For your sake!💔

364 49 36
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎




STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).


Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.







Zan iya sadaukar da komai nawa domin kai, hatta ko da rai na, dan rashinka a kusa da zuciyata zai iya zame mun wani babban giɓi a rayuwa, always remember that letter R is for Red, Red is for Blood, Blood is for Heart, and my Heart is for you.......
BINTU......

How can i express that your presence means the world to me? Don't you know i can't do without you? But why do you choose to make me miserable? WHY? WHY!???.......
AL'AMEEN..





Wani wahallallen miyau ta haɗe ƙut!, tana ƙara duban mutumin da ya zuba mata idanu, yana zaune kan tashi kujerar tazarar taku ukku kacal tsakaninsu, da alama gadinta yake da kuma wani abu daban, dan taga waya a hannunshi yana saitata, dai-dai lokacin wayar tai flashing haske akan fuskarta bayan ƙarar ɗaukar hoto ta biyo baya.

Wato wannan ne hasken da ake ta hasketa dashi tun ɗazu, hoto ake mata, to akan wane dalili ma? ko da yake har yanzu akwai dalilai da yawa da bata sani ba kuma take ɓiɗar saninsu.

Wani mutumine ya fito daga cikin bukkar, shi kam siriri ne sosai baya da tsayi, baƙi ne amman ba wuluk ba, akwai alamun hutu a tattare da shi, gashin kansa ya tara shi yayi tozo, kuma yayi dieying ɗinsa fari ƙal!, yana sanye da wando da riga da wani ɗan siririn glass akan karan hancinshi, amman kallo ɗaya zaka masa ka fahimci irin ƙaurayen nan ne da suka riga suka saida ma duniya zuciyarsu, kuma babu ɗigon imani a zukatansu, wayace manne da kunnensa yana magana da alama waya yake.

Cikin takunsa ya nufo inda take, da sauri mai aikin ɗaukarta hoto ya tashi ya tare shi a hanya, tun fitowarshi ma ta lura dukkan sauran mutane kowa ya bar abunda yake ya miƙe tsaye.

Kafeta yai da idanu yana cigaba da wayarsa, hakan yasa tai ƙasa da kanta tana ɗan jujjuya wuyanta da yai sanyi, sanadin ɗaɗewar da yai a sargafe, dukkan wata ƙwarin gwiwa nata ya ruguje kaf!, balle har ta iya ta sako masu tambayar da dukkan zuciya da gangar jiki ke azalzalarta akan ta firta.

"Eh ta farka!", taji ya faɗa, jim kaɗan kuma yace "to Alhaji kamar dai yadda ka faɗa hakan komai zai tafi, zamu cigaba da ajeta har zuwa isowarshin".

Shiru yai na wasa ƴan-daƙiƙu kamin ya cigaba da cewa "To shikenan in yazo zamu aika shi kamar yadda ka buƙata, amman ita ya za'ai da ita?".............

"To shikenan baka da damuwa" ya yanke wayar yana bushewa da dariya dukkan jikinshi na jijjiga da dariyar, yana ƙara narke idonsa akanta.

Wanda ke tsaye a gabanshi ya taya shi dariyar tare da miƙa mai wayar dake hannunshi, tana tsammanin hotunan ya shiga kallo, ji tai yace "Weldone! yanzu ka tura mashi hotunan, nasan bazai taɓa iya kaucewa wannan tarkon ba".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now