Yau da gobe kayan Allah.

471 51 5
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎


STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).



Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.







Duniya da rayuwa abokai ne, idan ka biyewa rayuwa ita kuma duniya zata biye maka, amma kuma ka sani cewa zasu kai ka su baro wata rana.






Ƙamshin tuyar albasa a cikin man unguriya ne yake tashi a muhallin da take, wanda ya isa har cikin ƙofofin ramukan hancinta, iska ta zuƙa cikin wani irin yanayi na ƙwaɗayin ƙamshin da ya cika mata ciki taf!, ƙu-lu-lu! Sautin da cikinta ya bada kenan cikin ƙoƙarin amsar saƙon da zuciyarta ta bayar, hannu ta kai bisa kan shafaffen cikinta tana shafawa a hankali.

Sai lokacin ta fara ƙoƙarin buɗa idanunta, tas! ta sauke su akan hasken safiya da ya fara ƙoƙarin hudowa cikin ɗakin, juyawa tayi akan hannunta na dama, akansu idanunta suka fara sauka, suna cikin jerin takalmanta dake jere a cikin shoe rag, a hankali ta isa gare su ta jawo su tana shafawa, ta rasa wane irin so ne take ma takalman nan? ko kuma dai wanda ya bata takalman ne? to har yanzu dai bata san ma zuciyarta ba.

Sannan kuma har yanzu abun yana mata kamar mafarki, in ta dubi takalman sai taga kamar jiya ne Yaya Al'ameen ya bata su, sai dai in ƙidayarta ta kama dai-dai shekara ɗaya kenan cif-cif da bata su.

Cikin shekara ɗayan nan kuwa? Zata iya cewa ba ƙaramar shaƙuwa ce ta shiga tsakaninta da Yaya Al'ameen ba, ko da yake ma duk wanda ya zauna da Yaya Al'ameen dole yaji yana jin sa a zuciyarshi, saboda mutum ne mai ba ma abunda ya damu dashi kula ta musamman.

Sannan yana da wasa da dariya uwa-uba barkwanci, ba ya da saurin fushi sannan mutum ne shi me fahimta, tana ga tun kan ta kai ko ina, wa innan abubuwan kaɗai sune take tunanin suka ƙwace ma Ya Saleem fadarsa a zuciyarta, wata sa'in sai ta rinƙa jin kamar ma tafi son shi akan Namiji tilo! wanda ta mallakawa yardarta a da, wato Yaya Saleem.

Wayar Inna ce ta taimaka wajen shaƙuwar da sukai da shi, domin a kullum suna manne da juna a waya, daga ƙarfe 10:30pm zuwa ƙarfe 12:00pm wannan ajajjen lokacin wayarsu ne a kullum, banda haka kuma duk lokacin da take da sarari sai tayi mai flashing shi kuma ya kira su sha firansu, yana bata labarai masu daɗi da ban dariya.

Wasu labaran ma da yake bata in ta tsaya tana tuna su, sai taga kamar shine ma ya ƙirƙira su da kanshi don kawai ya sata nishaɗi, i zuwa yanzu kuwa duk wasu ƙannenshi ba wanda bai sada ta dasu ba ta waya domin su gaisa, barin ma Zarah takwararta sun saba sosai, hatta Ammiensu yana yawan bata ita a waya suna gaisawa dan haka a gidansu kowa ya santa a murya a ido ne kawai basu ganta ba.

Yana zuwa ganinta a-kai-a-kai, sai dai tun bayan zuwansa gidan sau ɗaya bata ƙara sauke shi a gida ba, gidan abokiyar sirrinta: Naty, nan take sauke shi, duk da yakan nuna yana so ya gaisa dasu Baba, amman taƙi bashi goyan baya.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now