"I LOVE YOU" challenge.

342 37 0
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.

Kyautatawa mutanenka shi kuma Allah Ya kyautata maka. Idanuwanka su daina rufewa kan abin duniya da ka samu, wata rana kana ji zaka bar abin da ka tara ko kuma abin da ka tara ya barka. Don haka mu lazimci taimako don kaucewa yin da nasani.



Doguwar riga ce ta material mai taushi ta sanya, sai veil ɗin da zai dace da ita ta yana shi akanta ta ɗauki back pack ɗinta ta shirya komai ta goya abunta, kusan shiga iri ɗaya sukai da Maryam kowa dai da kalar nashi material ɗin, suna isa makaranta suka rabu kowa ya wuce ajinsu, yau su Bintu lab aka wuce sun sha fararen apron da hulunan da aka basu iri ɗaya, Bintu sai ta ɗaura gyalanta bisa kai kamar yadda Meerat tai, sai suka sa Apron saman dogayen rigunansu, sai hulunan da suka coke kan kallabin gefe guda sai suka yi kyau sosai.

In 2s aka ce suyi pairing kansu, Bintu da Meerat suka kama table ɗaya, an rarraba ma kowa abunda zai dafa sannan suka shiga aiki ga komai da ake buƙata nan an aje masu a teburin dake gaban lab ɗin.

An basu time kuma suna yi ana supervising ɗinsu, dan haka da sun tara datti a working space ɗinsu sai su kwashe su goge haka ma wanke-wanke ma basu tara shi, suna ta rounding up, Bintu ta kwaso dattin da suka gama kwashewa a wajensu, tayi waje dan ta zidda a can trash-can ɗin dake waje inda suke kai shi, tana fitowa corridor ɗin wajen taji ƙamshin kallar turarensa, tayi murmushi dan bata yi zaton shi bane, tana ɗago kai bayan ta gama zudda sharar ta hango shi ya shawo kwanar corridor ɗin daga other end ɗin.

Wani sanyi taji a ranta kamar ta ruga ta rungume shi take ji, ita ma tayi missing ɗinsa kwana biyu, ta tsaya tana kallon yadda yake takowa zuwa gareta, yana sakin Mata ƙayataccen murmushinsa.

Komai nashi birge ta yake, daga ɗan nesa da ita ya tsaya ya ƙare mata kallo, a hankali ya ɗora tafin yatsunsa a bakinsa ya manna masu kiss har tana iya jiyo sautin da bakinshi ya bada, muahhh! sannan ya cire hannun ya huro mata inda yai ma kiss ɗin yana kashe ido ɗaya.

Take taji wani sabon yanayi ya ziyarce ta, ba shiri ta sadda gashin idonta ƙasa tana jin yadda bargon kunya ke ta aikin lulluɓeta tun daga kan ƙafafunta har kai, tana jin takunsa yana matsowa kusa da ita kamin ya iso sai taji kamar ta nitse.

"Binana kun kusa gamawa ne?".

"Eh!" ta faɗa still idonta a kasa tana ta ƙara matse packer dake hanunta kamar tana shirin ɓallata.

"Owk bari na jiraki a can waiting room".

Ɗaga mashi kai kawai tayi, da sauri ta buɗe ƙofar dake bayanta ta koma cikin lab ɗin da sauri, tana mamakin ganinshi da tai kwatsam!.

Lokacin da suka gama har anyi awarding masu mark ɗinsu, ta samu bowls ta ɗibar ma Deey cabbage dolimon, Chinese chicken salad, sai apple smoothie ɗin da sukai ta jera a tray ta nufi waiting palour yana zaune yana latsa wayar shi ta shiga da sallama shi kaɗai ne a ciki, ya amsa yana ɗagowa, suna haɗa ido ta tuna abunda yai mata ɗazu da sauri ta maida nata kan tray ɗin data ɗauko, da ta aje tace mashi "bisimillah", sannan ta zauna kujerar dake fuskantarsa, kallonta yai yace "Binana wai bakiyi missing ɗina bane?".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now