School bus.

865 87 6
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*DUNIYA MAKARANTA CE.*

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa.



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))


SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.

Wanda ya yi tafiya a tsakatsakin burinsa, ya hadu da ajalinsa.



Page0⃣2⃣: SCHOOL BUS.

Filo tasa ta ƙara toshe kunnuwanta dashi amman duk da haka tana jiyo kwakwazon dake tashi a cikin gidan nasu wanda inda sabo yaci ace ta saba, domin tunda asubar fari ake fara bala'i a gidan a kuma rufe dare dashi, yawancin wanda ake da asubar kwanannene wanda ba'a ƙarasa ba ko kuma wanda ba'a samu damar yin shi ba saboda shigar dare, domin dai a gidan nasu ba'a bashin masifa.

Cike da takaicin dabi'ar ƴan gidan nasu taja tsaki tare da tillar da filan ganin baya tare mata komai dangane da muryar Ya gwal gwal dake ta aukin rakaɗi wanda a wanda bai san ta ba sai yayi tsammanin bata ba saba'in da biyar baya ba.

"Allah ya kawo mana agaji a al'amarin gidan nan, abu sai kace yaƙi! ko gari ba'a bari ya ida wayewa za'a soma da surfa bala'i, kullum kullum dai ba a gajiya da ɓaɓatu".

Bintu ta faɗa tana mai saukowa kan ɗan matsakaicin gadon ƙarfenta dai-dai irin na ƴan makaranta, hula ta ɗora akan doguwar rigar baccinta ta isa bakin taga tana mitstsike idanu tana faɗin "yau kuma da wacce za'a soma?".

Daga tagar ɗakinta tana iya hango tsakar gidan nasu ko tace filin masifar gidan dan duk wata masifa kamar doka anan ake yinta.

"Shi kenan dai ace ita kenan! duk wata matsala a gidan nan daga fuskarta take fitowa, in banda rashin imani yaushe aka taɓa haka? wacce a cikin matan gidan nan ta taɓa aikata irin hakan? da har za kace ba laifinta bane! in tana ciwo bakin nata ma ciwo yake da ba zata sanar ma kowa ba asan abunda ake ciki, sai kawai tabar yara ƙanana da yunwa bayan Allah bai hana mu wanda za mu sama bakin salati ba! wannan ai rashin tausayi ne ko da yake bata san ciwonsu ba tunda ba ita ta haifa ba kuma dama tana nunawa ɓiriri nata kawai ta sani, in taje can ta samu abunda ta ƙunsa ma cikinta da wannan fitsararriyar ƴar tata wato su sauran ƴaƴan gidan ko oho su mutu ko!? Nan wajen fa tun Asuba su Auwalu suka zo suka tasani da kukan yunwa, to wallahi Mahammadu ba za'ai wannan shashancin dani ba, kai in baka san ciwon ƴaƴanka ba to ni nasan ciwon jikokina, da anyi magana kace mai ciki, a'a mai iyali, ka jini da kyau in har bazata iya ɗaukar ɗawainiyar gidan nan da cikin ba to ka bata hutu taje can gidansu in ta haife ta dawo dai dai ta dawo" Ya gwal gwal ke ta aikin masifa tana yi tana gyara ɗaurin zani da ke ta barazanar ɓallewa saboda a saman ƙirji ta ɗaura shi duk da rigar dake jikinta.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now