The birthday party.

266 27 1
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎



STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).



Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.



Kuɓucewar buƙata ya fi sauƙi daga nemanta wajan waɗanda ba ma'abotanta ba.




Tunda satin bikin Teemah ya shigo basu da zama, sai zirga-zirga, duk sun gama kammala haɗa ɗinkinsu, sun sayo accessories da zasu shiga da komai, daga nan aka fara cin biki, aiko sunyi biki iya biki, irin bikin da su kam ko a labari basu taɓa ji ba, ba inda basu watsu ba domin bikin ba inda bai watsu ba, ma media ne kai hatta tashar farin wata sai da suka sa shagullan bikin, domin dai Alhaji sambo babban mutumi ne me ji da tashen nera.

Wannan karen kam da ƙyar suka rabu da Alhaji Minister sai da ma suka haɗa shi da Adeel ne kana suka samu lafiya.

Tunda suka shiga Farin wata sha kallo kam sun zaga Arewa lamarin da har a garin Mani labari ya ɗauka, yayinda wasu sukaji haushi da hassadar abun, wasu suka ce ai ba abun birgewa bane, yayin da wasu kuwa musanman ƴan makarantarsu da sauran ƙawaye abun ya birgesu matuƙa suna ina ma sune, lallai da gaske fa su Bintu sun zama manyan ƙwari daga hoto da sugaban ƙasa kuma sai a fara nuna su a T.V, suna zuwa bikin manyan mutane irin wa innan.

Ga shagalin da akai a bikin a videon ma in kana kallo abun birgewa ne ina ga a gaban ka akai komai, lallai garin daɗi nesa wai angulu ta leƙa masai, cimar da aka ci, kayan da aka sa, da yadda naira ta koka, sannan wai ma suna daga cikin ƙawayen amarya ah lallai dole ƴan-mata sukai ta ɗaukar aniyar za su ƙulla alaƙa dasu Bintu in sun dawo ko dan suma a dama dasu su waye.

A babban gidansu Bintu kuwa an yada ƙananan maganganu sosai, har da zagin tarbiyar Inna wai ai ga ƙarshen wa'azi da munafunci nan sun gani, Ya Gwal-Gwal kam tai ta bala'i tana zage-zage yadda kasan ance mata karuwanci Bintun keyi, shi dai Baba be tsoma masu baki ba yana kwance kan gadon danni dake shimfiɗe a tsakar gida inda ya buɗe sabon wajen hutawa a ƙasan wata bishiya, yana ta aswakinshi abunshi.

Inna ma dai kamar ko da yaushe bata tanka masu ba tasan so suke Mai-gidan nasu yayi magana yace Bintu ba zata ƙara zuwa Abuja ba, sabidda duk tasan suna baƙin cikin zuwanta Abujan nan.

Duk da haka dai Inna ta aje a zuciyarta cewa in dai suka dawo baza su ƙara zuwa Abujan ba suyi hutu mai tsayi ba tunda ta lura sakewa suke a can, dan ko wancen karen sun dawo mata da rawar kai ne gida, sun ƙaro wulaƙanci, wato sunje sunyi gogayya da ƴaƴan masu kuɗi ko?, ai duk ma ta kusa ƙarewa tunda duk sun kusa aure su tai gidan mazajensu, nan da baɗi sunyi candy daɗa ai shikenan.

*****
Su kam can a Abuja basu san wainar da ake toyawa ba, dan haka hankalinsu kwance kamar tsumma a randa, sharholiyarsu suke san rai kuma duk bada sanin Kawu Sulaiman ake wannan taɓargazar ba haka ma Aunty Naseey ita dai bata hana su fita sai dai tamasu nashiha kamin su fita.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now