A date proposal🌹

329 30 0
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.












Shin ko kana kishin Kasarka? Wannan shine mafi girman al'amari da burin da ake nema ga reka. Ka so kasarka ko ka samu martaba a wajen Ubangijinka, Son kasa wajibi ne ga kowa..

Tun daga nesa ya zuba mata ido yana mamakin canjawar da tai ƴan kwanakin nan da baya ƙasar, duk tabi ta birkita shi da sabbin salolinta, ya taɓa cewa ita A ce to yau in akwai abunda ke gaba da A zai bata kyauta, cikin taku ɗai-ɗai ta iso har gaban motar, a hankali ta buɗe ta shigo tana faɗin "da fatan ban daɗe ba".

Shi ko da komai na duniyarsa ya tsaya masa cak! ya ƙara dubanta cike da mamaki yace "Wai ina zamu je ne ma?".

Murmushi mai ɗaukar hankali tayi tace "Office mana!".

"Gaskiya ma a fasa kawai! na gwammaci in zauna in ta kallonki ni kaɗai".

Tauna cin-gam tai ƙasa-ƙasa cikin wani salo tace "duk yadda kace ƴal-laɓai ai haka za'ai" ta faɗa tana gyara zama.

"Hmm wai shekara nawa ne ta rage ki gama makarantar nan ma?".

"Ukku ne kacal!".

"Ohh kacal nema?" ya saki ajiyar zuciya, ya tada motar suka fara tafiya har suka isa gaban wani tangamemen company mai kusan hawa bakwai tsayawa faɗa maku tsaruwar ginin abun zai ɗauke mu lokaci, a gaba wajen an rubuta M&A MASKA MOTORS, da logonsu, kamar yadda ta taɓa gani a jikin compliment card ɗinsa yau gata zata je office ɗinsa da ƙafafunta.

Tana niyar buɗa ƙofa yace "Not yet!" ta juyo tana kallonsa da alamun tambaya, a hankali yake bin kowace gaɓa ta fuskarta da kallo me cike da ma'anoni da yawa har ya sauka kan ƙananan laɓɓanta, sencond ɗaya!, biyu!!, uku!!!... da sauri kuma ya janye idonsa ya miƙa hannunsa kan dash-board ya zaro tissue ya miƙo mata ba tare da ya ƙara kallonta ba yace "sai kin goge shi tukun".

Tabbas ta gane mai yake nufi, ohh yau taga takanta, haka ta ansa ta goge jan bakin tas, sai natural pink lips ɗinta suka fito shar dasu, sai suka ɗan ƙara ja saboda murzarsu da tayi, a taƙaice yaɗan kalleta sai yaga ma natural lips ɗinta sun ma fi jan-bakin kyau.

Sun yi aƙalla minti biyu suna zaune shiru a motar, can kuma ya ɓalle marfin motar yace "muje!" haka ta fito tana bin takunshi a hankali a baya dan ta tsorata da yanayinshi, ƙofar shiga wajen kamar ta banki haka take ga masu tsaro a waje a ciki ma sun tadda wasu.

Suna fara zuwa wajen mutane ta ga an fara gaishe shi sai an wuto shi ita ma sai a gaisheta cike da mamakin tare suke da ogansu, aiko da sauri ta koma gefenshi ya juyo suka haɗa ido ta ɗan saki gajeran murmushi shima ya maida mata a taƙaice, haka suka cigaba da tafiya tana ta mamakin sauyawar da yayi ƴan mintuna kaɗan, dan har idanunshi sun ɗan kaɗa sunyi ja kaɗan, ita kam bata gane yanayin da ya shiga ba sam!.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now