Da Soyayyah.

448 38 6
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.

Ko kana cikin masu matattar zuciya wanda baya ganin ɗan wani nashi? Yi maza ka gyara halinka ɗan makocinka ya zama ɗanka, haka ake yi sai rayuwa ta dawo sabuwa.


"Masha Allah, you look so breath-taking my dear😍". A tare suka sa sowa banda Bintu da ta doɗe baki da hannunta tana murmushi.

"To kin dai gani sai ki dage" cewar Karime.

Maryam tace "ki fara bina sau da ƙafa sai na koya maki".

"Kyaji dashi!" Bintu ta faɗa tana neman layinshi domin taji ya suka isa.

Maryam ta cigaba "nifa namijin da bai san kwalliya baza mu daidaita dashi ba, ni ina so kuma in yi yaƙi yabawa bai isa ba wallahi".

Karime ta amshe mata da "Ke dai bari akwai takaici barin ma in ya zama mijinka, koda kai kana so duk sai ya sagar maka da gwiwa saboda in kayin ma ba gani zai ba balle ya yaba".

Bintu da kiranta ya shiga tai masu alamun suyi shiru tana waya, Maryam Kam da bata jin ɗaya sai ta sa baki tace "kice mashi in kwalliyar tai mashi kyau da gaske, to ya biya wadda tai".

Da sauri Bintu ta matsa gefe, sai da ta gama ta dawo cikinsu tace "ku wallahi kun iya saida hali, dole dai sai kun tuna mashi da ƙuruci yake mu'amula, mtseeew".

Suka sa dariya suna ƙara ƙular da ita, karime tace "ke ma dai kin san halin Maryam ba ruwanta, komai zata faɗi ne".

Tace "to meye amfanin in ci naman shi, ai duk abunda baka iya faɗi gaban idon mutum to kar ka faɗe shi a bayan idonshi".

"Thank God in ma yaji ai yasan halinki, kunfi kusa".

"Kya dawo hanya ne ma wallahi dan kinfi kusa dashi" duka suka sa dariyar maryam.

Bayan la'asar aka fara shirin kai amare, ita kam Bintu tana zaune hankali kwance dan bata sa ran kai kowacce a cikinsu ba, suna zaune daga ita sai Maryam a ɗaki domin Karime ta tafi, sai Bahijjah dake kwance kan gado tana baccinta, Inna da Yakumbo suka shigo, "Ya ana ta shirin kai amare kun sharɓe anan" Inna ta faɗa.

Suka yi kallon-kallo ita da Maryam kana tace "Yo Inna wai hadda mu za a tai?".

"Ji shirmen banza, yo da banda ku? Ku zaɓi wacce zaku raka a cikinsu su dai su Safiyya duk cikin garin nan zasu zauna, Maryam ce da za'a kai Kankia Sai Ruƙayya da za'a kai Katsina".

Maryam tai tsagal tace "Katsina za muje Inna" ta faɗa tana kallon Bintu, Yakumbo tace "ai sai ku tashi dan gaya can anzo ɗaukar Ruƙayyan".

Maryam ce ta tashi ta buɗa wardrobe ɗin Bintu dan ta ɗaukar masu kaya domin ita ba ma tazo da kaya ba sai dai suyi amfani da na Bintun, su Inna na fita tace "Ke banza ce baki gane motive ɗina bane na cewa Katsina, kuma ko ba haka bama zamu ga gari tunda bamu taɓa zuwa ba".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now