-kala a rayuwarta.

Haka kowa ta cike ra'ayinta sannan suka maida mai form ɗin, a washe garin ranan yaje ya biya ya masu komai, yanzu haka gobe ne za'a fara classes ɗin sabbin ɗauka suna ta shiri cike da zaƙuwa.

A can Mani kuwa ƴan uwan Al'ameen sunje sun nema masa izini sun kuma kai kuɗin gaisuwa an kuma ansa, dan haka zuciyar masoyan fes take kullum suna manne da juna a waya da dare kuma sai yaje sunyi hirarsu abunsu hankali kwance.

Wahsegari ta kama litinin, ƙarfe 8 na safe sun gama shiri tsab kuma duk sun kama ma Aunty Naseey aikin gida, Kawu Sulaiman ne ya kwashesu sai da aka sauke Tatus makaranta kana ya kaisu wajen ya basu kuɗi ya nuna masu inda zasu hau bus in sun tashi, duk yai masu bayanin yadda zasui transport har gida, ya tambayesu ko sun gane? Suka ce "eh" yace in ma basu gane ba su kira shi a waya, sukai mai godiya suka sauka, makarantar babba ce sosai, an rubuta sunanta da style a gaban gate ɗin.

Anyi grouping ɗinsu into 3 badges, ko wane badge 3 hours zasu nayi, wanda suka fara 8 za sukai 11, wasu su shiga 11 su gama 2, wasu 2 zuwa 5 shikenan sai kuma wahegari, sukai shawara da Maryam su ɗauki ajin safe, haka kuwa akai suka rubuta sunansu a ajin ƴan safe, da haka suka rabu kowa ya tafi fanninshi.

Ajin basu wuce su sha biyar ba kuma mata sunfi yawa, Bintu ta zauna kusa da wata yarinya da yanayin shigarta ta birgeta, kallo ɗaya zaka mata kasan yarinya ce mai class wayayyiya, ƴar hutu wacce ta iya gayu, Bintu ta mata sallama yarinyar ta amsa a taƙaice cike da yauƙi ta juya ta cigaba da latsa wayarta cikin ko in kula tana taunar cingum cikin natsuwa.

Daga haka Bintu taja bakinta tai shiru sai dai rabin hankalinta na kan yarinyar yadda take abubuwanta, shigarta, yadda take taunar cingum kamar tana tausayinshi, yadda ta riƙe wayarta ma kanshi abun kallo ne, ga hannunta fari tas yaji adon zobuna amman ba barkatai ba a tsari, akaifarta kuma tasha baƙin lalle.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now