THE PHONE CALL.

472 48 7
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎



STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.


SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.







Zaifi a tsaneka da yadda ka ke. Da a So ka da yadda ba ka kai ba.







Ana tashi a islamiya suka jero suna tafiya a hankali, kamar masu tausayin ƙasa, Sajida bata zo ba kuma basu san dalili ba, ko da yake ma ita ƴar-Al-ƙa'ida ce! Ba kowacce rana take zuwa makaranta ba, tun shigowar Bintu aji Karime ta lura cewa kamar damuwar dake kan fuskarta ya linku ne akan wadda take ciki safiyar yau zuwa lokacin da suka rabu.

Yau ba tare suka zo makaranta ba kasancewar Karime ta fita da wuri domin kai ɗinkin sallah daga nan kuma ta wuce islamiyar, hakan yasa ta kira Bintu ta shaida mata akan ba zata samu biyo mata ba kar tai ta jira.

Tafiya suke yi shiru, ganin bata da niyar magana yasa Karime faɗin "yaya dai Sis? Ya na ga kamar kin ƙara shiga wata sabuwar damuwa? Ni dana ke expecting inga kinzo da labari mai daɗi! Ko har yanzu baki gama tunanin bane?".

"Hmmm Karime! Ina fa labari mai daɗi a nan? Na gama tunani na kuma gano komai, sai dai abunda na gano bai mun daɗi ba sam!.
Tun lokacin da na fara saka idanu a kansa, zuciyata ta aminta dashi, tayi mashi babban masauki a cikinta, mu'amula da shi yau da gobe yasa tayi sabo mai wuyar fassara da shi, halayansa da kalamansa suka sa ta buɗe mashi ƙofar soyayya ba tare da tayi shawara da ƙwaƙwalwa ba".

"To yanzu kuma meye abun rashin daɗi a nan?".

"Yanzu da na gano cewa zuciyata na cikin rafin son ya Al'ameen, ruhi da duk wata gaɓa ta gangar jikina sun mara ma zuciya baya akan hakan, sai dai ƙwaƙwalwata ce kaɗai tayi masu mubaya'a, ita kaɗai ce take gargaɗar zuciya akan rashin sanin makomar soyayyar Ya Al'ameen data faɗa, akan rashin sanin dacewa ko cancantar yin hakan?".

"To me yasa?".

"Hausawa suna cewa son maso wani ƙoshin wahala, idan na biye ma zuciyata? To bani da mafaka a cikin zuciyar da take ma bege, domin gurin da take nema a cike yake, me shi ya riga da ya siyar da filin ga wata zuciyar daban, ba zaki bani shawara na biye ma ƙwaƙwalwata ba? domin gujewa ɓacin rai?".

"Lallai Bintu! Ke kuma me yasa kike tunanin Ya Al'ameen baya sonki, wallahi ko ni kaina ina hango kalar tarin soyayyarki a ƙwayar idanunsa, ko kalar kallon da yake maki ma kaɗai ya isa ki fahimci cewa ya jima da sonki a zuciyarsa, kuma a cikin kaso ɗari! na baki casa'in da biyar kan cewa, maganar budurwar shi da yai maki ba gaskiya bane! Zolayarki kawai yake.

Kuma ba dan komai yayi hakan ba face dan ya gwada ko saƙon sirri da zuciyarshi ke aika ma taki a ɓoye ya soma tasiri a gareki? Sai kuma gashi ya samu amsar shi a sauƙaƙe".

Hannu bintu ta ɗora a goshi cike da takaicin abunda tayi, tsayawa tai daga tafiyar ta dubi Karime "yanzu ne na ƙara fahimtar wasu abubuwa da yawa da ya rinƙa mun duk cikin ƙoƙarin yaga ya sani kishi, duk cikin ƙoƙarin ya gano kona faɗa tarkon da ya ɗana mun, kuma yaci da yawa, amman daga yau na daina wasan ɓuyar nan da shi, kamar yadda yai mun wasa da zuciya? Nima sai na gara tashi zuciyar domin yaji ko da daɗi, sai na tabbata na cire mashi duk wani hasashe, da zaton shi akan zuciyata, a wannan lokacinne zan fara soya mashi gyaɗa a hannu, wannan shine zai zamo tukuicin wahalar da ya bani har na tsayin kwana uku ban ji muryarsa ba".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now