Lokaci da Rayuwa..

497 52 10
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎



STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).



Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.











Mafi gajiyawar mutane shine wanda ya kasa samun yardar ƴanuwa, mafi gajiyawa daga gareshi shi ne wanda ya tozarta wanda ya samu daga cikinsu.








Tana zaune a magudada tana wankin kayan makarantarta tana ta tunanin Mai-takalmi, sunan da ta samai kenan, abu kamar wasa yau watan su shida da haɗuwa, amman har yau ta kasa cire tunaninshi a ranta, ita tambaya ɗaya ce inda zata samu mai amsa mata ita to da zata daina tunanin shi har abada, dan yanzu kam ta gaskata maganar Maryam na cewa akwai wanda Allah ya ƙaddara sau ɗaya zaku haɗu a rayuwa, kuma daga lokacin ba zaku ƙara haɗuwa ba, shi kenan kuma har abada.

Tambayar data fi damunta shine "yana cikin ƙoshin lafiya?" waze amsa mata? Babu! Shiyasa kullum take cikin tunanin, shin yana ina ne? A wane hali yake?ƙila ma fa da gaske halan ya manta da sun haɗu, ita ke ta damun zuciyarta da tunaninshi, ko tace zuciyarta da kanta ke rakito mata tunanin nashi, kusan kullum tare da rigarshi take kwana a jikinta, tana shaƙar ƙamshinshi, in kuma ƴan gidan nasu sun taɓota a jikin rigar nashi take kukanta.

Tunda ita dai Inna ba shigar mata faɗa take ba sai dai ta bata haƙuri ta bata shawarwari tare da nasihohi, kuma sun ishe ta komai sai dai akwai abunda in an mata ko an ma Inna dole sai ta koka take jin daɗi, Yaya Saleem ne mai shigar mata shima yayi mata nisa.

Ta tsunduma a tunanin rayuwarta sai ganin tulin wanki tayi an jibge mata a gabanta, a hankali ta ɗaga idonta ta sauke su kan Iya, kana ta ƙara maida dubanta gun kayan wankin da ta aje cikin rashin fahimta.

"Ga nan kuɗin sabulo ki siyo, in kin gama naki sai ki wanke waennan, kayan makarantar su Yahaya ne" Iya ta faɗa cikin isa tare da ajiye mata ₦50 a gefenta.

"Iya! Su Yahaya fa kika ce, yanzu nice zan wanke masu kayan makaranta fisabilillahi, sun fa girmeni Iya, kuma ma maza dasu ba su wanke kayan makarantar su ba sai ni zan wanke masu kamar wata ƴar aikin su?".

"To in sun girme ki sai akai yaya? ina ce sun isa ki wanke masu a matsayinki na ƙanwarsu?".

"Haba Iya! ai in haka ne ba ni kaɗai bace ƙanwarsu a gidan nan, baga su Uthailama nan ba, sai me yasa ni ƙaɗai za'a ba wankin na su, jiba ma fa yadda kayan sukai buɗu-buɗu".

"To yanzu na gane! so kike ki cemun ni ban isa dake ba kenan, ban isa in saki aiki ba saboda bani na haife ki ba ko, shine ki ke kira mun su Uthailama tunda su na haifa ko?".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now