Back for a reason to love.

504 51 3
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎



STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).




Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.





SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.





Shin kai mai amana ne? ko mai gaskiya ne kai? amana da gaskiya suna tafiya ne a tare, ka rike amana kuma ka faɗi gaskiya zaka buwaya.





Tana fita gate ɗin gidansu ta miƙe samɓal, tafiya kawai take ba tare da ta yanke hukunci inda zata ba, kawai so take tayi nisa da gidansu, tayi nisa daga duniyarta, tayi nisa da baƙin cikinta, tayi nisa da kowa da komai, ta shiga wata sabuwar duniya ita kaɗai, sai take ga kamar hakan ne kawai zai sa damuwarta ta yaye, saboda muddin ta tsaya a gidan nan! kuma ta cigaba da jin kukan twins, tare da ganin shatin bulali a jikinsu, sannan ta cigaba da kallan hawayen Inna, to ita kanta bata yadda da kanta ba akan abunda zata iya aikatawa.

Hawaye wasu na korar wasu akan kuncinta, duk da ana cewa zubar hawaye yana rage nauyin zuciya, to ita dai bata san me yasa wannan hawayen nata dake zuba a halin yanzu, basa wani hoɓɓasa dan gane da rage nauyin da zuciyarta tayi ba, sai ma take ganin kamar ƙara kumbura mata zuciya suke.

Kasancewar rana ce ta hutu, wato asabar kuma ƙarfe goma na safiyar har ta gota, hakan yasa mutane da yawa suna waje suna shan hantsi, jefi-jefi kuma tana wuce gun-gun jama'a wanda suke zagaye a kaskon mai ƙosai, ko wara ko kuma fanke, sai dai duk yawan mutanen nan babu wanda ya nemi ya mata magana ko ya nemi jin ba'asin kukanta, ko dai ba sa lura da ita ne? to wai shin ma! ko dai ta daɗe ne bata gano cewa baƙin jini ne gareta wanda ya sanya mutane basa son hulɗa da ita? Basa son mu'amula da ita? ko ko yaya abun yake ne?.

Ko da yake ma, meye nata na damuwa? kar ma kowa yai hulɗa da itan!, saboda ta lura sanin mutane da yawa shine yake jawo maka ƙunci da yawa! kuma ma a halin yanzu duk wanda yazo da sunan zai yi mata magana ko ya nemi jin ba'asin kukanta, to tabbas zai ƙara jagwal-gwale mata al'amarin ne.

Saboda bata tunanin akwai wanda zata iya fasa ma ƙwan gidansu, ko me yaje ya dawo dai sune a ƙasa dan haka ba amfani, in ta yanke hukuncin gaya ma Yakumbo kuwa? to ba tantama ƴan-sanda zata ɗebowa Iyatu, wanda duk ta ƙare duba da furucin da Baba yayi akan batun to zai iya sakin Inna akan hakan, abunda kuma ko a mafarki ba zata so ya faru ba kenan.

Wata kwana ta sha da sauri kamar tana tsoron kar ƙafafunta suyi kuskuren kaita gidan yakumbo, hakan yayi dai-dai da dosowar wata baƙar mota wacce ke tafiya a hankali kamar mai tuƙa ta baya da lakka a jikinsa, tsaki taja ta ɗauke kallonta daga motar, dan duk sai taji haushi ya kamata tasan ko waye mai motar hankalin shi a kwance yake dole zai tsaya yana wani tafiyar ƙasaita a cikin unguwa, ita yazo ya wuce ma ya barta taji da abunda take ji tsuuut.

Aiko kamar mai motar yaso baƙanta mata dan sai da ya daɗe kamin ya wuce ta, da kamar ma burki yaci sai kuma yaja ya tafi, ita kuma kawai sai ta ƙara saurin tafiyarta, bata yi ƙwararrun minti biyu da rabuwa da mai motar ba, ta tsunkayi murya daga bayanta cikin dodon kunnenta ana faɗin "BINAFAH!".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now