farincikinta yana tare dashi..

216 21 0
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.

--------------------------------------------------------

Na gama fahimtar cewa duk wani farinciki da zan iya samu a rayuwa to yana da alaƙa da shi, ban san ko akwai kallar son da nake yi mashi ba? Shin yana faruwa haka ko kuwa ni kaɗai ce?.
BINTU.

-------------------------------------------------------

Yau juma'a su Maryam suka gama zana jarabawarsu, ita kuma Bintu yanzu da safe ita kaɗai ake bari a gidan, har yanzu in ta samu kanta a cikin ƙaɗaici bata iya tare zuciyarta daga kukan rashin Innarta a rayuwarta.

Tana matuƙar kewarta sosai da sosai, duk da cewa ba sallar da zata idar bata nema mata rahamar ubangiji ba, sannan duk lokacin da ta kalli wani abu ya tuna mata da ita, ko taji wani abu da ya tuna mata da ita, ko kuma ta faɗo mata a rai, sai tayi mata addu'a.

Tun lokacin da tana raye dama tana mata addu'a sosai sai dai yanzu ta linlinka saboda yanzu ba abinda Inna tafi buƙata kallar addu'arsu shiyasa bata taɓa ɗaga hannu ta manta da ita ba, kuma tana tuna ma su twins akan su riƙa mata addu'a.

Wannan ƴar damuwa data ƙara shiga cikin satin nan sai duk ta ƙara ƙanjamewa ta rame sai ɗan hasken da fatarta ta ɗan ƙara ta murje saboda sabilai da mayuka natural da take amfani dashi.

A cikin satinnan ne kuma Al'ameen yace mata zai zo, gashi har yau juma'a satin na niyar ficewa amman be riga yazo ba, dama yace baze gaya mata ranar da zaizo ba suprise visit ze mata.

Sai dai tun tashinta yau take taji a jikinta kamar yau zaizo, gashi tunda ta tashi bata jin wani kuzari dan bata wani samu bacci jiya ba, kwana sukai kan su Jawad da suka ƙi bacci sabida allura da aka masu, komi cikin sanyi jiki take yinsa.

Tun bayan fitarsu a daddafe ta gyara gidan tana kuma ji da sanwar dambu da ya sha zogale da gyaɗa, sai gab da azahar ta sauke, ta shiga wanka, da ta fito ne ta tada salla, bayan ta idar ta jawo kwandon shafarsu ta shafa mai, ta ɗauko madubi tana kallon kanta.

Tsayawa tai tana ganin yadda idonta ya faɗa saboda ramar da tai, taɓe baki tai ta dangwalo hoda da niyar shafawa, har ta ɗora foam ɗin akan kuncinta sai kuma ta maida ta rufe ta ture kwandon gefe, ji tai bata son yin kwalliyar kwata-kwata dama rabonta da shafa koda dai-dai da hodar ne ta manta.

Ko kaya bata sa ba, da zanin wankan ta kwanta kan gado ba ɓata lokaci ko bacci ya sureta, ta tabbata kona minti talatin bata yi ba taji ana tada ta, a wahalce ta buɗe ido tana kallon Maryam tare da faɗin "meye?".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now